← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 193

Sashe 41

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Y zeenatu ne ta shigo tana ta Fada Fadi take"Wlh Amina ki rika Karisa aikinki..Domin nam gidam ba bawanki..Ni ba Hamida bace Darajan Mamanmu kikaci Wlh..!
Amina na jinta tana Danne Dariyanta Daga kwamcen Tana kallonta kai ta kada kafin tace"Ba Laifinki bane..Mamanmu take Daure miki gindin Iskamci Watarana ai ba Maman ko..?
Naga uban da zai zauna kina wannan iskamcin bai ci ubanki ba..!
Ita dai bata tanka ba har ta gajii da Mitan ta fice bayan Fitar Danmallam Damam Sallama yazo yi ma su Yaya Gobe Jirginsu na dare me zai tashi zuwa Jidda a Filin Sauka da Hawa na Aminu kano.

Sai da ta ficen ne Amina ta fito da Dariyanta tana Fadin"Allah Sarki..Ya Zenatu kawar ya Abida...!
Hamida ta kalleta kafin tace"Ke kam ki tashi ki gyara kayanki Amina Harda fa Sabbi ciki..!
Amina ta kyabe baki kafin tace"In kin Damu ki gyaramin Hamida!
Hamida tace"Na rantse kuma bazan yi Kaffara ba..!
Tsaki Amina taja Kafin tace*To sai ki kyaleni malama!
Hamida tace"Yau anyi Fada da Mariya da Sa"adatu..Har da Dambe sai da mallam Auwal ya Zanesu..!
Da Sauri Amina ta Mike tana Fadim"Don Girman Allah..?
Hamida tace"Wlh suna Zage Zage..Kinsan Hamne da tsoro sai kuka take yi..!
Amina ta Daka Tsalle har da shewa kafin tace"Ahyayyeee...Yau naji Dadi karshem alewa kasa.
daman ai xaman munafunci baya karko..Tacizi yatsa Kafin ta cigaba da Fadin"Naso yau naje..Da sai na kara Yamutsa wajem munafukai..!
Hamida tace"Gwara dai da baki je ba..!
Amina ta balla mata kafin tace"Ga Shedan ko..?
Hamida kina shigarmin hanci fa ki kyaleni.!.
Hamida tace "Daga Fadin gaskiya..?ai ba karya nayi ba Da kin nan wajen Allah kadai yasan iya inda abun zai kai..!
Amina ta karkace baki kafin tace"Hanne wai me aka mta take kuka..?
Hamida tace"Me kuwa..?tsoro gareta Taga suna Ta kwasan Dambe..!
Amina tace"Aikin banza Hanne banza ce..Me abun kuka..?
Allah ya Tsareni..!
Hamida dai bata kara mgama ba Domin Har ga Allah taji Dadin da Amina bata zo ba Domin Allah kadai yasan Iya inda Fadan nan xai kai Amina sai ta hau Fadan ta siyeshi ta kara Maggi da gishiri.
Waashegari Da Safe ta shiga wajen Hanne ta iske Su Sakina suna gidan suma ta shirin Tafiya Ya Jafar zai kai su kano Ya Nasir yana da aiki A asibiti.
Amina ta kalli Hanne tana Fadin"Wai ganin ana Fada da Sa"adatun ne kike kuka..?
Hanne tace"Ni bana son ganin ana DAmbe ne..Ko kike kike Fada ai ina kuka..?
Amina tace"Wlh karya kike yi..Natan Dai kike kuka ke mai yar"uwa Ki kama Kanki Hanne Domin in kece Dariyama zata yi kina abu kamar wata sakarya..!
Hanne tace"Bakomai naji..!
Kinsan yau su ya Danmallam zasu koma..?
Amina ta tabe baki kafin tace"Jiya sun zo gidanmu naji Mamanmu na Fadin..!
Dukkansu zasu koma..?
Hanne tace"eh mana..!
Amina tace"To in suka tafi sai yauahe..?
Hanne tace"Yace ma Hajiya sai wani abu ya taso..Im bai taso ba sai nan da wata Shidda zai zo..!
Amina tace"Allah ya tsare..!
Aranta kuma Fadi take"Allah ya raka taki gona..!
Lallabawa tayi ta gudu gida abunta batama san Tafiyarsu ba su yaya dai da mamanmu sun je sun karayin musu sallama sai yamma suka Dawo suna Fadin wai har ya Jafar ya Kira suna kano basu dai tashi ba sai Dare.
Sai washegari wajen chan Rama taji ana Fadin sun sauka a jidda Daganan zasu hau Mota zuwa Madina ko ajikinta Sai taji kamar wani Nauyi ya tafi Bata ko kaunar ganinsa ma ballatana jin muryansa.

Bayan wata Daya..!
Amina na kwance da Safe tana barci Taji ihun Hamida asaman kanta tana Dukanta Lokaci Daya tana Fadin"Amina tashi..Tashi.!
Next week zamu fara zuwa makaranta an gama mana komai..!
Amina da sauri ta Bude idanuwanta cike da barci tace"ke a ina kika ji..?
Hamida tace"Yanzu naji Ya Jafar yana Fadama Mamanmu..!
Amina tace"Ina zamu koma..?
Hamida tace"Ina kuwa..?Unity...?
karamin tsaki taja kafin ta gyara kwanciyarta Tana Fadin"Yanzu dai chan zamu koma..?nifa na Tsani Unity din nam..Allah yasa banda munafukar nan Sa"adatu..!
Hamida tace"Kema kin sani..Gabadayanmu ne..!
Amina ta Yamutsa Fuska kafin tace"Ban so ba..!
Naso kowa ya kama gabansa..Ke ni fa Wlh nafi son zaman gidan nan akan komawa Shegiyar Unity din nan..!
Hamida tace"Ke yanzu zaman bai isheki ba..?Tab ni Wlh na gaji..!
Amina tace"Da an bari Second Term sai mu fara zuwa..!
Hamida bata bi ta kanta ba ta Fice tana Murna Amina ta Bita da kallon Na Tsausaya.
Da yammah ma sai ga Hanne tazo suna Murna ita da Hamida Amina tun Tana Daukan mganar wasa sai gashi ta Tabbata an kawo musu sabbin kayan makaranta na Senior da Jaka da takalma Da Safa da Sabbin Littafai ya Shamsu yakawo musu nasu Ranar Monday zasu fara zuwa.
Kowa na Murna banda Amina Tsakani ga Allah Hutun bai isheta ba ta so sai Second Time su koma makaranta ammh Ina ba wanda zai bar su su zauna agida ana kallonsu Takaicinta Daya Sa"adatu bata kaunar su na Hada Hanya don bata da yarda zatayi ne kawai.
Har ya Zeenatu sai da ta mata mgana Tana Fadin"Ke Amina Hanne da Hamida na Murnan Jjc yan SS1 KE banga kina yi ba..!
Amina tace"Murnan me..?Unity ce fa..?Daman wata kayan gabas ne ba nan ba..Ni gabadaya makarantar ta isheni..!
Ya zeenatu tace"Kina da aiki..Tun Zamamin su ya Nasir Unity ta kenkyshesu ballatana ke Zuwan yau yau..Yarinya Unity Dolen kowa ne indai Dam nan gidan ne ko dam Gidan Baba Mallam..!
Amina baki ta Tura bata kara mgana ba Ganin yadda ya Zeenatu ta Tsakal kale,Tana ta bayani Hamida na Tayata su adole suna kara yabon Unity a wajemta Tabe baki tayi aranta tace ko Ta Tsani makarantar nan ba Sauyi kowa man yayi ya gama suma kuma nan din zasu gama..!

*Janafty*
[11/3, 2:05 PM] Sweet sis: *TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*🅿️15*

*Jumma"a*
9:00am
Chapter 41 · 0% Book details