Sashe 29
Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gammu a waje sai yayi mana mgana..! Amina tace"mu tafi gidan su ya jafar inda su ya zulaiha suke muga abunda suke achan..! Dukkamsu sukayi Shiru suna kallon Amina kafin tace"Dilla mu bi ta nan baya bamai ganimmu..!. Jin haka yasa suka yarda nan da nan suka Zaaya suka bi ta baya suka fara Tafiya akuyan Daure ta samu Sake sun san gidan Dayake ba wani Nisa Sosai a kasa sukaje sai gasu abakin get din gidan Amina ta fara buga get din gam gam..gam gam.kamae zata Fasa kofar Daga chan sukaji Muryan Abida tana Fadin"Waye haka..?ana zuwa kada ya balla get din..! Ido suka gwalo sun san Halinta kafin suyi mgana ta Bude get din Tana kallonsu tasha kunshi ja hannu da Kafa Hararansu ta farayi Daya bayan Daya kafin tace"Daman Araina sai da naji kune..To kima uban me kuka zo yi..?ko nan da sa"anninku ne..! Amina tayi Saurin cewa"Mufa mun zo mu amare ne..! Abida ta ballaa mata Harara kafin tace"ku musu mene..?kaji min yara da iyayi to bAzaku shiga ba ku juya ku koma..nasan ba wanda yasan kun fito Daga gida..! Hanne tace"Muna ganinsu zamu tafi ko Amina..? Da Sauri Amina tace"Eh Wlh..muma kinga basai amana irin kunshinki ba..ko Hamida..! Gabadayan su suka amsa Domin su ba wanda yabi ta kansu ma mganar kunshi gwara Hanne da Hamida suna ma kansu Amina kuwa sai dai in Mamanmu ce ta kamata ta kunsa mata. Abida ta Daure Fuska Kafin tace*To wlh bazaki shiga ba irin lalle na ko..?ni sa"arku ce..?kuna yara da ku sai son shiga cikin manya dillah ku wuce ku bama mutane waje..! Amina ta tura baki kafin tace"To mu leka..!? Abida tace"To leka..!. Da Sauri Amina ta Zura kai ta wajen Hannun Abida Data Bake get din zata Leka taji ta Daketa abaya Dayasa ta Dawo da kamta da Sauri Abida tace"Matsa ku bani waje..Marasa kunya kawai ba sa"anku anan..! Tana gama Fadin haka ta fara kokarim maida get din Amina ta kalleta tana sosa inda ta Daketa da karfi tace"Dadin abu ai ke ba Amaryan bace Ehe..! Tana gama Fadin haka ta Zura da gudu su Hanne suka mara mata baya Abida ta saki tana kallonsu afili ta Furta"Yaran nan sun bala"in Raina ni..! Kan bala"i zamu hadu ne duk sai kun ci ubanku..! Tafada kafin ta maida get din ta Rufa suna Shashen ya jafar ne sso Hayaniya suke Dayake Duka yan"uwan Hajiya daga Maiguduru ne sukayi musu Lalle da Kitso da kuma gyaran jiki nan suke kwana Anty Shamsiya yau chan gida zasu kwana ita da Fadila. Daganan da suka fito sai da suka kusa gida suka Daina gudu suka Duka suna Hutawa Amina ta Dago tana Haki tace"Ya Abidar nan muguwar yar bakin ciki ne..! Ta hanamu shiga mu gani ance ana ta mu su gyaran Amare..! Hanne tace"Eh su yakura ne fa suma tun ranar da sukazo hajiya ta turosu nan..! Amina tace"Ai dai zamu gansu gobe duk Tsiyanta nifa daman tundanaji muryanta nasam sai ta bamu mtsala..! Zafira tace"Mata da kirki ne..? Amina ce"Ko kadan..Bata da mutumci ya Abida kina ganinta haka..! Gabadayansu dariya suka saka Amima ta Cigaba da Fadin"Ke kinga gidansu Hanne..?Kaf ba mai mutumci yasin..! Hamida tace"Kai Amina ga ya Danmalam ai bai taba Dukanmu ba..! Amina tayi jim kafin tace"Shi kuma wannan dama dukan yake yi da Mganarsa..! Hanne da Hamida suka Kalli juna suna Danne Dariya Amina ta gansu ta Hararesu tana Fadin"Munafukai..! Zafira tace"Me ya faru ki bani labari..? Da Sauri Amina tace"Wlh kuka Fada mata sai nayi muku Rashin Mutumci..! Dariya suka kara saka mata ta kwalo musu ido Zafira na magiyqn su Fada mata Amina ta Faki idonsu tace"Wayyo bayanku maciji..! Ai bata gama Rufe baki ba suka Zura aguje tabi bayamsu tana Dariya. Allah ya taimakesu sanda suka Dawo an shiga Sallar mangariba sai suka Lallaba suka Shige gidan Baba Malam. Shashen Hajiya ba waje duk ya cika duk da wasu suna Kitchen din gidan suna ta soyankaji su da su Baba Lami yan aikin gidan. Karahenta dai Shashen Hajiya uwa suka Shige sukayi salla adakinta ita bata ma nan tana Shashen Hajiya taje suna mgana.. Sallar kadai sukayi suka Fito su leka chan su leka har shashen Anty Amarya sai da Amina tace suje saboda tana son ta kara ganin gulma Akwai suna shiga suka iske Sakina da Sarood zaune kugu Daya Jidda na Kan Cafet tana ta Hada Turaran wuta da Sabulun Salo cikinwasu kananun Robobi ita da wasu Daga cikin Dangin Anty Amarya..basu ga Sa"adatu ba bata nan tatafi kunshi an samu Sake. Hanne ne kadai da Hamida suka gaida su Sakina banda Amina Data yi keme keme Anty Amaryan bata Falon. Anty Sarood ta ganesu tana ta yi musu Mirmishi. Sakina taga Amina na wani kallon ko Daya Daya yasa tace"Ke..Baki da kunya ko..? Baki iya gaisuwa bane..? Amina ta yamutsa Fuska kafin tace"Na gaisheku..! Sakina tace"Karya kike..Hanne kadai da Hamida suka gaishemu da wannan yarinyar..! Ta fada tana nuna Zafira. Amina ta Tura baki batayi mgana ba Jidda ta dago tana kallonta Kafin tace"Wai Amina daman baki daina wannan Rashin ta idon ba ko..?ko ni ai baki gaisheni ba..! Amina ta yi wani jim kafin tace"Ina yininku..! Daga haka ta juya tana Jan hannun ZAafira Dake kusa da ita. Sakina ta rike baki kafin tace'Yarinyar bata da kunya..! Amina na kunkuni tace"Eh din ai na gaisheki tunda kuma ba Duka miki zan yi ba..! Da karfi tayi suna ji ta fice Jidda ta girgixa kai tana Fadin"Kamar ba yar gidan Baba Sa"idu kaf ya"yan gidanan ta fita zakka..Allah ya shirya..! Sakina batayi mgana ba baki kawai ta Tabe ta juya tana ma Sarood mgana Wacce ta maida hankalinta Sakina na jin Labaraci tun anan balle kuma Da suka koma chan Zama da Larabawan yasa yaran ya zauna mata sosai. Kitchen suka shiga suna neman abinci sun samu Jallop din shimkafa da aka Dafa da Rana. Amina idonta na kan manya manyan Baho cike da Naman kaza da Naman rago duk am soya Amina da nama Tuni Ranta ya biya. Akitchen din sukaci abinci suna cikim ci Amina tayi ma Hanne Rada"Yasin sai na saci naman chan..! Hanne tace"In aka kamamu fa..! Amina tace"Dillah bamai ganinmu..! Har suka gama cin abinci Amina na Tunanim mafita Su baba Lami na Kitchen da sauran mutane suna ta aiki kowa Hankalinsu baya kansu Anty Nasara ce ta shigo ta gansu yasa tace"Me kukeyi a kitchen..? Kuje waje mana ku sha iska..! Dole suka fice Hanne nama Amina Dariya ita kuma tayi Fuska Shashen Hajiya suka koma suka samu chan gefe suka zauna bama wanda ya Lura dasu Amina aranta tana Takaichun yadda in ana sha"ani bamai bi ta kansu aranta tace ai suma sun girma sun wuce yara yansu. Suna nan har akayi sallar Isha"i suka tashi sukayi salla. Sai alokacim Hajiya ta gansu tace"kuna nan ashe..?na zata kuna gidan Sa"idu ne..! Hanne tace"Tun dazu muna nan..! Tana Sauri ne ana mata mgana yasa ta wucesu Amina tace"Kowa baya bi ta kanmu..! Hamida tace"Wlh fa kallemu kamar wasu almajirai..! Amina tayi dariya kafin tace"Almajiran ne mana duk inda mukaje ana koranmu..! Hanne ce ta ma Amina Rada a kunne tana Fadin"Kin fasa satan naman ne..? Amina tace"A"a Ku tashi muje..! Haka suka sake ficewa Kitchen din Amina ta leka taga ba kowa sai su Baba lami su kuma suna ta Hidiman yanka Albasa suna Hira Amina ta yafito hanne tana Fadin"Ku tafi daga chan..Ni zan shiga na Debo mana zan taho..! Hanne ta mika mata wata bakar Leda Data Dauko daga Dakin Hajiya tace"Zubo mana anan..! Zafira ce tazo zatayi mgana Amina ta mata alaman tayi shuru Hanne ta mata rada tana fadin"Ke nama Amina zata sato mana..! Zafira tace"Yauwa daman wlh tun dazu miyauna ya tsinke..! Amina ta Sadada ta shiga kitchen din ta Duka ta Bude ledan ne ta rika Zuba Nama Har sai da ta Kusa Cika Hanne da Zafira suna daga bakin kitchen din suka hango Anty Amarya zuwa da Sauri Hanne tace"Amina Ga Anty Amarya nan ki taso..! Jin haka yasa ta taso da gudu su kuma sun riga sun ruga har tana bangaje Anty Amarya,Da tayi baya tana Fadin"Ke ke..Waye anan..! Ina Amina bata tsaya ba sai Aharaban gidan inda su Hanne ke jiransu Anty Amarya bata ga Fuskat Amina ba. Ta shiga kitchen tana yi ma su Lami Fadan suna barin yara na Shigowa. Haraban gidan akwai haske tunda an kunna Gen yasa Amina ta jasu suka shige wanu dan lungu Dake Wajen kofar Shiga Shashen mallan da dan Duhu kadan suka ZAuna Amina ta Fito da Naman Hamida ta zari ido tace"Amina kin Debo da yawa in aka gane fa..? Amina ta tura wani nama bakinta Tunda naman sa ta Debo na kajin suna kusa da Baba lami yau gidan Gonar Baba malam yasha Diban kaji da Shanaye. Sai da ta cika bakinta sannan tace"Dillah kefs kin cika tsoro..Abu da yawa wazai gane..? Zafira ta mika hannu zata Diba Amina ta make hannunta tana Fadin"Kada ki samin hannu ko na Hanaki..! Jin haka yasa ta Dakata Amina ta Dauki Tsoka Hudu hudu ta basu Ta bama Hanne Biyar ta Dauki Sauran tana Fadin"Mai satan ke da wannan..! Hamida tace"Kai Amina naki yafi yawa..? Amina ta balla mata Harara tana Fadin"To Sarkin korafi..Dayake ke kika je kika Debo naman..! To wannan ma in baki so bani kayana..! Tafada tana mika mata hannu Hanne tayi Saurin cewa"Hamida karbi abunki..Mun ji Amina tunda ke kika Debo Dauki wannan..!. Amina ta murguda baki kafin tace"ko baku yarda bama..In mutum yaji Haushu yaje ya Debo nasa. ! Hamida tasan da ita take yi ammh bata tankata ba suna jin namansu Zafira ke fadin"Wai shanaye nawa aka yanka da kaji..! Duk gidajen nan fa akwai Nama ko"ina ka shiga. !. Amina tace"Waya sani Zafira..?kila sun kai dubu kajin Shanayen kuma kila goma..! Tafada tana Tura naman bakinta Hamida tace"Haba inaga ma sun fi..Kinsan in ana Biki haka ake ta Yankosu ana shigowa dasu..! Zafira tace'Cab...ai gidan Gonar ta kare..! Amina tace"Ke..kina da Hankali kuwa..?Kinsan adadin Dabbobin Dake gidan gonar nan ta baba malam..? Ke babban waje ne fa na taba gani a Wayar Ya jafar da yazo yana nuna ma su Mamanmu na rantse da wanda Raina