← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 193

Sashe 48

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bata taba katarin ganinsa ba,Sai watarana sun dawo daga islamiya,Idi bai zo Daukansu ba Motar tana ta basu matsala ya shamsu ya Tarkasu su ya Abida ne ke baya su kuma suna gaba su uku kamar koda yaushe Sa"adatu na baya tare da sabeeha da Umaima ya shamsu da su ya Akilu suna bayansu sun taso su gaba Kafa kafa Hira suke a tsakaninsu Labarin littafi Amina ke bama su Hannu kasa kasa suna Dariya sun kawo kofar masallacin Baba mallan kamar an ce ta Daga kanta sama ta Hangosa abakin Masallacin yana Tsaye cikin irin Shigarsa kamar ko yaushe da Jaket baka Baki ta saki da Hanci tana kallonsa Cikin mamaki Farimciki yaji yau daya ganta ta gansa Hannu ya Dagamata Lokaci Daya da Mirmishi.
Su hanne sun juya suga me take kallo kamar ya sani ya Duka kamar yana Gyara igiyan Takalmi sai basu gansa ba Amina suka koma suna kallo kafin Hamida tace"Wa kike kallo Amina..!?
Sake kallon wajen tayi sao kuma taga bashi a wajen ta fara waige waige Ya Nasir ta gani yana Daukan Buta sai ta Fara Tunanin ko gizo yake mata yasa tayi saurin cema Hamida bakomai..!
Ta Dauka bashi take gani ba sai da washegari ta kara ganinsa Lokacin sun fito zasu islamiya,shima ya Ganta ya kuma mata Mirmishi gani na ukun da tayimai da Safe ne Ranar asabar zasu tafi Hadda ta fito tana jiran Hamida jikinta ya fara rawa Yana Daga Tsallaken su chan bakin wani gida Wannan karon bayan Mirmishi har sai da ya Daga mata hannu ta fara Tsorata tana Tunanin kodai ba Mutum bane Kila aljanine Datake ganinsa a ko"ina kuma ta kasa Fadama ko Hanne haka kurum bakinta yayi nauyin data gaza Furta komai.
Daga Lokacin kuma duk sanda ta fito gida sai tayi waige waige ko zata gansa sai dai bata kara ganinsa ba sai ta yadda da Tunaninta kila gamo tayi da aljani.
Harta da su Hamida sun fahimci kwana Biyu Amina ta rage karkasashinta da suka tambayeta sai tace bakomai basu damu ba sanin Halinta Lambo take halinta na tashu ne Lokaci bayan Lokaci kamar mai Bugawar jinnu.
Bata kara ganninsa ba sai bayan Shudewar kwana Hudu tsakani ta kara ganinsa a gabda gidansu Ranar Wata Laraba sun dawo daga makaranta,Gidansu Hanne ta Tsaya sai da tayi sallar mangariba Hanne ta Rakota Mazan gidan duk suna masallaci Baba Mallan na wa"azi
Har hanne ta rakota kofar gidansu suka Tsaya suna mgana yana Daga gefe basu ganshi ba har Hanne ta juya ta koma gida ita kuma ta juya zata shiga gida Taga mutum yasha gabanta.
Ta firgita taso ta yanka Ihu ne sai ya Hasko hasken wayarsa lokaci Daya yana fadin"Nine..AmIN...!
Taji muryansa ai ta Haddaceta kamar Karatu Cikin tsoron da bata taba jiba ta fara waige akwai hasken a wajen Karo na farko taji mganar su Hamida in wani ya zo ya ganta fa..?
Abu ne da bai taba Faruwa ba..!
Tana ji yana Fadin"Amina kin bani Wahala..?wlh da gaske ina sonki..baki ga yadda na koma saboda ke ba...?
Yake fada yana kallonta da Dukkan Zuciyarsa Jikinta ne ya fara rawa domin taji motsi tunani take ko wani ne zai fito Daga gidansu ta manta ba kowa Aba bai dawo ba kuma Ya Jafar yana masallaci wani Firgici ne ya shigeta Dayasa ta Damki hannun Aminu suka sha kwanar Dake Tsakaninsu gidansu gabanta nacDukan uku kamar ta rike kaya haka tayi saurin sakinsa kafin tace"Don Allah ka daina bina..Kaga bansan ka ba..Ka daina Bibiyata kada kajamin mtsala..!
Take Fada acikin idanuwanta yake ganin Tsoron wamda Daga gani tsoron ya shigeta Lokaci Daya.
Cikin Gyara tsayuwarsa yace"To in na Daina Binki ni ya zanyi..?
Wlh tallahi kin ji rantsuwan Musulmi ina sonki Amina sonki ya hanani zaman waje daya ki kalleni koda yaushe ina garin nan na kasa zaman Kano ballatana Yola koda yaushe korafin Nenne na ta daina gane kaina kuma Wlh duk kece Sila..!
Yadda yake mganar ne yasa ta ke kallonsa acikin idanuwansa ta Hango gaskiya aciki.
Sai dai ta tsorata wannan wani abu ne da bai dace yana Faruwa akanta ba Arude tace"Meyasa sai ni..?ni fa karamace akwai yayyina ga su ya Abida duk bakace su ba sai ni..?
Kai Tsaye yace Mata"Ni ban sansu ba ni ke na sani..kuma ke Allah ya Saka Kaddaran haduwarmu Amina..!
Amina ta zaro mai ido tana Fadin"To wlh ahir dinka da bina..Kada ka sakani Cikin mtsaaala in Aba ya Sani ko ya Jafar ko ya Nasir wlh kasheni zasu yi..!
Ka rabu dani Amina ba kamar matar da ka sani bane yarinya ce ni ban gama karatu ba..!
Da sauri yace"Nasani zan jiraki Amina da gaske nake ina sonki kuma na Rantse zan aureki..!
Amina ta Dafe kirjinta tana Fadin"In wani ya sani zaka jamin bala"i daman nayi suna..Amina tayi suna ka rabu danu don Allah ban san me kake fada ba..Don Allah ka tafi ka kyakeni..!
Yaji Rokonta bayaso ya ja mata matsala yasa ya ciro katinsa Daga aljihun wandonsa ya mika mata yana Fadin"Zan tafi badomin na tafin kenan ba..Zan tafi ne saboda kin Rokenu sai dai zan dawo zan rika Binki duk inda nasan zan ganki Amina banfara sonki da wasa ba Wlh..Wannan kati ne da Lambobin wayata aciki duk sanda kikaji kina son mgana Dani ki samu waya ki kirani zan zo..!
Kin karba tayi ta noke hannunta Tana Fadin"Kasheni kake so ayi in aka ganni Dakai..!
Kai ya girgiza mata bai yi mgana ba illah Hannunta Daya kama ya saka mata katin kafin yace"Ba abunda zai faru..Ki sani Aminu Buba yana Tare Dake acikin kowani Bugawar Numfashinki Amina na barki Cikin Amimci..!
Daga haka ko waige ya Fice Daga Kwanar Jikin Amima ya fara rawa ta Murza katin hannunta.
A.A Buba tagani ajikin katin da address dinsa da jerin Lambobinsa kamar ta yardaahi sai kuma ta Fasa taji Ranta na janta data adana katin Kilan watam watarana yayi mata amfani yasa ta Dunkule katin Daga hannunta sai da ta leka ta Tabbatar daya tafi kana ta fito ta shige gida aharaban ta Tsaya tana maida Numfashi Cikin sikat dinta ta Boye katin bata so wani yaga bata Shiryama wannan Jidalin ba yafi karfinta wannan karon..!
Cikin kayanta ta Boye katin Boye mai Tsawon da ba wanda zai gani kuma koda wasa bata taba Fadama su Hanne ba.
Bai yi karya ba Tun da karancin Shekarunta Ta Fahimci Aminu na cikin Duka bugawar Numfashinta ta Rage Walwala da yawan mgana Tun ballatana data Daina ganinsa data Kulle ido zata kwanta shi take gani da kuma Kunnuwanta na Sauraran Muryanta bata son so ba..Sai dai ta Fara Fahimtarsa a karance karancen Datakeyi sai dai tasan Shekarunta basu kai ga bama wannan a Tsarin Jadalin Gidansu soyayya ko manyansu basu yi ta ba ballatana saboda haka wannan Tunanin baya Cikin muhallinta.
Su hanne da Hamida sun gaji da korafin Chanzawar Amina ranar Tana jinsu da Hanne ta shigo tana Fadama Mamanmu har yaya tana Tsakar gida alokacin Hanne take korafin sauyawar Amina.
Zeenatu na wanki abakin Famfo tace"Nima na ganta kwana Biyu ba Tsiwa nace kila aljanub Salahancinta ne suka sauka..!
Hamida tace"Allah Nafi son Aminar mu ta baya..Wannan shurun shurin bana sonta..!
Hanne tace"Ko ya Abida sai da tace Amina ta sauya..Sai Hajiya tace Hankali ne tayi girma yazo..!
Mamanmu najinsu tace"Kwarai da gaskiyan Hajiya..Hankali da Natsuwar dake mata gori ne Allah ya bata yanzu..!
Hamida tace"Mamanmu Amina kamar tayi gamo fa..?ko Aljanun Dare ne suka bata tsoro kinsanta da Fitan Dare ko tsoro bataji..!
Ya zeenatu ta saka Dariya tana Fadin"Waya sani ko ta hadu da Cika Lora..!
Gabadayanau suka saka Dariya Har Yaya Dake gyaran kubanta acikij Ranta tana Fatan Hankalin Amina ne yazo kada ace shurunta wata Tsiyar take shiryawa kamar yadda ta Saba.
Amina nadaga cikin Daki tana jinsu Mirmishi tayi ta Furta"Gamo nayi Hamida..Tabbas na gamu da jidalin Danike kira ni Amina..!
Chapter 48 · 0% Book details