Sashe 132
Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ita kuma Haj.Uwani Anty Amarya na fita ta yi shewa ta kara Sakin shewa kafin tace"Mu zuba mu gani marliya..Karki fara ja da Uwani Domin ni walkiya ce ban Fito ba sai da na shirya..!
Haka take ta fada tana Dariya tasan Daman zatayi mamakin yadda tasan komai nasu Mama hatsabibiyar Bokanyance Dake Niger ita take Sanar da ita duka aikin marliya ita da Balaraba ita kanta da Farko ta Razana da jin sunan mamanmu domin bata taba Zaton matar mugun halinta yakai haka ba, sai dai batayi mamaki ba Sanin yadda Idon kowa yake Rufewa kan neman Duniya..sannan Ta kara jinjina ma wannan kalmar na rai ba abakin komai yake ba wajen Biyan Bukata Tunda Balaraba ta saka aka kashe yaya Matar data Zauna da ita Tsakani ga Allah ta bar mata gidanta da ya"yanta kawai saboda Cikar Burinta na mallakan sa"idu..!
Tana wannan Tunanin kamar Daga Sama taji muryan Hajiya tana Sallama sai ta Rude ta mike da Sauri ta fito Tana kokarin Daidaita yanayinta Hajiya dake tsaye Tsakiyar Falon Uwani ko Zama ta kasa ta kalli Uwanin Yadda ta fito tana abu kamar wani abu dai ya faru yasa da Sauri tace"Wai ni Uwani me ya faru ne acikin gidan nan bansani ba..?
Naga Amarya ta fita Daga shashen ki da Gudu tana kuka ina ta mgana bata jini ba kema mayi sallama kin Fito kamar kina ma a firgice ne Hankalina ya tashi muke Faruwa..?
Haj Uwani na jin haka kawai sai ta Zube saman Cafet din Falonta ta Fashe da kuka yi take yi ba Saurarawa ta kara Tadama Hajiya da Hankali Cikin Rudewa tace"Ko Cikin yaran mu ne wata ta rasu kuke Boyemin..?
Hajiya Uwani na jan majina da Hanci tace"Ai gwara ma Mutuwa da wannan Zargin da Amarya ke jifana dashi Hajiya..!
Hajiya tace"Wani Zargi kuma Uwani..?
Haj.Uwani na kara saka kuka tace"Hajiya wai ni Amarya tazo ta sama tamin zagin kare Dangi da Zargina wai ni nake asiri ina Zubar ma Sakina da cikinta..Fitar nan da kika ga tayi ni tazo ta kare ma Tanadi Hajiya..!
Hajiya ta Zaro ido kafin ta saka Salati ganin haka yasa Haj.Uwani ta karkace baki ta Cigaba da fadin"wai malaminta ya mata Duba yace ci kin matan mallam ne..kawai hajiya sai tace ni ce..Nan tazo ina ta mata Rantsuwa taki yarda dani ina Fadamata kada tayi saurin yarda da irin mallaman nan na karya masu Hada Fada bata Saurareni ba Hajiya haka ta fita tana kukan da Ikirarin sai ta ga Baya na..!
Hajiya nan da kika gani daman wajenki Zani Na fada miki abunda ke Faruwa naji Ciwon wannan abun sannan na Fadamiki bazan kyale Amarya ba sai ta san tayi min kazafi..!
Ta karishe Fada tana kuka Wurjajan..hajiya kuwa sai Faman Salati take yi kafin tace"Kinga Uwani bar kuka..wannan mganar ba tawa bace..Bari naje na kira mallam na Sanar dashi abunda ke faruwa wannan mganar tayi muni da yawa Uwani..!
Haj.Uwani na jan majina tace"Ko kin gayamai Hajiya ni bazan yafe ba..Sai an Bimin Hakkina akan kazafin da Amarya tamin..!
Hajiya bata Saurareta ba ta Fice tana Jimamin wannnan abun aranta tana Jin Haushin Anty Amarya bata taba Zarginta da shiga malamai ba ammh jin abunda ta aikata sai taji duk ta Zube mata ina amfanin wannan aikin..?ta Biyema mallaman karya suna neman hada fada acikin gida.
Hajiya na fita Haj Uwani ta mike ta Share Hawayenta ta yi Dariya kafin tace"Marliya tun a yau zaki san kin Hada Hanya da Uwani Diyar Hamza Tsafe..!
Ta fada tana Dariya har ta Hango yadda Marliya zata gane bata da wayau a falon mallam Dakin da Umaima take ta leka barci take yi Domin yanzu ko Makarantar Haddar ta Daina zuwa saboda Ciwon nata ya tashi gadangadan ana ta dai fama da mgunguna ne.
Hajiya ko na fita Bedroom dinta ta shige nan ta bar Hanne da Hamida afalo suna rike da Littafansu bata ma Bi ta kansu ba ta Shige Daki wayarta ta Dauko ta Kira mallam bai yi nisa ba yana gidan mai anguwa ya Kirasa kan Cases din Filin wasu marayu da aka kawo mai mganar to daman mai anguwa in wani abu irin haka ya Faru na bangaran addini yana kiran mallam Domin su Tattauna.
Yana jin Hajiya tace yazo gida ba Lafiya yace mata suna ma kan Hanya.
Lokacin ana gabda kiran Sallar La"asar ne yasa suna Dawowa yace bari ya Tsaya yayi sallah kafin ya shiga Cikin gidan
Hajiya ta fito ranta a jagule sai yanzu ma ta lura bata ga Amina ba Tunda dazu da suka Dawo daga makaranta,yasa ta kalli Hanne da Hamida dake ta yin aikin da malamin Lissafinsu ya basu a makaranta tace"Ina Mamah yau. ?
Hanne tace"Tana gidan baba Sa"idu dazu da muka shiga gaida mamanmu ta kwanta sai ta fara barci mu kuma da Zamu tahilo bamu tashe ta ba..!
Hajiya bata ce komai ba ta kada kai kafin tace"ku tashi kuyi sallah Lokaci yayi..!
Daga haka ta koma Cikin Bedroom dinta Ammh aranta sai da tayi Tunanin barcin Amina yayi yawa kamar kasa yanzu ko da asuba fa Dakyar ake tashinta wani Lokacin da Daddare kafin takwas Amina ta kwanta sannan in suka Dawo makaranta sai tayi barci ammh sai bata kawo wani Tunani ba tafi Barinsa a Saboda Basa Zama a zirga Zirgan makaranta da Sauransu.
Hajiya ta idar da Sallah kenan Kiran mallam ya shigo mata yace gashi ya shigo Gidan Hajiya batayi kasa agwiwa ba ta saka lullubinta ta Biya Shashem Hajiya Uwani Dake zaman jiran Kiran mallam suka tafi Falon mallam suna zuwa Hajiya tace ta fara gayama Mallam yadda taga Anty Amarya sannan tace Uwani ta maimata abunda ta Fadaamata Haj.Uwani ta gyara Zama ta Fara Rattafama mallam yadda ta Fadama Hajiya ta karishe cikin kuka tana Fadin"Mallam abu dayane in na Tuna yake min ciwo..Da Amarya ta Zargeni da laifin kisa Mallam..?
Ashe haka ta Tsaneni bansani ba..Ta rasa kazafin da Zatamin sai kazafin kashe gudun jini Tun kafin ya Fito Duniya..? Wannan in gaban yan Sanda za"a kai ai babban cases ne mallam..!
Mallam da ransa ya gama baci ko mgana bai yi ba ya Daga wayarsa ya kira Anty Amarya wacce ke cikin Bedroom dinta tunda ta Dawo Daga Shashen Uwani ta shige ta rufe kanta tana kuka kukan rashin mafita da madafa kukan takaici da gazawa a karo na farko ko sallah bata tashi tayi ba sai ga Kiran Mallam sai da gabanta ya Fadi balle Dayace tazo ta same sa afalonsa a kausashe.
Ai bata gama Sarewa ba sai da Sawo Hijabinta Fuskarta duk ta kode ta iso Falon mallam ganin Hajiya da Haj Uwani sai da yasa gabanta ya Fadi Jikinta ya fara rawa ta Tsaya Cak ta kasa gaba ballatana baya.
Mallam cikin kaushinsa yace ta kariso ita ake jira,Jiki a sanyaye ta kariso ta Zauna gefen kafar Hajiya a kasa tana kallon Uwani dake mata Dariya a kasa kasa Daganan tasan wani makircin ta kulla mata..
Kanta ya Daure sanda Mallam yake karanta mata abunda Uwani tace ya Kalletaa Cikin bacin rai yana Fadin"Marliya ashe ban Dade ina muku nasihan yarda da malaman tsubbu ba..?
Shine kika kai kanki bayan kin yarda dashi shine ya karanto miki karya kika zo kika Hadamin Fada acikin Ahalina alhalin na Dade ina gargadinku..?
Anty Amarya ta Tsure hankalinta ya tashi ta kalli Haj.Uwani dake matsan kwallar karya ta maida kallonta kan mallam taga yana mata wani kallo Sai kuka ya taso mata ta Fashe da kuka Tana fadin"Wlh ma..!
"Karki ce tak a nan wajen marliya..Baki da abunda zaki fadamin bana Kiraki Domin kimin karin bayani bane..na kiraki ne naja miki kunne Wlh Tallahi in na karajin mgana makammancin wannan sai na Saba miki in ma ban yanke Igiyan auran dake tsakanina Dake ba. domin ina kyamatar Zama Dake Marliya tunda kin zama Mushuruka mai bin malamai da yan Tsubbu makiya Allah..!