← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 193

Sashe 2

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata gama Rufe baki ba Yaya Zeenatu ta Dauka da Fadin"Kema kinsan bazata taba fada ba wannan mai Taurin kan tsiya..Duka ne kadai yaran data sani kuma yau sai kin Daku..Domin ba Dadewa Ya Jafar yazo ya Tambaye ki muka Fadamai gaskiya shida Ya Nasir suka shigo kuma yadda suka Fita yau in s suka kama Dukanki sai na Lahira yafi ki jin Dadin Sakarya mara Tunani..! Ta karishe Fada tana Hararanta kafin ta saki tsaki ta Cigaba da Duba Littafin Turancin dake gabanta Fuskarta Kaf irin na Hamida ne sai dai Amina tafi su haske ammh har Zulaihat din suna kama ta jini ita Amina manyan Ido ta Fisu da rashin jiki. Har Duhu Amina take gani Saboda yunwa da gajiya ga bacin rai bataso ta shiga Cikin Dakin suna Cigaba da yaba mata mgana tasan sai ta tankasu kuma basu da imani Taruwa zasu yi suce zasu Daketa tasan bmai Centonta sai Mamanmu in ta Yaya ne su kasheta ita kuma bata iya Shuru da bakinta wanda ya fadamata goma sai ta Fadamai ashirin. Shawaran canza Daki tayi da Niyar Shigewa Dakin Mamanmu ta Saki Labulan Dakinsu tana Fadin"Duka ai baya kisa..Dayana kisa da ko Burbushin Amina ba"a samu ba..Kuma ni ba Sakarya bace Ehe..! Tafada tana kunkuni Zulaihat Dake Dakin tace"Eh me kike cewa ne..? Zeenatu Wlh Zaginki tayi..! Tafada Cikin takaichin yadda Amina take so ta zame musu ciwon kai acikin gidan ko Aba bata ce Amina na jin tsoronsa ba. Zenatu tayi Falati da Zanen datakeyi wanda Bilogy teacher dinsu ya basu Doguwar rigace ajikinta ta Fice tana Fadin"ki barta bakinta zan fasa wlh..Zatasan wa take ma rashin kunya..! Tana daga kwancen tace"Uhm..Ki Dirji bakin gudun Reni ammh nasan ko kin gama bakin Amina bazai taba mutuwa ba..! Tafada Lokaci daya tana girgiza kai aranta take fadin Allah ya shirya Amina Zeenatu ta fito Daga Dakin Daidai Lokacin da Hamida take fadin"Mgana fa nakeyi Amina..?gwara ki fara fadamin Inda kika Tsaya na samu yadda zan kare ki agaban Ya jafafar yau.! Azafafe Amina ta Dago Daga Nufar Dakin Mamanmu datayi niyya Jakarta ta Sauke Saboda Jidalin Dake kanta bazata iyasa da wannan nauyin ba,Manyan idanuwanta ta Sauke kan Hamida tana Fadin"Hamida...Hamida..Hamida Sau nawa na kiraki..? Hamida na yar dariya tace"Kamar sau uku..! Amina ta tareta da"ba kama bace..Sau uku na kiraki saboda ki gane girman Warning din da zan miki..Hamida ki Fita Daga Rayuwata Wlh..Ina ruwanki da inda naje inace ke bagaki kin Dawo gidan ba..!da kike fadin ki kareni gaban ya Jafar na sakaki ne..?ke kika saka kanki kina kokarin kare abunda bazai taba karuwa ba Hamida Ni Amina wake sona..?Aba kullum Amina mai Laifin ce awajensa Hakama Yaya kowa baya fadamin abun Alheri akaina Daga Mamanmu sai Baba Mallan ke sona..Sai Hajiya Baba da Hanneta bandasu fadamin me yabon Amina..?kinga kuwa ko Icce aka sakama baki haka Lalacewa yake yi ballatana Mutum kamar ni to bari kiji na Fadamiki ni AMINA SA"IDU GUSAU kainuwa ce dashen Allah baki ko Duka baisa yaga karshena ba, ballatana ganin baya na saboda haka ki adana kalaman bakin ki kuma Rufemin Dattin bakin ki in kuma ba Haka ba ki jirani na ci na koshi in Jidali kike nema na Rantse da wanda Raina ke hannunsa kin Tare ni kin sam.u..! Tafada Lokaci Daya tana Girgiza kugunta kamar wacce take Shirin Dambe,Zeenatu Data fito tsayawa tayi tana kallonta Hamida kuwa cigaba da wankinta tayi tana Fadin"Allah baki Hakuri..Kya yi bayani in kika shiga Hannun Ya Jafar..! Wani Tsaki taja kafin ta Duka tana Daukan Jakar makarantar tana Fadin"In yazo kada ya bar Amina da Rai..Yau aka saba ko yau za"a kareta Hamida..?da duka na kisa da yanzu Amina ta Dade a kushe..! Dauummmm...! Taji Saukar Dunkullen Dumdu abayanta kafin ta karisa mganarta Dumdum dayasa sai da ta Duke kasa kan Jakarta tana bankare baya saboda taji Saukan Dumdum a bazata. Zeenatu tace"Yauwa Yaya..Don Allah Daketa bari na karyo Iccen Bishiyar Nan ki Daketa da ita tunda tace Duka baya mata komai..! Tafada tana Nufar Bishiyan Dake Haraban wajen ai ko ba"a Fada ba,Tasan Hannu Dayake ke da wannan Dumdum ba tun yau ba Tun tasowarta bata iya Haddace dukan kowa ba, da an Dageta taji zafi ya Huce shikenan ta manta ammh Duka Daya Duka Daya daga Hannu Dayane bazata taba manta yanayin ba bata Cika Duka ba mai Hakuri ce sai dai In ta saka hannu ta Duma maka Dukanta Har Ka kwana bazaka manta dashi ba Hannu Dayane mai kama da goma YAYA CE..ita kadai ce Amina bata saba da Dukanta ba kuma Dukanta ne kadai ke saka Fitar Hawaye a Duka Idanuwanta Aba bai duka sai dai Fada Ko su Ya jafar sai dai su gaji su kyaleta zatayi ihu ammh in ka Duba ba Fitar Hawaye ko Daya Amina akwai Taurin rai da kafiya kamar kafuran Farko..! Dagowa tayi Idanuwanta na Cikowa da Hawaye ta Sauke kan Fuskar Yaya kamar an Tsaga kara yadda kukasan yan Biyu sai dai bambamcin Amina yarinya ce Yaya kuma Shekarun sunja akallah 49 aduniya ammh Hatta Shape din Fuskarsu iri Daya ne tafi Amina Haske sosai ita din Fara ce ammh ba Tar ba. Cikim bacin rai take kallon Amina rai Daya..Rai kwara Daya da Tunda ta Haifeta bata Huta ba Amina..Amina ta Addabi kowa acikin gida da waje ba inda ta bari ita kadai take so ta jazamusi hawan jini da Ciwon zuciya ita kadai TA FITA ZAKKA..cikin Ya"ya goma sha Biyu Dake gidan kowa ya gama lafiya banda Amina kowa Amina tagaji takai makura ga kauda kanta kan Lamarin Amina. Tana Kitchen Sanda Amina ta shigo Taje Duba Wani mganin Ciwon Ciki ne Ararrabi Data ijiye Cikinta ke Juyamata take so tasha..Tun Sanda yaran suka Dawo suna Fadin basu ga Amina ba takasa mgana to me zatace...?wannan ai ba karon Farko bane da Amina tataba batan Dabo a makaramta ba,akwai Lokacin da har an baza Cigiya agidan Radio sai gata ta Dawo wai taje Birthday din yar a Jinsu kaninta ake ma Birthday Bakimciki yasa Aba dinsu ya kamata yayi mata Duka ammh baisa ta Daina ba Amina kanta Tsaye take aikata Duk Abunda taga Dama,a kananun SheKarunta Duka ya Zame mata sabo eh mana Gaskiya ta fada Da Duka na Kisa da an kasheta ita kam Tin tana Daukan Amina aljanu gareta har ta yarda ma kanta Lafiyanta Kalau Amina Zakka take so ta zame musu Cikin gidan nan da Zuru"a gabadaya. Koda ta Haifesu kaf ya"yanta Ba ita take Renansu ba BALARABA ce Mammansu banda Jafar duka ya"yanta ita take Renonsu ta yayesu in ba Fadamaka akayi ba bazaka Taba Cewa Yaya ta Haihu ba Duka yaran Gidan komai nasu Mamanmu Mamanmu Kowa mamammu In kaji Yaya sai in Mamanmu ta sakota Cikin Shirginsu komai na Tarbiyan yaran da komai na Rayuwarsu na Hannunta ne sai In ma ta musu wani abun take sani Daga baya ba ita kadai kaf Dangin Sa"idu suna girmama Balaraba Kuma sun saka mata suna ita mai karamci ce Taci wannan sunan Domin ita Maman kowa ce. Bazata kyale Amina ta zautataba kullum Kokenta kan kare ma Amina ne,Mganar Rauninta kan Amina ne Koda yaushe Cikin nema mata Taimako take gani take Aminar ba ita kadai bace kullum kalamanta kenan "Yaya ku daina Ganin Laifin Amina..Adaina Dukar min Ya'a yaya ba Laifinta bane.. ku lura kamar Amina ba ita kadai bane ni dai ina Zargin Aljanu suka taba Amina Tun tana ciki..Yaya bazan taba barci ba sai naga Amina ta dawo kamar kowacce y'a acikin gidan da watarana Zaku yi alfahari da ita..! Lokacin datake Fadar haka kukane acikin Ranta da Zuciyarta tasha kuka Har da majina kan Amina in ana Dukanta haka zata zo ta tare har ana Samunta tana Fadin"Jafar ka bari..Kada ka sake taba ta nace..! "Mamanmu ki barni..Ki bari na Illata wannan rayuwar kafin ta kashe mana Uba da Bakaken Hallayarta..! Rike Amina take ajikinta ta Fashe da kuka tana Fadin"To in bazaka bari ba sai dai ka Hadamu duka ka Dakemu..Ammh bazan bari ku illatamin yata ba..! Ita ta Haifi Amina ammh wannan Raunin Maman Amina ke Daukansa bata Cika maida kai kan lamarin Amimar ba Tunda bata wata shakuwa Tsakaninsu,ammh yau taji tana so ta Nuna ma Amima ta bar wasu Zukata su Huta ta Duba Raunin Mamarta akanta ko Saboda ita ta sauya wannan Bakin Halin nata. Kallon Datake mata Da kuma Tuna wasu abubuwan yasa Hawaye suka Cika kwarmim idonta. Amina na Dafe da baya ta Bude tace"Yaya..ki ts Bata kai ayaba Yaya ta kaimata mari wannan karon ya Sameta da Karfi Har sai da ya fito da Zulaihat Daga Daki da Gudu Hamida ma ta bar wankin da Sauri ta karisa tana Fadin"Yaya kiyi hakuri..! Har Zeenatu Dataje Karyo Icce sai gata ta dawo Wlh bada gaske take ba Bata Dauka Yaya zatayi Duka ba,Duk da Rashin jin Amina yarinyace mai Shiga rai sannan Kaunar junansu ajininsu yake koyaya wni abu ya samu Daya Dukkansu sai sun ji wani iri. Amina na musu rashin kunya kunkuni da Sauransu suna zugawa in za"a Daketa ammh akazo ana Dukanta sun Rika bada Hakuri kenan Hamida mai Saurin kuka Harda kuka take sai an gama Dukan tazo tana Daga Aminan sai ta Kalleta tayi Dariyan dauriya da yaki da Abunda take ji tace"Wai Kuka kike Hamida..?kuka fa..Kima Daina kuka Amina ce Aminene ce badai mutum ba sai ta Allah..! Hamida na sharan kwallah takan Dungure mata kai tana Fadin"To kidaina wasu abubuwan don Allah Amina..Ba domin kowa ba domin Aba da kuma yadda muka zama Zuru"ar gidan bazanga..! Amina alokacin sai dai ta kalleta tana Fadin"A"ah fa..Ni bansan laifin da ake yawan Fadin Amina nayi ba. abunda dai nasani shine Amina..AMINA SA"IDU Haka Allah yayita..Ko ta Sauya shi Hali ai zanen Dutse komai zai Sauya da Mutum banda Halinsa..! Yaya ce ta katse ma Hamida Tunaninta Cikin Fitan Bacin rai da wani bakinciki Yaya ta Rufe Amina da Duka kota ko"ina tana Fadin AMINA Yanzu abunda kika Zabama rayuwarki kenan..?So kike kamar yadda kika saka ma ABA dinku Hawan jini nima ki sakamin ko..?Gidan Uban wa kika je bayan an tashi makaranta..?Duka Sauran yan"uwanki sun gaji da nemanki sun dawo..Saboda ke kin FITA ZAKKA agidan nan sai abunda kika dama kike yi
Chapter 2 · 0% Book details