← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 193

Sashe 9

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari tun Safe kamar abun arziki suna Idar da Sallar asuba Sukayi azkar Hamida da Hanne suka zauna Zulaihat na Biya musu karatu Ya Zeenatu na Kitchen tana Soya musu Dankali Amina ta Fita Tsakar gidan Dakin Mamanmu ta fara shiga bata Ciki Tana Dakin Aba sai ta wuce Dakin Yaya ta sameta kan Darduma tana Karatun Qur"ani yadda Amina Tayi sallama ta Shigo aranta Tana Fatan Daman Amina ta zauna haka sai dai ina tana Shigowa taci karo da Jawaad dake barci nan kusa da Yaya ta Daga hannu ta Dagamai Duka tana Fadin"Wana kama yanzu..?
Ta Tashi yana Sosa inda ta Dakesa Wuyansa ta Chakuma kamar wani Babba tana Fadin"Wa kake ma Dariya Jiya..?
Yasan Halinta yasa da Sauri yace"Bafa Dake nake ba..yi hakuri ya Amina..!
Fayau Fayau ta Fallamai mari tana Fadin"Daman na Fada maka na fika jidali..Yanzu sai nayi wirgi dakai sai ka Bugu iya Buguwa!
Dakatawa da Karatun tayi ta Dago Tana kallonta kafin tace"To sake sa kafin kiyi wurgi dashi..Fitarmin Daga Daki..!
Ta Fada Cikin Bacin rai Amina ta kama Hanya tana kunkuni Lokaci Daya Tana Fadin"Yaro yayi ta iskaci ba"a gani..Sai ace baza"a Dakesa ba..Kwarankwatsa na gansa sai na bugesa..!
Tana jinta tana Fada Har ta Fice Daga Dakin kai ta kada tana Kokarin Cigaba da Karatunta sai gashi ta Leko Tana Dagama Jawaad Hannu Tana Fadin"Zaka sani ne yaro bar ganin Yaya..!
Ta dago Cikin Bacin rai tace"Amina..!
Da Sauri tace"Ina kwana Yaya..Daman nazo gaisheki ne..!
Ko Sake kallonta batayi ta kalli Jawaad tana Fadin"Wuce kaje ka Tube kaya na saka ruwa a Kittle a Tiolet kayi wanka dashi..lokaci na Tafiya..!
Ba Musu ya wuce ita kuma Amina ta wuce aranta tace"Nidai na Fita Hakki na gaisheta..!
Daganan Falon Aba ta je tana ta Sallama kafin taji ya amsa mata kamar ta Allah haka ta shiga kanta na kasa yana zaune kan kujera yana Duba Wasu Takardu ya Dago yana kallonta Da Sauri tace"Aba ina kwana..?mamanmu na ciki..?
Yana Nazarinta yace"Ita kikazo nema..?tana ciki tana barci..!
Da Sauri tace"A"a nazo gaishe ku ne Aba..Sannan na tambayeka..Wai ni na saka maka Hawan jini Aba..?
Kai Tsayen yake kallonta kamar yadda Itama ta Sauke masa Dara Daran Idanuwanta wandanda yake kallonsu kamar na Hadiza Lokacin tana kamarta.
Ita kadai ce acikin ya"yansa take iya Kalllnsa ido Cikin ido ta Fita zakka Tabbas ko acikin Ransa Amina Dabam take har Tunani yake daman Hausawa sunce Maraji aciki yayan Mutun sai kaga kafi sonsa To shima Hakanne sai dai yana kokarin Danne komai sannan yana ganin kamar Kaunar Dayake ma Amina tasamo Asali ne Tun Kaunar Daya ke ma Mahaifiyarta har yau gobe Hadiza In soyayyarta ta Motsamai sai yaji wani Abu acikin Kirjinsa mai Nauyi game da ita.
Saurin Dauke kansa yayi daga kallonsa ita kuwa ganin haka yasa tace"Kayi Shuru Aba bakace komai ba..?
Sai da ya Daidaita natsuwarsa kafin yace"Waye ya fadamiki haka..?
Kai Taaye tace"Waye zai fada..Yaya ce Aba..!
Kai ya dan jinjina kafin yace"A"a bake bace..Ciwo na Daga Allah ne da kuma Girma kinsan ai nafara Tsufa..!
Yafada yana kallomta Itama kallonsa take Tana so taga tsufan Dayace ya Fara,Yana da Tarin Baiwa da Zati in ka kallesa shi ba Fari bane sai dai yana da Haske Daga Zaunen Dayake zaka gane yana da Tsawo da Dan Jiki Sannan akaron Farko zaka san a Tsaye yake Bakin Zamafare kodaga yanayin mganarsa da Zamfaranci.
ALHAJI SA"IDU AMINU GUSAI kenan Ba Rago bane mutun ne Jajirtattace wanda ba abu kadan ke saka aga Rauninsa ba sannan mai Neman na kansa wanda baisan Lalaci ba mai Ra"ayi da Tsari da kuma tsauri kadan acikin Rayuwarsa.
Ashekarunsa in ya wuce ne ya kai 59 zuwa da 60 yana da Tarin gemi baki Mai Kyali kyalin Furfura kadan Shi ai Dan Malam ne kuma Duk wanda yasansa Tun Farin yasan sa da Gemu ne shiyasa wasu Mutanen da suka sansa a baya suke mai lakabi da SA'IDU MAI GEMU..!
cikin Lokaci ta kare mai kallo Kafin tace"Wlh Aba baka fara tsufa ba..Gemun ka fa baki ne bai yi fari ba irin na Baba malam..!
Tafada Har Fararan Hakoranta suka Bayyana Kauda kai yayi yana Danne yanayinsa kafin yace"Tashi kije..Kuyi shirin makaranta kada,ku makara..!
Da Sauri ta Mike tana Fadin"To Aba..!
Daga haka ta fice ya Bita da kallo Acikin Ransa yana Fatan kada watarana Amina ta zame mai Zakka da gaskem da bazai iya Da Jidalinta ba.
Ba wanda yamata mgana ta Dauki Tsintsiya ta Share gidan ta Fito da wanke wanke Lokacin da Hamida ta Fito ita da Hanne,bayan sun je sun gaida Aba da yaya suka zo suna Tayata Har suka gama suna gamawa Hamida ta Shiga Tiolet din Dakinsu sukayi wanka,Amina a Dakin Mamanmu tayi wanka ita da Hanne Yau Ya Zeenatu da Rigima tatashi Mgana Kdan sai ta fara Harara da Fada Amina tayi Dariya aranta tace"Su ya Zeena kwana nawa ne..!
Domin adokar Malam in aka Aurar dasu ya Zulahat suma za"a bama Manemansu Daman neman su Domin Daman akwai su Baba Malam da Aba sun sansu kune bazaku sani ba sai Lokaci yayi.
Su ya zulaihat wata Biyar da suka gabata aka bama Manemansu izinin fara ganawa dasu kuma Tunda Hanne tace mata taji ana mgana auran ya tashi..Ba adau Lokaci ba sukaji Baba Malam yace Rana kaza Daurin auran Da yinin Biki Daman komai na Bukata an Tanadar dashi
Bikin Amare Hudu ne za"ayi Ya Zulaihat Daga gidan Ya Sadiya yar wajen Anty Amarya Ya Aishan Hajiya Babba Ikram din Anty Uwa sune za"a Aurar dasu wannan shekarar kuma Dukkansu suna matakin Shekarar karshe ne a makaranta Dama wannan kowa ya sani Tundaga kan Iyalan gidanmu har Gidan Malam maza ne ke Karatu mai zurfi mace kuwa iya Secondary sai Karatun addini har matakin Sauka da Hadda za"a Aurar Dake in mijinki ya amince adakin ki sai ki Cigaba ammh agidan Mallam da Gidan Baba Sa"idu ba wacce ta wuce wannan Matakin.
Sama sama suka karya da Dankali da kwai da tea susan in suka bata Lokaci ya shamsu zai ce atafi a barsu makaranta bata da nisa dasu sosai ammh gabadaya yara da manya a School Bus ake kaisu.
Amina ce karshen shigowa Motar Hijabinta yasha Tattara saboda Rashin Guga Daman a Kujerar tsakiya suke zama su uku ita da Hanne da Hamida
Sanda ta Shigo sai da ya Shamsu dake Bakin Kofa ya rankwasheta yana Fadin"koda yaushe kece abaya..!
Aranta sai da tayi Allah ya isa tana ganin Akilu da Zubairu na Dariya bama wani fa Girmansu sukayi ba Kwafa tayi aranta tana Fatan samun wata Dama.
Tana ganin Sa"adatu na Hararanta itana ta maida mata kafin taje ta Zauna kusa da Hanne tana gyara zaman Jakarta wanda Qur"ani ke Ciki da Taujud sai Sauran Littafin Islamiya.
sabeeha ce ta ga tana kallomta Lokacin da Motar ta Fita Daga Haraban gidan Baba Malam Hararanta tayi kafin tace"Qurwata Kur..Wlh Aniyar kowa sai ta bisa..Amina dai nan bari wh badai Mutum ba sai Allah..!
Ya Zeenatu ce ta dago daga gaba Tana kallon Amina kafin tayi mgana Ya Umaimatu wacce bata da Cikakkiyar lafiya tana Fama da mtsalan junnu don ma ana Tsaye akanta saboda haka Tayi Deliying karatu Ashekaru ma ta Girme su ya Zeena kamata yayi tana Cikin su ya Aisha ammh Saboda Lalurarta yasa komai ya koma baya Bata zuwa makarantar Boko iyakarta jss3 Mallam yace ta daina zuwa.
Cikin Sanyinta tace"Amina ki bar mgana haka kina cikamin kunni..!
Tafada tana yamutsa Fuska Amina tamele baki tace ahankali.."Kaji Sauran Iska..!
Hanne kadai ta jita Ya Abida Tsaki taja Zatayi mgana Shamsu ya Juyo Daga gidan Gaba yana Fadin"Kun Damemu da surutu..In bazaku Duba Littafanku ba kada na sake jin bakin kowa anan..!
Duk da ya Aisha da ya Zulaihat suna gaba dashi ammh suna girmama juna..ya Ikram na gefe tana jinsuTak batace ba tana ta Duba Qur"aninta Ballatana ya Sadiya datayi kamar bata amotar....!

******
*A RANAR..!*
10:50am.

Madina na gaji na Fara Sarewa acikin wannan Tafiyar tamu..Haba abu Daya yaki ci yaki cinyewa..Shekera wajen goma sha muna abu Daya babu Riba na kasa samun abunda nake so nake kowani Lokaci kina Fadamin wannan karon zamu dace To yaushe..?gobe ko jibi..?ba Rana Madina kowani Lokaci aikin baya Tafiya Daidai na Fara Tunanin ko dai bani da Sa"a ne. ?ko kuma ban zo Duniya da sa"a ba ko kuma kila bani da kashin arziki ne..!

Bansan me ake cewa Dagachan bangaran ba Sannan ita kanta me wayar ba ganin Fuskarta nake yi ba ta riga ta juya ba waya ce rike a Hannunta tana mgana cikin Zafi da kuna..!

"Kullum sai kice na kara Hakuri..?Har zuwa tsawon wani Lokaci zan cigaba da Dauriya da Nade wannan Bakinciki na shekara da shekaru dake Cikin Raina..?Nagaji fa Madina na Fada miki..nayi babbn aiki kan Na samu abunda nake muradi aka Kuskure a karon Farko Madina..JAFAR naso ya zama Haka JAFAR naso Madina..Ba AMINA ba..Meyasa shi aikin ya kuskure kansa sai ya koma kanta .?kinsani bata Cikin Lissafina Domin ita karamar alhaki ce..Sai gashi Sakacinki da yarda Dake da nayi yasa Aikina ya Lalace Komai ya kare ban samu komai ba sai Wahala da Bakinciki Madina to me yayi min Saura..!?
Shuru ya kara Biyo baya kafin ta Daga hannu Cikin kaifin Murya tace"Kul..Dayyaba batasan Ja da baya ba..Madina yanzu aka fara wasan..Yadda nayi alwashin ta rasa komai sai ta rasa madina...Tun ashekarun baya nake fama da Kunar wannan Kaunar wannan Soyayyar dani ke gani acikin Idanuwana SA"IDU ji nake kamar na kashe shi na Wuta..Madina ki Dora aikinmu..Ba gudu ba ja da baya..!
Mu keda Nasara....Nasara tamu ce..
Hahahaaa..!!!!
Lokaci Daya tana Sakin Wata Dariya kafin Shuu kamar Walkiya tayi Saurin barin wajen batare datayi waige ba..!

*Janafty*
[11/6, 3:35 PM] Sweet sis: *TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Sadaukarwa ga Halima yusuf gwarzo(Besty)Alherin Allah yakai miki aduk inda kike*

*🅿️05*
Chapter 9 · 0% Book details