← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 193

Sashe 157

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ana cikin hakane Mallam ya tara Su Hajiya duka matansa ya sanar dasu Cikin watan nan manema auran su Hanne da Hamida da Sa"adatu zasu zo su gana dasu basu yi wani mamaki ba Daman ai su san tunda sukayi jarabawa a SS2 susan mallam bazai zuba musu ido ba aurar dasu zai yi Anty Amarya ce kadai ta nuna Damuwarta ta kalli Mallan tana Fadin"Mallam nawa duka duka yaran nan suke..?
Shiyasa naso da ka bari sai wannan shekarar su zana jarabawar tasu kamar yadda duka yaran gidan nan suke yi..!
Mallam yace"To ai nasu tsarin ne yazo ahaka sun gama zaman me zasu yi..?
Kuma daman tun kafin haka suna da mgana akansu ai bazan zuba musu ido suna zaune haka ba sannan da kike mganar yara su hannatun ne yara..?
Ko basu kai sha takwas ba nasan sun kusa ko Hajiya..?
Hajiya na gefensa tace"Ai sun ma Shiga a watan musulunci mallam..Su kansu sauran yan"uwan nasu suna Sha takwas wasu sha tara ake aurar dasu nake ga..!
Mallam yace"Ahto .Nidai na fada muku ku sanar da yaran ku su fara Shiri Insha Allahu bikin kuma zai kai karshen watan gobe ne bazan Dauki Lokaci ba..Su kuma su Akilu na yi ma Wani abokina Dake Jami"ar ABU mgana zai tuntubamin in sun samu gurbin karatu chan zan tura su tare. !
Hajiya ta amsa da Allah ya bada Sa"a ya kuma yi albarka Hajiya ita da Hajiya Nasara Hajiya uwa dai duk yadda takai ga Boye Damuwarta Sai ta bayyana Mallam nata aurar da duka ya"yansa ya manta da Umaima ne .?
Bai taba mganarta ba ya Jingineta gefe ba boko ba islamiya sannan ba mganar aure Tunda ta ke ganin ta kusa Cika Burinta sai kuma Umaiman yanzu ne damuwarta.
Ita ke da mallam yau yasa su Hajiya suka fice suka barta sai da suka shiga Ciki bayan yayi wanka yayi shirin kwanciya ta kallesa tana Fadin"Mallam naji kayi mganar auran su Hanne ne..?
Ban ji ka saka Umaima aciki ba..?
Na zata wannam karon zaka Hada da ita ne..?
Sai da ya Zauna gefen gado ya dora kafafunsa saman gadon sannan ya Fuskaceta yana fadin"Umaima da bata da Lafiya Uwani..?.
Kuma ma ba wanda ya kaawo min mganarta ne har yau shiyasa kikajini shuru da ita..Sannan ni fata na ta samu Lafiya sai komai ya Biyo baya. !
Sai hajiya Uwani ta saka kuka tana Fadin"Haba mallam domin Allah ya Daura mata wannan Laluran sai kace bazatayi aure ba .!
Ai sai ita ma ka hadata da mijin daya Dace da ita kamar yadda kake ma Sauran ya"yanka har da ma wanda ba Naka ba. !
Ta karishe Fada tana kuka kallonta kawai yake yi yana Nazarin mganarta Mimirshi yayi kafin yace"Uwani..Kinsan Kalmar wlh Rantsuwa ce..?
Ta daga kanta ya Cigaba da Fadin"To wlh tallahi ban taba Tallata ya"yana ba ko ya"yan Sa"idu ba Duk Cikin yaran da na aurar dasu zuwa akayi aka sameni mganar ana son aure Cikin iyalaina abu Daya nake yi shine ni nake Zaban wacce ta Dace sai nace na bama wane na bama wane kaza..Sau Daya tak na taba Aikata haka kuma shine na karshe da yardan Allah mganar Umaima kuma ni bazan zama mara adalci ba kamar Zalunci ne na aurar da ita da wannan laluran batare da sanin wanda zai aureta ba Saboda haka in Bukatar hakan ya taso Lalle to sai an Bude komai a Fili in wanda yazo neman auran yaji ya gani Shikenan Uwani nima zan so ganin na gama Sauke Nauyin aurar da duka ya"yan Matan da Allah ya bani..!
Daga haka bai kara mgana ba sai ma mganinsa na Ciwon kafa Daya Dauka yana Shafa ma kafarsa tasa.
haj.Uwani tayi jagale tana kallonsa kafin ta Cigaba da matsan kwallarta Hujjan mallam ai ba Hujja bace in ya bata da ita yadda ake ganin girmansa ai bazata wulakanta ba ammh Saboda An ga gazawarta ne kowace mata za"a gama kwashe ya"yanta ita kuma ko Oho.
Ranar haka suka kwana kowa da Abunda yake sakawa aranta,Da Safe data koma Shashenta ta Kira Batula ta Sanar da ita komai tana Fadin"Batula Hankalina ya fara tashi..kannen bayan Umaima mallam aurar dasu zai yi tana Zaune. !
Batula tace"Mafita kawai ki shiryo kizo Tsafe mu tafi Niger wajen mama..Bazamu bari aga gazawarmu b...!
Da wannan shawarar Haj.Uwani ta Zauna adaran ta tambayi mallam zuwa Tsafe bai hanata ba yace Allah ya tsare ya bata kudi 20k da zata tafi da harda kayan abinci yace ta tafi dashi gidansu tana ta godiya idi ya kaita washegari bai kwana ba Aranar ya Dawo.

Cikin Satin da mallam yayi ma su Hajiya mganar auransu hanne Tuni Labari yakai ko'ina tunda su hannen har masu auran dake wani garin iyayansu sun fada musu hanne da Hamida Hajiya ta kirasu ta Fada musu duk da daman ai susan haka zata Faru ammh sai da jikinsu yayi sanyi aure fa?tunda sukaji mganar basu da wani Walwala daman Amina na nan ne itace Cikin kowani yanayi bazata taba bari su damu ba Jidalinta kadai ai ya Ishesu Allah sarki Amina suna kewarta sun gaji da jiranta da saka ran Dawowarta har sun cire rai ma.
Bangaran Sa"adatu kuma kuka ta Dinga ma Anty Amarya wai bata son aure yanzu sai da Anty Amarya ta kusa Dukanta sannan ta kyaleta Domin ko ta kai wacece ita bata isa taja da Umarnin mallam ba Sadiya yayarta Anty Amarya ta Fadamawa ita kuma ta Kira waya aka bama Sa"adatun ta mata fada shiyasa Sa"adatun tadan Saki ita kanta Anty Amarya bata so ba ammh to ya ta iya..?
Mallam in ya Fadi mgana ai bamai Tada ita kuma sai Allah...
Mamanmu da Aba ya Fada mata Murna ma ta Farayi zata yi Biki na kece raini wajen aurar da autarta hamida Saboda Tasan mallam gangariyan mazaje masu Nagarta yake aurar da ya"yansa da nasu garesu Shiyasa bata da wata Damuwa in akwai abunda Hajiya da mallam ke yi suna Burgeta wannan Sadaukarwan nasu ne, basa numfasawa sai sun ga duka ya"yan agidan auransu mai Cike da Nagarta ne Shiyasa da Anty Amarya ta Kirata tana Korafin auran yayi kusa sai da Mamanmu taji Haushinta da Tunanin tana Bakinciki to in ba Haka ba menene. ?
Yara sun gama karatu to me zasu jira ai sai aure ammh tana neman ta nuna Bakinciki akan hakan,Sai dai bata Damu ba sanin ko me Anty Amarya zatayi Mallam dai bazai sauya mgana ba Sannan ai ita kakarta ce ta yanke saka Tunda tana ta amsan kudade wajen Aba da sunn siyama Hamida yan kayan kitchen tunda kayan gado da Sauransu mallam ke musu kowa ya sani ai ita fa Duniya sabuwa aranta tasha Fadin ko yanzu kasuwa ta Watse mata ai dan koli yaji Riba...
Chapter 157 · 0% Book details