← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 193

Sashe 5

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Jafar gaban Amina ya Tsaya yana kallonta kamar yadda itama take kallonsa abun na bashi mamaki ba kowa ke iya Hada ido dashi ba Saboda kwarjininsa da yadda kannensa ke tsoronsa  ko Jadwa Datake Daga shi sai ita bai jin tana kallonso ido Cikin Ido.
Kai Tsaye Cikin Kakkausar Muryansa yace"Da aka tashe ku makaranta ina kika Tsaya..?ko nace ina kikaje..?
Amina kai tsaye tace"Gidan yar ajinmu Zainab isa..!
Da mamaki yace"Yaya ta aikeki ko mamanmu..?ko Aba..?
Itama Cikin dan mamakin ta Waro Idanuwanta kafin tace"Kudina naje amsowa..!
Tafada tana Dan Tura baki Hannu yasa ba tsammani ya bige bakin yana Fadin"Watarana sai na rabaki da Hakoranki na gaba..!
Nasir Dake bayansa yace"An fa Tada sallah Jafar..!
Jin haka yasa ya ja kunnenta Har sai da tayi kara Cikin Fada yace"Kije kiyi sallah ki jirani kafin na wuce zan dawo ban yarda da mganarki ba..!
Sannan ya saketa gefe ta koma tana Sosa kunnenta Nasir ma sai da ya bata Rankwashi mai Zafi sannan suka Fice Sai ga Jawaad ya Fito ya Bisu abaya da Gudu yana ma Amina gwalo,Tana Dafe da kanta Dataji zafin har Tsakar kanta tace"Yaro in na kama ka sai na Lahira yafi  ka jin Dadi..Na fika Jidali da Fitina..!
Tafada kafin ta mike tana Kakkabe Jikinta nan bakin famfon ta karisa ta Bude ta fara alwala sai da ta gama kana ta shige Dakin Mamanmu ta isketa kan Darduma tana Lazimi..!
Kai Tsaye Amina ta wuce uwar Dakinta tana Fadin"Mamanmu na Dauki Hijabinki Cikin Wardrope dinki..nawa suna Dakinmu kuma bana son shiga..!
Tafada Muryanta Cikin yar shagwaba Tana Daga zaunen kan Darduma ta Daga mata kai Ciki ta shige ta Bude makeken Wardrope din ta Bude barayin Gogaggun Hijaban Mamanmu ta Dauko guda Daya ta fito tana zuwa Mamanmu ta matsa gefen Darduman Datayi sallar duk da Shinfidadden Cafet din italiyan din Daya malalen Falon
Tana cikin Sallar mamanmu ta Fice kuma Tana da tabbacin Dakin Yaya zataje domin duk bayan mgariba da isha"i adakin take yinsa suna Hira da Tattauna wasu abubuwa Kamar ba Kishiyoyi ba..
Tana Idar da Sallar ko dan addu"a bata Tsaya yi ba ta mike Zaraf kamar an tsunguleta mganar Ya Jafar take Tunawa Dayace zai dawo duk da tasan da Wahala ya dawo yau sai gobe saboda akwai wa"azin da Baba mallam ke yi kowani bayan Sallar mangriba zuwa Isha"i sannan in an gama zasu Rufe da Sallar Isha"i kuma Tana da Tabbacin Aba ma ya dawo suna masallacin Tare in ma sun fito daga waje zasu gaisa ya wuce gidansa ina ma wannan mayyar matar tasa zata barsa ita Har mamakinta take yadda take mutuwar son Ya Jafar ko ina abun so a wajen wanda ya maida mugunta Dabi"arsa.
Baki ta Tabe bata tsaya Cire Hijabin Jikinta ba ta Fice Takalmin mamanmu na Yawom Tsakar gida ta Zura ya ma mata yawa sosai karamar kafarta ta Zurma aciki batason shiga Dakin su ne Saboda hamida tasan su Ya zeenatu ba lalle su bi ta kanta ba ammu Hamida gani taake tafi kowa Shigar mata Hanci da Dunkunkune in ta koma Dakin Hamida tayi mgana sai ta tankata kuma Hakan kamar wani Lasisi ne ta siyo ma kanta Fada Wajen Aba Shiyasa ta zabi Tafiya gidansu Hanna tayi zamanta sai Dare yayi Lokacin Hamidan ta kwanta sai ta Dawo.
Batare data Fadama kowa ba,kamar yadda ta Saba yin komai gaban kanta ta saka kai ta fice Daga gidan kuma Har ta fice bata Hadu da kowa ba,Awajen ma ba kowa Saboda an shiga masallaci Wajen yayi Haske Saboda an kunna Generator massllaci ba wuta suma ana Dawowa sallah su Ya shamsu zasu tada na cikin gidan Mallam babba ne mai bama Duka gidan da gidansu wuta taji dai ana ta Fada D'an malam Dake madina ya aiko da kudi aka siya har ma gyaran gidajen da aka sabunta musu wattanin baya duk shi yake turo ma dasu Ya Jafar kudi su kuma suna aiwatar da umarninsa.
Tasamu nasaran shiga gidan kanta Tsaye saboda Buba megadi shima yana masallaci wannan Dokar Baba Malam ne,ba hujja kana jin ana Kiran Sallah ka fake da wani aiki ya zama Dole kowa ya bar komai ya tafi kiran Allah
Gidan Baba Malam ya wuce yadda zan kwakwatanta muku Babban gida ne mai Dauke da Haraba mai girma Dauke da Motoci guda biyar hudu suna Bayyane Daya kuma an Lullubeta da Tamfol Tadade ahaka in ba mai mallakin Motan ya Diro garin ba bamai da ikon hawanta Duk da bai Saka Dokar haka ba,Sai Dayar bakar prado din ta mallam ce in fita ta kamasa Dayar 306 iri daya guda Biyu Daya ta Ya Jafar ce Daya ta Nasir,Sai wata benz baka ta Aba ce,Sai babbar Macapolo ta Jigilan makaranta ne.
Haraban gidan na Zagaye da Fulawowi masu kyau da yarari.
Daga Cikin gidan kuma Flat Biyar ne ajere na Farkon na Baba Malam ne grefensa akwai Dakuna kamar guda Biyar saboda mazan gidan Falt din Dake bayansa kuma Shashen Hajiya Babba ce Uwargidan Mallam sai shashen mai bi mata Hajiya uwa Daga nata sai na Anty Nasara na Anty Amarya shine na karshen wanda Daga gefensa kuma wani katon Kitchen ne da Store mai Dauke da Kimai na Bukatar mace na girki Kowacce tana da nata ashashenta ammh Gudun Fitina yasa aka Fitar da na waje inda duk wacce keda girki Zata Fita ita da yara da masu aiki suyi komai Tare Dokar gidan ce da Tsarin komai Bisa Tarbiya da Sunna Baba mallam Sharahararran malami ne Daba iya Nigeria ko Gumel ba Har Kasheshen Larabawa an san dashi.
A Babban Falon Dake shashensa ake Taruwa Matan da yaran maza da mata aci abinci sannan Ashashen sa ne kadai akwai Talabijin shima kuma In suna wajen sai Tashar Karatu sai wa"azi in ba kaga an Sauya sai in Dare ya Tsala yana so ya kalli Labarai Sun saba ya Zame musu jiki Duk wanda ya kwana da tashi agidan Mallam ina ka Fito karatu ina zaka ne..Me kace Aya ce mai na maida maka Hadisine ba iya Iyalan gidan ba Har damu da muka Hade dasu muma Dokarsa muke bi Domin har yau har Gobe in ba"a Fada maka ba Mutanen gari Dauka Suke mu jikokin Mallam ne BABA SA"IDU ne babban yaron Malam..!
Kai tsaye shashen Hajiya Babba ta wuce Domin nan ne Dakin su Hanne Auta take ga Hajiya,Bata Tsaya sallama ba ta Tura kofar shashen da Karfi Tana Kiran sunan Hannan.
"Hanne...Hanne..Hanne..!
Take Fada lokaci Daya tana Wulka manya Idanuwanta Cikin kayattacen Falon na Hajiya Dayaji komai na More Rayuwa.
Sai dai mamaikon taga Hanne sai taci karo da Hararan Ya Aisha Dake Zaune kan Darduma tana karatun pass Q domin suna gabda fara WAEC da NECO, Bata katse Karatun nata ba ammh Amina tasan Hararan ko ta macece Yasa ta Daga Hannunta tana Fadin"Yi Hakutri Ya Aisha..sallamu Alaikum..!
Tafada kai Tsaye tana kara Wurga ido wajen neman Hanne.
Abida Dake zaune kan kujera Tana Karatun Qur'ani
Wacce Tunda taji Bangazan kofa Da kira tasan sai Amina itace kadai bata da natsuwa Kaf acikin ya"yan gidansu da gidan Baba Sa"idun.
Itama Hararan ta jefa mata kafin tace"A tsakiyar falon ake sallama Amina..?
Sai alokacin Amina ta ganta aranta ta Furta"Uwar sa'ido..!
Afili kuma sai ta Dan Rasauya ido kafin tace"Sallama fa sunanta sallama Ya Abida..!
Abida daman ai tasan bazata koma ba Kafiya ce da ita kamar kafura.
Bude mata ido tayi tana Fadin"Au bazaki koma bakin kofa ki sake wata ba kenan..?
Amina ta Bude baki tace"Ah gaskiya..!
Cikin kunkuni tace"Haka kurum..Tab...
Abida tace"Me kikace..?
Kallonta tayi da manya Idanuwanta kafin tace"Nifa ban ce komai ba..!
Abida Kai ta Rausaya a cikin Idanuwan Amina akwai wani kaifin da indan ta kalleka sai kaji gwiwanka yayi sanyi..!
Da hannu ta nuna mata tana Fadin"Hanne tana Dakinmu tana Guga..!
Ai bata gama Rufe baki ba Amina ta Kwashi gudu tana kara kiran sunan Hanne Wacce sai Lokacin taji kiran da Sauri ta kashe Iron din Daman Hijabin haddarsu na gobe take gogewa ko mafarki take yi tasan Sautin Kiran Amina Dabam yake kuma akowa da Hannatu yake Kiranta Aminene ce kadai ke kiranta da Hanne.
Akofar Dakin sukaci karo Dakin Dake kusa da Bedroom din Hajiya sai wani Wanda suke Saukar baki Dangin Hajiya in sun zo nesa dana Hajiya.
Kusan karo sukayi da juna Wanda yasa Hanne tayi baya tana Fadin"AMINA gani nan fa..!
Tsayawa sukayi suna kallon Juna kafin Amina Taja hannunta su koma Cikin Dakin Tana Fadin"Hajiya fa..!?
Hanne tace"Tana Dakinta..!
Amina tabi Dakin da kallo ta Sauke ganinta kan Hijabin da Hanne ke gogewa tace"Dadina Dake kina da Zafin Nama Hanne..ni fa ban ji ma Hijabin nawa awanke yake ballatana akai ga gugansa..!
Hanne Dukawa tayi ta kunna Soket ta Cigaba da Guganta ita kuma Amina kan Karamin gadon Hanne ta Zauna Babban na Ya Abida da ya Aisha ne
Hanne bata damu ba tace"ai ke babba ce..Amina kike ni kuma Hannatu..!
Amina Tayi dariya tana Fadin"dillar Sarkin Tsoro..Ki Saki jiki ki amsa sunanki Hannatu Yusus Abdurraham Bazanga kowa shakkarki zai yi..!
Hanne na Guganta bata Dago ba tace"Uhmm..Meya fito dake Daga gida da Daran nan..?nasan da Dalili..!
Amina ta Tabe baki tana Kwabe Hijabin Jikinta Lokaci Daya tana Fadin'"Ke da kika sani..Yau fa Har Yaya sai da ta Dakeni Hanne su Ya Zeenatu suka min gami wajen su ya Jafar harda fadamin in ya Dawo sai na Sani..!
Hanne na Duken ta Dago kanta tana kallon Amina Kafin tace"Kan Tafiyarki yawon da kika saba in an tashi makaranta ko..?nima fa ana tashi nazo ajinku bakya nan..!
Gajiya akayi da jiranki Ya shamsu yace mu taho gida..!
Amina ta Zabga mata Harara tana Fadin"Ni daman bance ku jirani ba..Nasan Hanya..!
Hanne tace'Koma miye dai baki kyauta ba..Amina don Allah ki daina Wasu abubuwan kai tsaye ko ni in kika fadama zakije wani wajen.ko Hamida haka zata faru..?
Amina ta Juya idanuwanta kafin tace"Hanne..Hanne..Ki kyaleni don Allah kada ki batamin rai bazaki iya da Jidali na ba..!
Hanne bata Kara mgana ba itama Aminan haka Sai da ta juya taja Littafin Data gani kan gadon Hanne Ta Fara Budewa kafin ta Dago Tana Fadin"Hanne akwai Kwazo..Kin yi aikin Malamin Lissafin nan..!
Hanne na Nimken karshe a Hijabinta tace"Ba Dole ba kada ma na manta kinsan mugu ne wlh ya Rantse Bulala goma ga duk wanda bai yi ba..!
Amina ta tabe baki kafin tace"Kan bala"i..Wai haka yace..?
Hanne ta kashe Soket din ta Mike Dauke da Hijabin tana Fadin"Ajinmu ba..Bansani ba ko ku bai Fada muku ba..Ammh nasan komai tare yake mana ba bambamci..!
Amina tace"Oho ni fa sanda ya shigo ina chan ina Karatun littafin da Ziyada ta daukomim adakin Antyta Garin Kallon Ruwa kin ji Dadinsa Hanne..!
Hanne ta tsaya kyam tana kallon Amina kafin tace"Amina Daman baki Daina wannan karance karancen nan ba..?kinsan fa in aka sani bazaki ji Dadi ba..!
Amina tayi tsaki tana Fadin"To sai me..?ke zaki fada..?ke ni kyaleni Sai fa nayi kema zan koya miki Allah da dadi..!
Hanne tace"Allah ya Tsareni..!
Amina ta tsuntsire da Dariya tana ganin Hanne ta Bude babban Wadrope din Dake Dakin gefen inda kayanta yake ta sakashi Kana ta Rufo Tana kallon Amina kafin tace"ki Tafi da littafin gida ki kwafe kada muje Ranar Monday Uncle Gaddafi ya Dakeki kinsan Halinsa..!
Amina tace"Dillah Rabu dashi..Duka na Kisa ne..?da yana Kisa da babu Burbushin Amina aduniya kuma ya Dade bai yi Dukan ba Alqur"an bazan yi ba..!
Hanne ta kada kafin tace"Ammh in kika kiyye taba Lafiyarki fa Amina..?
Amina tayi kamar bataji ta ba ganin Haka yasa Hanne ta karisa gabanta Tana Fadin"In ya jafar ya dawo fa..?
Amina na Dariya tace"Ke bazai dawo ba kema kinsani..Yaushe mai wannan Dakalin bakin zata barsa..!
Hanne na Rufe baki tana Fadin"Ke Amina Anty Shamsiyan ne mai Dakalin baki..?
Amina na Dariya Harda Buga Kafa tace"Eh mana baki taba Lura ba..Sai ma in tana mgana..Sweetheart..!
Amina ta fada tana kwaikwayonta Dayasa sai da Hanne ta Duka saboda Dariya Kafin ta Dago ji kake Tas sun Kashe da juna Cikin Nishadi Tare suke Zube kan gadon Amina nama Hanne Rada akunne dayasa ta kara Saka Dariya tana Tureta Lokaci Daya Tana Fadin"Ba ruwana..Ba ruwana Amina..Bazan iya Da jidalinki ba kinsani..!
Amina bata Damu ba Chanza Fuska tayi tana Fadin"Kin Tuna sadda Muna aji uku a islamiya kullum Karatunta Dayane..Anjadada.Kalli Leben nata jadaddaad..!
Dariya sai da tasaka Hanne Hawaye Saboda yadda Amina ke yi da baki kamar Tsohuwa zatace isuhu..!
Cikinta ta Dafe tana Fadin"Ki barni haka Amina kada ki kullarmin da ciki da Dariya..!
Dariyan suke gabadayansu Basu san da shigowar Hajiya ba sai dai sukaji mganarta Daga sama.
Chapter 5 · 0% Book details