← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 193

Sashe 39

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Sa da aka fara Haraman fita da Amare su Hanne suka Tabbatar da Amima bata gidan sun Duba ko"ina basu ganta ba.
Zafira tace*To ina taje..?
Hamida tace"Gida ta koma fa..!
Zafira tace"Muje to..!
Hanne ta harareta kafin tace"Jeki a karya miki kafa..
Zafira ta kama bakinta kafin tace"Au na manta ne kai ban kara zuwa Bikin na. Gidan Wlh..mu achan gusai in ana Biki ba inda bama zuwa bamai Takura mana..!
Hamida da Hanne suka ce Hamm atare sun kasa mgana.
Suna gani aka fita da Amaran suna kuka ammh ba Halin su bi Tawagan masu Rakiya.
Falon Baba Maallam aka shiga Dasu Hajiya Babba,Sai Hajiya uwa sai Yaya kadai suka shiga dasu.
Baba Maallam da Aba sai su ya Danmaallam da Su ya jafar ya Nazeem ya Nasir ya Nazir dukkansu dai mzan suna ciki hatta su ys shamsu Sauran matan kuma suna Waje suna Jiransu Ciki harda Sakina da su Sarood da Aliyu taso ta bi Sadiya zuwa Dutse Umar ya hanata yace ta bari Daga baya.
Nasiha ne maallam yayi musu,Kadan Ba da yawa ba Domin yace duk abunda zai Fada musu an sanar dasu sai Aba shima yayi nashi sai Ya Danmaallam sannan ya Nazir sai su ya Jafar hatta su shamsu sun musu sallama.
Daganan Baba Mallam ya ba kowacce Qur"ani Izi Sittin da azakar da Cashaba yace in suks rike kyautarsa sun gama Lafiya..
Daganan ya mike suka fito shi da Aba da Hannayensu suka saka kowacce a Mitar da za"a kaita gidan Miji suna kuka suna Daga ma iyayensu Hannu.
Su ya jaleela da su ya Nazifa da su ya Fatima duk suna Kofar gida bakin Motocin suna sallama dasu sauran matan suna daga cikin gida.
Daya Bayan Daya Motocin Amaran suka tashi sai fatan Allah yakai Lafiya sannan mata suka koma cikin gida.
Alokacin ne Danmallam suka cikin gida da Aliyi suka gaisa dasu Hajiya sannan yace Aliya ta fito su tafi sai da taje ta ma Hajiya sallama ta bata kayan Cincin na biki tana ta Godiya.
Kafin La"asar suka wuce Bayan sun Rabu kan suma suna nan zuwa.
Sallar la"asar kadai yayi a anguwan ya Shiga Mota ya koma gidansa ya kwanta Saboda Hayaniya.
Zuwa Dare gabadaya Amaren Dake nesa sun isa Mazajensu sun kira Baba Maallam suka shaidamai sai Hamdala gidan kuma sai aka Fara Hada kayan Tafiya zuwa gobr hatta su Ya Jaleela ma Baba Mallan yace kada wacce ta kai mai jibi agida ya Jadwa ne kadai zai Dagama Kafa sai visan su ya fito.
Ya Akila da ya Fatima gobe zasy bi mazajensu su koma su jidda ne jibi zasu koma ammh gobr zata ce zata tafi Dutse zata sauka bayan tagama ganin Dakin kanwarta ta wuce kano..!
Su hanne sai Dare suka ga Amina adakin Mamanmu taci kukanta ta Share hawayenta duk yadda suka so su Zolayata yau Amina bakinta ya Mutu kazil batace ba haka suka kwana gari na wayewa sun sani suka Fara shirin tafiya Harda harta su ya Abida kuwa.
Kafin su tafi sukayi sallama da Zafira aranar zasu tafi Allah Sarki Sabo kamar kada su rabu,ko kafin su Dawo makaranta da yammah yan gusai sun koma,gida ba kowa sai goggo Husai da Ya Jadwa da Ya Jaleela da gobe jirgi zatabi zuwa Lagos ya Jawahir ta bi yan Gusai sun koma.
Ya Zahra ma ta tafi jirgin yammah tabi ita da Mijinta Daman yazo Daurin auran sai ya Zulfa da gobr zasu koma ita dasu Ya Uzairu su ya Nazir da Matarsa tun safe suka hau jirgi suka koma Lagos.
Chan gidan Baba mallam ma kowace Danginta sun tafi yan maiduguri kadai suka Rage sai gobe zasu wuce Ya Jidda ta Sakina da Sarood sun tafi Dutse tun Safe,Danmallam yaso ya hanasu Tafiya Hajiya tace ya barsu su tafi sai gobr zasu dawo.
Ta bangaran kowacce Danginta sun Tafi Sai daidai su Baba Lami nata Faman gyaran gidan.
Koda sukaje Hadda Amina bata manta ba sai da Taja Mariya da fada aka Fitar dasu Waje Mariya ta rika yima Amima Allah ya isa.
Ta kalleta tana Dariya kafin tace"Allah ya isa taki ce awajen Amina kin ga kaina tafi Dubu..
Take fada tana ma Mariya gwalo sai Da aka tashi Hadda aka Sallamesu da aka shiga islamiya ba haka ta Dinga Tsungilinta sai da aka kara Kadata waje.

*Janafty*[11/3, 2:05 PM] Sweet sis: *TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*🅿️14*

Kimanin Sati Biyu kenan da Watsewar Bikin su ya Zulaihat baki na nesa da na kusa duk sun koma Gidajensu Goggo Husai ce mutanen Jordan da ya Jadwa basu Tafi da wuri ba saboda Mtsalan Visa sai cikin Satin nan suka samu tafiya.
Amara suna gidajensu cikin Koshin Lafiya sai Fatam Allah ya Zaunar dasu Lafiya Bakim Madina ne kadai ya Rage basu koma ba suma suna ta Shirim Tafiya cikin karshen watan da muke ciki Zasu fara sabuwar shekarar Musulunci achan Madina din.
Chapter 39 · 0% Book details