← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 193

Sashe 161

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya Aisha tace"To ai ke zaki sashi ya Sauya miki ina ruwanki da sai kin jirasa..Shi da yake da mata Biyu kowacce da sunan data ke kiransa kema sai ki samu naki tunda dai shi balarabe ne ki rika cemai HAbibi..!
Amina ta kalleta a karkace kafin tace"Allah ya tsareni..Habibi fa..Sunan da wannan gajerar matar tasa fa take kiran sa dashi kenan..!
Sai nima na Dauka..!.?
Ai na tasani kwaikwayo sai ta Rainani ma ya Aisha in taji ina kiransa da haka..!
Ya Aisha na Dariya tace"Oh ai bansani bane da gaskiyanki tobari mu sami wani suna ki rika kiransa da Norul kalbi mana..!
Amina ta yamutsa fuska kafin tace"Bai yi ba chanza wani..!
Ya Aisha tace"To Hubby..!
Amina tayi shuru kafin tace"Hubby..?
To har gwara ma wanman..!
Ya Aisha tayi dariya kafin tace"Yayanmu ya shiga uku..ya fada komar Aminenen hajiya da mallam..!
Amina na Dariya tace"Ko zaku Cirosa ne..?
Ya Aisha tace"Ina fa ai muna jin Dadi..Acigaba da kula mana dashi Allah ya kara kauna da soyayyah..!
Amina tace"Shi yace miki yana sona..?
Ya Aisha tace"Basai ya fada..Kowa ya ganki ai yasan kun fadama juna..!
Amina ta Hura hanci kafin tace"Ku ke gani ba..Ammh ai matansa yafi so akaina..!
Ya Aisha Dariya kadai take ma Amina Cikin zolayarta take kara gayamata Wasu sirrukan zama da miji,Amina ta Bude kunne tana Saurara bata da kalmar da zata gode ma Ya Aisha da yakaka zaman ta dasu alheri ga Rayuwarta har Abada bazata manta da gudumuwarsu ba.
Ta Dade a Dakin ya Aisha Sai azahar ta fito ta koma Dakinsu ita da Yakaka tana Shigowa yakaka na goge goranta ta kalleta tana Fadin"Ki rika dan yawatawa Takwarata sai kafafuwan naki su saki sannan ita mai juna Biyu ba"a son ta rika kumewa waje Daya .!
Amina tace"To yakaka ai baki rakani ba yau..!
Yakaka ta mike tana fadin"To Dauko mayafinki mu taka zuwa Haraban gidan..Ai bana ki takama Takwarata ba..!
Duk da dai kishiyatace ke domin kinsan dani komawa madina ba tashi..!
Amina na Dariya tace"Sai kun dawo..Ai ina nan zaki dawo ki sameni in wadanan guzumayen matan nasa suka koroki..!
Yakaka tace"Su har sun isa..?
Ai mu in muka shiga mun shiga kenan Asiri ko tsafi bai isa ya Girgizamu ba..Allah muka rike shiyasa gamu nan a Tsaye ga Kafafunmu..Kainuwa dashen Allah..!
Amina sai dariya take yi ta saka mayafinta tana fadin"Kwarai yakaka mu ikon Allah ne da na mutum ne da Tuni sun Shafe babinmu..!
Yakaka tace"Af keda kika san komai..!
Da haka suka fito daga Dakin Yakaka ce ta leka ta fadama Aisha sun fita takawa ita da Amina ta musu fatan Dawowa lafiya haka suke yi tunda Cikin Aminar ya tsufa.
Yakaka kitchen ta shiga suka gaisa da Saude ta Daukan musu ruwa suka fice Tunda in Amina najin tafiyar har karshen Layi Yakaka take janta iyaka in sun gaji su zauna Amina ta sha ruwa ta huta.
Sai da suka kai karshen Layin Maitama sannan suka juyo suka Dawo suna tafe a hankali suna Hira sama sama har suka dawo kuma Amina hakan ba karamin taimaka mata yake yi ba sai da suka dawo sukayi sallah Sannan suka zauna suka ci abinci Amina tuwo taci miyar kuka wacce Tun jiya Saude ta mata shi.bayan tashi ta koshi sai kuma ta kwanta ta Huta Daganan sai barci karar wayarta me ya Tada ita Daga barcin daman bata wani barci mai Nisa Tunda Cikinta ya tsufa..yakaka Dake Dakin ta miko mata wayar tana Daga kwancen tace"Gashi nan tun dazu ake ta kira..Ina jin mijinki ne to ban da ma shi ba wazai kira..?
Amina ta amshi wayar yakaka sai ta fita kamar yadda ta Saba ta bata wuri.
Sai da ya kara kira ta Dauka Cikin Shakewar murya suka gaisa jin yanayininta yasa yace"Meke faruwa ne..?
Kai Tsaye tace"Me ka gani..?
Dagachan bangaran yace"nayi ta kira baki Dauka ba..Sannan yanzu kuma kin Dauka naji muryanki ta Chuse fata dai ba jikin bane..?
Amina ta muskuta ta mike Zaune tana Fadin"Lafiya lau na dan kwanta ne shiyasa ban ji kiran wayar ba..!
Kai ya gyada kafin yace wani abu kawai yaji tace"HUBBY..!
Tsayawa yayi yana Tunanin ko dai bada shi take ba sai da yaji ta kara maimaitawa"Hubby..nayi kewarka sosai yaushe zaka taho..?
Danmallan Dake Cikin Office dinsa bai san sanda yayi baya da kansa kan kujeran Dayake zaune har da sabule Hula yana Shafa gashin kansa..
Cikin wani yanayin Farincikin Dayake Ciki yace"Yau nine Hubby Amina..?
Yaushe na tashi Daga ya danmallam din..?
Bakinta ta Tura kafin tace"To ko baka son sunan ne..?
Da sauri yace"Wa ne ni..?
Sosai sunan yayimin dadi..Sannan nima ai ina kewarki sosai..Zan dawo Cikin Satin Bikin insha Allahu kada ki Damu nima ina son nazo na ganki ke da Abunda ke Cikinki..!
Amina ta murmusa kafin tace"Ammh ai nima baka sauyamin suna ba..!
Dariya ta basa yasa ya Murmusa yana Fadin"Waya fada miki..?
Amina tace"Ai ban taba ji bane..Da fa Amina kake kirana..!
Kai Tsaye yace"Uhm kece dai baki Taba jiba..Ni nasan sunan da na saka miki Acikin raina sannan dashi nayi Saving din lambarki a wayata. !
Amina tace"Don allah ka fadamin..!
Make kafada yayi kamar tana gabansa yace"Naki bazan fada ba. !
Amina ta fara Shagwaba tana Fadin"Don allah fa nace..!
Kuma ai ni na fadamaka sunan da na saka maka..!
Jin zata faramai kukanta na Fama yasa ya Dakatar da ita yana Fadin"Tsaya Tsaya.kafin ki faramin wannan kukan naki da bayajin Lallashi..Ai ke NOOR ce..Haske ce ke Amina acikin Rayuwata Tun da kika shigo Rayuwata nake ganin haske kan komai nawa sannan nake ganin Daraja kima da martabawa wajen Iyayena sannan suke kara sakamin albarka da godiya gareni..Daga nan na Fahimci ke haske ne ga Rayuwata..!
Amina sai ta fara Hura Hanci tana jin Dadi sai wani Blushing take yi Cikin Fara"a tace"Da gaske ni Haske ne awajenka..?
Yana shafa kirjinsa yace"Ki bari nazo ,zan kara tabbatar miki Noor..!
Amina ta washe baki ta kasa mgana Dadi take ji akan ranta Cikin wani yanayi yace"Ya Bby na..?
Yau yayi motsi kuwa..?
Amina tace"Dazu muna dan takawa ni da yakaka sai naushi na ake yi aciki..!
Tafada Cikin yar shagwaba har da Jan hanci Danmallam yayi dariya Amina na jinsa sai ta sakamai kuka tana Fadin"Dole kamin Dariya tunda kamin Ciki ka tafi ka barni da wahala kana chan kai da matanka kana jin Dadin ka shine har kana min Dariya..!
Ya rude Hankalinsa ya tashi ya fara Lallashinta yana fadin"Wani jin Dadi baki kusa dani..?kinsan Allah ni fa kina Haihuwa zan taho Dake nan bazan jura zama baki kusa dani ke da abunda zaki haifa ba. na riga na samar Miki Shaidar zama a kusa dani..!
Amina jin haka yasa tace"Da gaake..?
Yace"Sosai ni dai kimin alfarman ko Hajiya tace bata yarda ba kice ke Zaki bi mijinki abunki..!
Amina ta fara Dariya tana Fadin"Wlh ba ruwana..!.
Wai shi zai mata wayau yana Fadin"Au baki son ki koma garin da Monzon Allah sallahu alaihi wasallam ya Zauna..?
Baki son zuwa makka ne kiyi Hajji..!
Amina tace"Ina so naje..In na ganni a gaban ka"aba Hubby kasan me zan fara roka..?
Yace"A"a Noor..!
Amina tacigaba da Fadin"Zan duka in Dafa ka"aba in rokar ma yaya Afuwa da salama sannan na roki Allah ya Hadamu a darussalam..!
Kai Tsaye yace"Allah ya Amsa ina jinki sai me zaki roka..?
Amina tace"Zan rokar ma Hajiya da maallam gamawa da duniya lafiya..Sai kuma Aba shima zan rikor masa kwanciyar hankali da Zama lafiya da wadata..!
Danmallan yayi Tagumi kafin yace"Sai kuma me zaki Roka..?
Amina tace"Sai kuma na roki Allah ya bama mijina Wadata na alheri Allah ya Zaunar damu lafiya Allah ya karamana kaunar juna ya shiryamana abunda Zamu haifa ya bamu ikom Musu Tarbiya bisa Amana da koyarwan addinin islama..!
Ayadda take mgana sai da yaji ajikinsa Cikin mamakinta yace"Wani mijin naki..?
Kai Tsaye Amina tace"Kai mana Hubby..dole zan gode maka..Domin kaima ka bani Taimako wajen dawowa da Rayuwata daidai sannan ka aureni Cikin wani yanayin da bakowani Namiji zai iya ba..Nagode kwarai Allah ya baka ikon yimana aldaci..!
Danmallam sai yaji kamar yayi kwallah ashe haka Amina ke da Hankali..?
Kai tsaye yace mata"Ameen Ameen Noor..Allah yayi miki albarka Allah ya Saukeki Lafiya insha Allahu Buriinki Zai Cika kin ji ko..?
Ta amsa mai Cikin jin Dadi,Shuru na wani Lokaci kafin taji yace"ANA BEHABBIK YA NOOR.....!
Amina ta ji mganar kamar Daga sama yasa tace"Me kace..?
Shi a tunaninsa bata ji me yace ba Sabida Labarci ne ya fada sai yayi saurin cewa"Bakomai..!
Kawai sai ta murmusa batace komai idonta ya kawo kwallah haka suka gama Hirarsu sukayi sallama Suna gama wayar ta rumgume wayar akan Cikinta tana Fadin"Ina son babanku..Wlh nima Ana Behabbak Hubby Umar..'
Hawaye ya kawo mata tayi saurin sharewa tasani tana son mijinta so mai tsanani data bata san yaushe ya fara ba Sannan yadda take kishin sa ko matansa basu kaita ba shiyasa ta Tsani ko jin sunansu kamar ma ya sani in suna Hira baya mata mganarsu shine zaman lafiya.
Washegari suka tafi asibitin tunda yanzu duk sati suke zuwa saboda Cikinta ya tsufa.da suka Dawo ne suka Tsaya Shagon salloon aka musu gyaran kai da Gyaran kafa Daman Amina ta Fadama Ya Danmallan yace kada tayi kitso ta bar mai gashin nan yafi son ya gansa haka ya fi bashi sha"awa ita kuma Amina duk abunda Zata Burgesa shi take yi bata Damu da kowa da komai ba sai shi sai Cikinta ke gabanta.

*******
Chapter 161 · 0% Book details