← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 172 OF 193

Sashe 172

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Anty Amarya bata iya kallon mallam ba Saboda yadda taji muryansa ba wannan amon ballatana karkashi Abunda ke Faruwa ya Dakushe komai Tana sharan Hawaye ta Cigaba da Fadin"Ni burina shine na Zama Tauraruwa a wajenka..Na zama ni ce agabanka kafin kowa..Sannan Burina na zama na Dara duka matanka a wajenka..Sai dai ina burina bazai taba Cika ba indai Hajiya na Duniyarka na yi barnar kudi akan ka mallam da Hajiya Saboda kawai na Zama Tauraruwa a wajenka sai dai hakan bai Samu ba kowani aiki baya Tasiri akan ku saboda kun rike Allah sannan ko acikin Wani Hali baku daina ambatonsa ba. !
Sannan tun zuwana gidan nan na Fahimci Hajiya ta yi mana Fintikau,Komai naka itace,Daga ita Sai SA"IDU sune kadai suke gabanka da su kake shawara sannan uwa uba Sa"idu ne ke jan Ragamar Duka Dukiyarka nayi iya Bakin kokarina na Raba hakan sai dai ban cimma gashi ba..Sai na Sauya shawara da taku..Na Fahimci in ni bazan zama Tauraruwa ba ta Sanadin Sakina zan iya Cika Burina Har fiye da yadda nake Tunani..!

Tunda ta ambaci Sakina Danmallam ya zura mata ido yana kallonta sakina kuma jin an zo wannan gabar kawai sai ta kara Volume din kukanta ta soka kanta Tsakanin Cinyoyinta tana gunjin kuka ko Aliya Dake gefenta bata da karfim gwiwan lallashinta.
Anty Amarya na jan Hanci da majina ta Cigaba da Fadin"Har ga Allah Lokacin da na Dauko Sakina ta zauna awajena da zuciya Daya ne sai daga baya..Data fara girma na Fahimci Tana matukar Kaunar Umar in ta gansa ta Dinga mai rawan jiki kenan shi kuma alokacin bata gabansa ita da su Jidda da su Nazifa duk Daya ya Daukesu..Ban tabbatar ba sai da na Samu Sakina mukayi mgana ta Nuna min in ba Umar ba bazata iya auran kowa ba Daga Lokacin na hango Cin ma nasarata ta bangaran Sakina..!
Ni na shiga na fita na Karkato da Hankalin Danmallan akan sakina..Duk da alokacin akwai ya"yan malamai manya wadanda suka fita komai da suka so su hada zuru"a da Maallam kwatsam yace Sakina yake so..Nasam ko Hajiya alokacin tayi mamaki Sanin ba wata alamar Soyayya a Tsakaninsu sai dai sanin ita bamai yawan maida kai kan sha"anin Umar bane yasa bata nuna komai ba ko a Fuskarta ba..!
Hajiya ta jinjina kai tabbas ai Biri yaso yayi kama da mutum Rana Tsaka Danmallam yace Sakina yake so ashe Ba yin kansa bane lalle Allah shine Sarki.
Anty Amarya tacigaba da Fadin"Mallam kuma bai nuna komai ba sai ma farinciki zai yi tuwona maina..Tunda yarcda ya rikeni Sakina Tsakani ga Allah haka yake rike da ya"yansa Daya Haifa,ammh duk ban gani ba Zuciyata ta kekashe da cikar Burina..!
Ban yi salama ba sai da aure ya Kullu Tsakanin Umar da Sakina sannan naji Hankalina ya kwanta sannan na sanya aka doramai shakkar Sakina da Duk abunda zatamai bazai taba gani ba ballatana ya Dauki mataki akanta Shiyasa sai tayi ta yin abubuwa bai Taba Daga ,kai ya Dubeta ba Sannan wannan aikin mai girma ne Tunda shima yana da Tsari ajikinsa Dakyar aka samu nasara akansa..!
A wannan gabar ne muka Hada hannu da Balaraba wacce ainihin sunanta ne Dayyaba..Ni kuma marliya nake ammh ana Kirana da Madina sai muka juya sunayemmu Domin kada Bacin rana a fahimci in da muka Dosa..!
Ni na kai Balaraba wajen malamin Dake min aiki anan Dutse Bukatarta ta Farko shine ayima Jafar mugun asirin da zai Fandare ya zama gagararree ya bi Duniya ya lalace kada yaji mganar yaya ballatana ta Sa"idu ya Zama YA FITA ZAKKA Acikin Dangi wanda Daga karshe Sa"idu zai gaji ya tsine mai kada dai ya amfana da Haihuwarsa har Abada..!
Sai akaji goggo Husai ta saka Salati Tana kuka tana Fadin"Innalillahi..Ammh wlh Balaraba kin cika bakar muguwa azzaluma..!
Sai kawai ta koma ta zauna tana Fadin"Allah yayi gaskiya..Zai Tsare bawansa a duk inda yake..!
Jafar kuwa ko Dagowa bai yi ta kasan Inda yake zaune Hawaye ne ke Digar masa Danmallan kuma Hannayensa Jimke Cikin na Amina tun labarin Anty Amarya na Sanadin Auransu da Sakina yake ta Hailala acikin ransa..!
Mamanmu kuka take yi kamar ranta zai fita ita da Anty Amarya da suka san yau komai yazo karshe..!
Ba wanda yace musu kala su kansu ya"yansu zuwa Lokacin sun Fahimci komai ban da tashin kukan au bakajin komai afalon..!
Mamanmu na Toshe kukanta ta Cigaba da fadin"Sai dai an samu matsala..Aikin sai ya kuskure maimakon Jafar sai ya Sauka kan AMINA tun Yaya nada Tsohon Cikinta alokacin..!.
Sai kallo ya koma kan Amina wacce ta kifa fuskarta kan hannun ya Danmaallan tana ta kuka,mamanmu na kallon Amina ta gyada kai tana fadin"Tabbas abun bai sauka kan kowa ba sai kan Amina..Mallam din da kansa ya fadamana haka ni da Madina da muka koma da Korafin aiki bai ci ba..Ya sanar damu aiki yaci Sai dai ba akan Jafar ba,akan Abunda ke Cikin Yaya..!
Alokacin gani muke kamar wasa sai da Yaya ta Haifi Amina sannan muka gasgasta kowa yasan tun Haihuwan Amina ta fita zakka cikin ya"yan gidan da kowa ma,sai kuma nayi amfani da kissa na,na rika jan Amina ajiki ina nuna nafi kowa sonta tunda kowa baya kaunarta Saboda Rashin kunyarta da Kuma Yadda ta addabi kowa ban so Amina ta tsaya haka ba naso ne ta Lalace tabi Duniya ta Zama Karuwa sai dai ina burina bai Cika ba Allah ya Tsare Amina duk Rashin kunyarta bata mu"amala da maza ba Sannan Tarbiyan gidan su data gidam Baba Mallam ta Zauna mata Daram Sannan Allah ya Tsareta da Fadawa wannan Halakar..!
Duk soyayyar da nike nuna ma Amina na karya ne bayan Sihirin Dake tare da ita nima na bada tawa gudummuwar wajen kara Lalata Rayuwarta,Ban taba mata Fadan tayi ba Daidai ba,Duk da alokacin in na Fadamata zataji Domin na Fahimci Duk Duniywa bayan ni da su Hajiya Amina bata yarda da kowa ba sannan tana kaunata Fiye da yaya data kawota Duniya da hakan nayi amfani na Gurbata rayuwar Amina ban taba bari ta ma kanta wani abu ba bana so watarana hakam ya amfaneta sai na Zabi na Sangartata kada ta iya komai ta tashi ahaka ta kuma rayu ahakan na Tabbata watan watarana sai haksn ya Zama illah agareta.
Saboda irin Kaunar da nike nuna mata ba wanda ya taba Fahimta ta Komai sai dai in saka Hamida Amina kuma na Dauketa wata Shashasha ce da bazata iya moran rayuwarta ba Sannan na kara nesantata da Mahaifiyarta yar da har Yaya ta koma ga Allah Amina ko da na Minti Daya bata taba rabarta ba. !
Amina ta Dago jajayen idanuwanta tana kallon Mamanmu kallon Tsana da wani Bakimciki haka Hamida itama da su Zulfa suke kallonta Cikin kyama da wani Takaici Aba dai bai Dago kansa ba har alokacin..!
Mamanmu bata Damu da kallon da suke Binta dashi ba ta cigaba da Fadin"Duk abunda kuka ga Amina nayi ba yin kanta bane..Tana da Sihiri ajikinta sannan da Shafar aljanu su suke sakata ya wan tsorata da kuma Mugayen mafarkai sannan duk abunda ya Faru da Amina kan Aminu na sani ammh ban taba Hanata ba..Ban kuma nuna mata na sani ba da Gangan nake ijiye wayata in da Zata gani saboda ta Dauka alokacin Naso ne Aminu ya lalata Amina Ya yi mata Cikin da zai yi Sanadiyar tsarwata zuciyar Sa"idu da yaya Tunda na Fahimci har ahakan Kaunar da suke ma Amina na Dabam ce ta fita zakka ko acikin ya"yansu ita din mafi
soyuwarsu ce..!
Wannan Karon har Hajiya sai da ta Saki Salati Amina taji kamar dan Ciikinta ya juya ta fara Kokarin tashi Daga jikin Dannallam kawai sai ya kamata ya Rumgumetw zuciyarsa na Bugawa Fat Fat ammh bai Daina kiran sunan Allah ba kada ya rasa natsuwarsa Amina ta nitse Cikin kirjinsa ta wani Fashe da wani marayan kuka Mamammu ta Cutar da ita Cutarwa da bazata taba iya yafe mata ba..!
Mamanmu kanta na kasa tacigaba da Fadin"Sai dai Burina bai cika ba..Allah ya tsare Amina Daga tarkona..Acikin wannan tsukin mallam ya Shammacemu ya Daura mata aure da Danmallam auran daya sa na Harzuka Madina ta harzuka itama,Auran da shine Silar Sanadin mutuwar YaYA..!

"KARYA KIKE YI..Hadiza bata mutu ba..Ke kika KASHETA Balarabaa..!
Chapter 172 · 0% Book details