← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 193

Sashe 34

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

kan hakkokim mata akan Mijinta kafin ta gangaro kam Hakokin miji kan matarsa sannan ta bada Shawarwari sosai da kuma Mgugunar karin Ni"ima bangaran isalama domin Taimakom mata Hamida ta taba Amina tana Fadin"Ku Tsaya ku Saurara Wlh mgangunta akwai amfani aciki..! Amina ta saki Tsaki kafin tace"Dilla mu kyakemu ta ina zai amfane mu..?ko kina cikin Amaran ne Hamida? Hamida tace"A"a abun ba bakar mgana..Ko don gabs nake nufi..! Zafira tace"Gaskiyan Hamida mu ma nan da Shekara Biyu muma amaran ne..! Amina ta saki Tsaki kafin tace*Sai ku jira Lokacin..Me kuke ci na baka na zuba..? Ba wanda ya tankata ita kanta Hanne ta maida Hankalinta kan malamar ganin haka yasa Amina ta maida Hanlinta itama Sai tabe baki take yi Domin ita bama wani fahimta take yi ba. Shida saura Mintuna aka gama Wa"azin bayan an gama su ya Abida suka fara rabon su Jakunkuna da Karamin Frame na Ayatul kursiyi da su ya Aisha zata raba Daga bangaransu. Sai ya Zeenatu da ita da kawayenta suna ta Rabinsu Turaran tsinke da Memo na ya Zulaihat su Sa"adatu kuma suna ta Rabon Turaran Wuta na Rushi,da su Sabulun Salo harda Fallen Atamfa,acikin Wata Katuwar Leda da mafitai na zamani. Bangaran Haj.Nasara ma su na ta Raba Kananun Kofuna da Kuma Mug na shan Tea abun sai wanda ya gani. Kowanne sai da su Amina suka Dauka ba"a sani ba Har da su Sa"adatu Amina tace"Da kudin Baba Mallan akayi sai mun dauka..! Hamida na Dariya tace"Amina kina da Karfin Hali..! Amina ta balla mata Harara,sukayi Dariya kafin ma atashi suka Gudu gida Saboda kada asasu wani aiki kamar kuwa sun sani ana ta Cigiyansu su taimaka a kimtsa wajen aka nemesu aka rasa sau su Ya Abida suka Bige da aiki chan aka barsu a makaranta bayan sun gama Sallaman malamansu maza Hajiya kuma ta Sallami Malama Hafsah da tazo tayi Wa"azin mata. Duk a kasa suka koma gida su Ya Nazeem suna masallaci wajen Karatun Baba Malam. Sai Bayan mangariba su ya Abida suka Dawo amaran kaf suna Shashen Hajiya Babba nan Zasu kwana Har sai gobe bayan Daurin auran za"a kai kowacce shashen Mahaifiyarta na karshe,Shine Falon Baba Mallam inda shi da Aba da kuma su ya Danmalam manya inda za'ayi musu Nasiha Tare da mazajen nasu sannan kowacce a Damkata Hannun mijinta. Su Amina ko Abincin Dare basu ci ba suna ta cin kayan Fulawa Hamida tace"Kada ya danne mana zuciya mu kasa tashi..! Amina tace"Dillah zuwa gobe da Safe ya Sabbabe..! Sai da suka cinye kusan duka Sauran su bama yara har suka koma suka kwanta suna Hira Daganan sai barci.
Chapter 34 · 0% Book details