← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 193

Sashe 3

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ko Amina..?Bin Maza kika fara..?Nace bin Maza kika fara..?Wlh ina Tsausayinki Ranar da Bakinciki zai kai Alhaji kasa Nima kin Sakani kuka ba sau daya ba sau Biyu ba, Amina ki kashemu ki Huta nace ki kashe mu ki huta..! Amina bakinta bai yi Shuru ba Fadi take"Ni bana bin maza..Wlh Allah Amina bata bin maza ki yarda dani Yaya..! Take fada tana Tsiyayan Hawaye,Hawayen da Dukan Yaya ne kadai da kalamanta kan saka aga Fitarsu daga Idanuwan Amina. Bakinta ta Bike sai da ya fashe cikin Takaoci tace"Kina Kara batamin rai in ina mgana kina mgana..Amina Bakin ki na Daya Daga Cikin Nakasunki bakin ki baya iya mutuwa koda girman Laifinki yafi girman Duniya ne..! Amina ta sharce jinin bakinta tana Fadin"Yi hakuri Yaya..! Haka kawai take fada tana kuka sosai abu Daya yafi Tsaya mata arai Cewar da yaya tayi tana bin maza tasan Tana da kafar yawo da Bin Gidajen kawaye gayyar ko ba"a gayyaceta ba Amina sai taje tasan tana da rashin kunya da Kafiya da Taurin kai da Tsokana tasan bata da Kirki wani Lokaci ammh Wlh maza basa gabanta Tsakaninta dasu sai goge reni Domin har ayanzu Amina bata jin kunyar zagewa ta Chasa wanda yayi mata shiyasa kaf ajinsu na Boko da islamiya suke shakkarta bata Duba Jinsu ita wanda yace mata kole ne zatace mai cas ammh bata bin maza ita ba yar iska bace! Gabadaya jikinsu Hamida yayi sanyi Amina na kuka tana Fadin"Kiyi hakuri yaya..! Ita uwa Dabam take acikin Ranta tanajin kamar Amina ta koma Ruwan sanyi da Yaya zata Daina damuwa akanta Mamanmu zata Daina kuka akamta ammh ko ta Dauki alwashin abanza da ta gama Damuwarta za taji kamar kara mata wasu abubuwan akeyi wani Lokacin ita kanta Har mamakin irin Taurin zuciyarta take ko na wani kato albarka. Dukkansu Hakuri suke bama Yaya batace komai sai kwallah Data ke sharewa Zeenatu ne ta Ruga Dakin Mamanmu ta taso ta wacce take kurya tadan kwanta Sama Sama taji Zeenatu na Fadin"Mamanmu..Mamanmu..! Bude ido tayi tana Fadin"Zennatu meyasa kika tasheni..?nasan barcin yammah bai da dakyau..Kaina ke Saramin..! Da sauri Zeenatu tace"Daman nasan baki ji ba.Yaya yau ranta ya baci gashi chan tana kuka tana Dukan Amina..! Ai bata gama ba ta ingize Zeenatu ta Diro Daga kan gado Dankwali a Hannunta Zaninta na neman Faduwa ta Fice da gudu Zeenatu ta Bita da kallo ta Girgiza kai. Tana fitowa ta isa ga Amina ta Rumgumeta tana ganinta ta riketa tana kuka take fadin"Mamanmu don Allah ki fadama Yaya bana bin maza Wlh ban bi maza gidan su yar Ajinmu naje Zainab isa kudina naje amsowa na iske sun yi tafiya ba kudi a hannunsa saina tako akafa mamanmu ammh kiji fa abunda yaya ke..! Bata karisa ba ta Rufe mata baki Cikin Rauni tace"Basai kin fada ba..Nasanki Amineene..bazaki fara Halin da bana ki ba.. Share Hawayen Daina kuka matukar mamanki na Raye baki ba hawaye har Abada..! Tafada tana share mata kwallah Cikin kauna Yaya kada kai tayi ta bi hanyar Dakinta tana Fadin"ki Rika samun waje acikin ranki kina fadama Amina gaskiya..Ko tana so ko bata so Ta fita zakka acikin gidan nan..! Daga haka ta bankade labule ta shige Dakinta Mamanmu bata Damu ba mikewa tayi tana Dago Aminan Lokaci Daya tana Fadin"Hamida Dauki Jakar Amina ki kaimata Wajen Dirowarta..Ke Zeena zubo mata abincinta a filet ki hado mata da Ruwa da Zobo yanzu adakina..! Zulaihat dake gabanta ta kallah kafin tace"Matsa ki bani waje..! Zulaihat ta kalleta kafin tace"Mamanmu..! Rai bace ta balla mata Harara tana Fadin"Ki yi wanke wanke..Gobe Aminan tayi..ku kuma kuyi abunda na sakaku..! Daga haka ta shige Dakinta Dauke da Amina Dake kuka kamar ta maidata Ciki Hamida ta ja Jakar makarantar Amina zuwa Dakinsu Dirowansu kusa da juna ne Domin gadon su ma ahade yake ita tana Sama ne Amina na kasa saman gadonta ta ijiye mata ta Fice ta koma bakin Famfom ta Cigaba da wankinta ita kuma Zeenatu ta shiga Kitchen ta Bude Cooler ta Dibo Taliyar da Kifin Dake ciki ta Bude Fridge ta Dauko Ruwa da Zobo ta Fito zuwa Dakin Mamanmu. Ita kuma Zulaihat ranta bace ta Fara Fito da kwanukan da aka bata akichen Zuwa bakin Famfo. Hamida Dake Dauraye kayanta Tace"ki barshi Anty Zulaihat in na gama shanya zan wanke! Kai tsaye tace"Yauwa.Daman duk Ranar da Amina ta kwaso jidalinta yafi Shafarki..! Daga haka ta wuce Bata bi takan Hamidan Dake Dariya ba tana Fadin"Amina ce Anty Zulai..Wlh ko Aba baya iyawa da jidalinta ko Ya Jafar gajiya yake..! Take fada tana Dariya shanyan kayanta tayi tazo ta fara Jika kwanukan sai ga Amina ta fito Daga dakin mamanmu kallonta tayi itama ta kalleta kai tsaye tace"Gobe da Safe har zuwa rana zan yi wanke wanke..Zan rama miki kada kice kin Dauki Jidalin Amina..! Tafada tana Share bakinta Daya kumbura Hamida kai kawai ta kada Amina ce sai tayi mgana. Ta fara wanke wanke sai gata tafito jikinta Riga ce doguwa na Atamfa sai Hular Dake kanta Kayan makarantarta ne ke Hannun ta Zata wanke saboda gobe Asabar suna Hadda Tun Safe sai yammah,haddar tasu daya take da islamiyan shiyasa ana tashi Uku da Rabi ayi sallah aci abinci a shiga islamiya itama Madaratul Umar Bin kallab din mallakin Baba mallam ce snnan gabadaya malaman makarantar ya"yansa ne da Dalibansa har ya jafar yana koyawar ajin manya Wato Jss1 da ajin matan aure ya Nasir da ya Uzairu da ya Nazim Duka suna koyarwa anan,Sai dai yanzu Ya Nazim da ya Uzairu suna Makarantar jami"a sai sun dawo Hutu suke zuwa Yaya shamsu ne shima Dukka da kananun shekarunsu Kansa na ja yayi Sauka da Hadda ga Sauran Littafai kai duk ya"yan mallam haka suke akwai kwanya kuma ance duk Kwanyarsu basu kai Babban DA'N MALAM ba dake jami"ar madina yana koyawar chan yake zaune da iyalansa sai karshen shekara suke zuwa gida sai dai Sakonsa akai akai yana zuwa ga mahaifansa. Har ta fara wankinta ta gama bata cema Hamida komai ba itama batace mata ba Tana idar wa kenan tana Shanya Sallamarsu Ya Jafar da da Ya Nasir ta karade gidan da Sauri Amina ta juya tana kallonsu Fes suka Hada ido hudu da Ya Jafar wata uwar Harara ya Zuba mata yana fadin"Gama Shanya..Ki Tsaya a inda kike ki kama kunninki..! Nasir Dake gefensa yace"in kin gama kama kunnin ki hada da Tsallon Kwado..Yau zaki gane iskancinki kadan ne Amina..! Daga haka suka wuce lokacin suna amsa gaisuwan Hamida Jawaad dake bayansu ta kallah yana mata Gwalo yaro dan shekaru goma.! Amina Rai ta bata a fili ta Furta.."Azzalumai Biyu kenan..Allah ya Hadasu abota kamar yadda Muguntarsu tazo Daya..! Hamida ta kallah wacce ta zuba mata ido Hararanta tayi da karfi Tana Fadin"Bana son gulma Hamida..! Kanta ta kauda tana Dariya gama Shanyar tayi ta koma bakin kofar gida ta Coge taki yin abunda akace sai taji motsi sai ta yi kamar ta Duka ta kama kunni sai taga basu bane sai ta Mike Dakin yaya suka fara shiga. Tana chan tana Hararan Hamida suka Fito Da sauri ta Duka ta Daga hannunta Sama Jafar ya kalleta Cikin wani yanayi kafin yace"Kada kiyi..Kiga yadda zan yi dake agidan nan..! Nasir kuwa wayarsa yake latsawa hannanunsa Daya Dauke da Littafan Karatu na addini Dakin mamanmu sukayi sallama suka shige Amina ta bisu da Harara afili ta Furta"Duka ai baya kisa..!
Chapter 3 · 0% Book details