Sashe 33
Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta zauna ta jirasu aka Jera musu Salatif aka sanya musu Lalle Hamida tana ta lallaban Amina Tayi kunshu tace bazatayi ba da ta gaji ta Daga mata Murya tana Fadin"Don Allah ki kyaleni Hamida. haba kin cika kwazzaba..Nace miki bazan yi ba ko Dole ne..! Wasila tace"Ke so ake a Rufa miki asiri ki Rufe farar kafar nan taki kamar ta maza..! Amina ta Daga idonta sama Tana Fadin"Ni kafata bata maza bace..Kuma ai Farar kafar ta Allah ce ba wanda yace saka Lalle Dole ce..! Wasila tace"Duk wanda ya aure Amima ya auri kazanta da rashin kunya..! Amina tayi mata banza aranta tana Fadin"Tunda mijin ya aurrki nima zan auri..! Lokaci daya tana kallon Wasila tana yar Dariya Domin Wasila baka ce Dulum sannan ga muni ba Laifi Basu je ko"ina ba Saboda kunshin su Hamida sai Gabda La"asar suka Wanke kunshi suna ta Sauri Domin Tuni wajen Walima ya cika tun dazu su ya Abida suna chan suna ta Gyare gyare Tuni masu Kanofi sun isa da kujeru sun kafa komai mata ma sun Fara Tafiya da wasu kayan Rabo da kuma abinci. Domin karfe Shida na yammah Za"a tashi Daga Walimar,Lokacin da suke Shiryawa ne Anty Hidiya ta shigo gidam Cikin gayunta Sanye da Wata Farin Leshi ta Nannade Jikinta da Lifaya ta saka Takalmi mai Tsini Da ya"yanta Yunus da Zainab suna Kiranta Zeeta. Yaran basa jin Hausa sai Turanci Amima ta kyabe baki tace"munga Magofork karewar Turanci don Uban mutum..! Tazo gaida Yaya ne Amina na mamakin kaf ya"yan Baba Mallam sun fi Ji da yaya kan Mamanmi komai suka samu sai kin ji Yaya Amina abun na bata Haushi Afili ta kan ce"Ai Mamanmu tafi ma yaya som mutane..! Sun gama Shiryawa Cikin kayansu sun saka Hijabasu Takalman sallansu suka sanya,Duk yadda suka so su Zille Basu samu Dama ba sai da su Ya Jaleela suka tasa su suka Dora musu manyan Kololin waina almajirai kuma suka Dauki Buhunhunnan Take awaya sauran kayan kuma Ya Nazem da yazo dasu yayi ta Jigilan Daukansu zuwa Chan haraban makarantar Data Fara cika da Mutane kaf Daliban Isalamiya da Hadda Tare da malamai da kuma Duka bangarorin gidajen biyu sun Hallata. Su Jadwa suka je suka zo da Amare da Amotar ya Nazeem,sun sha Fararan Hijabai Har kasa da Abaya bakake kamar Larabawa Hatta Kafarsu bakin Takalmi ne sun sha kunshi ja da baki Suna kyalin gyaran Maiduguri. Daga chan gidan wajen Walima aka Zarto da su ko gida basu je ba. Kowani Daki sun yi nasu ankon Banda anare da Baba Mallan yayi musu komai iri Daya su Ya Abida da nasu ankon tare dasu Amina data gansu dashi baki ta rike tana Fadin"Hajiya bata kyautamin ba..Sai fa nace kada tayi ma yaran nan irin namu..! Suna ta kunshe mata Dariya tana Hararansu. Hajiya uwa ma da Danginta irim nasu Amina sukayi da Fararan Hijabai sai Dakin Haj.Nasara ma ita da ya"yanta da Tawagarta sai Dakin Anty Amarya itama da nata ita da ya"yanta da Danginta Less sukayi Sa"adati sai ubaj iyayi take Amina ta tabe baki tana Hura hanci da karfi tace"Ba"adai Fimu ba Ehe..! Sa"adatu tasan da ita take ta kalleta suka Harari juna kafin kowacce ta kauda kanta. Duka gidajen ba wanda bai zo ba sai wadanda aka bari su Zauna agida Dokar Baba Mallam ne har Hajiya Babba ya bada Izinin taje Wajen Walimar Ya Nazir ya kawo su Duka iyayen nasu Anty Hidaya kuma da su Anty Shamsiya Amotar ya Nasir suka Taho. Ya Jafar kuma ya Dauko su Mamanmu Sauran mutane kuma da kafa suka taho Tunda ba Nisa Anty Sakina da Anty Sarood kuma ya Uzairu Ya kawo su a Motar ya Danmalam,shi yana chan gida yana Hutawa baya son Hayaniya. Wajen ya cika da Mutane,Walimar ta mata ne za"ayi wa"azin aure bayan an bama Amare kyautuka,Suma din sai sunyi karatu. Shugaba ya fara Jawabi mallam Datti ya yi bayanin Yadda su ya Zulahait suka zama Zakwakurai a cikin makarantar ya fada cewq suna da Haddar Qur"ani da kuma Sauran Littafai a kansu makaranta suna alfahari dasu matuka. Daganan aka fara gayyatosu Daya bayan Daya suma karati suna kuka ana Kabbara bayan nan aka basu Kyatttuka,kowacce adarasin data fi kwarewa ya Zulahat taci kyautan Iya Tajhud da kuma Muryan karatu sannan ta ci kyauta kan Haddace Buhari da Muslim. Su Ya Sadiya ma haka gabadaya gidanmi kowa mai kokari ne bamu da Malalaci ta bangaram karatu. Daganan sai aka fara Rabon Waina da su Donut abunda aka sanya a Takeway. Amina suna Daga chan baya ba wanda ya Nemesu su ya Abida ne da yan ajinsu ke ta raban har da su Mariya yan ajinsu Amina da Sa"adatu abun Rabon na abinci Gabadaya akayi ba bambamci Amina ta tabe baki Tana Fadin"Mu fa na lura a bikin nan kamar bamu da wani gata..Ji fa wai Rabon takeway din ma ba wanda ya Neme mu..! Hanne ma taji zafi tace"Uhm..Wai har da su Mariya..! Amina tace"ji sa"adatu dame tafimu..?Ai ba kowa bane yayi mana bakinciki sai ya Abida..! Yanzu bamu da bakin mgana in an koma Hadda kowa yaga yadda aka yarsar damu kamar wasu bare..! Zafira tace"Mu tashi muje muma ayi Damu mana..! Amina tace"Sai kin dawo ban tashi Wulakanta ba..! Wlh ya Abida sai ta tsinka ki a gaban Dubban Mutanen nan kawai mi Tsaya muga ikon Allah..! Suna nan zaune suna kallon kowa Amina ta karkata kunnen Hanne tana Fadin"kalli Yan"uwan Anty Amarya..Sun fi kowa zagewa. wai suma chan gidansu ba"ana Bikin ba..?sun wani zosun cikamana gida..! Hanne tace"Sai an sun tafi Amarya zasu je chan suyi Bikin su..! Amina tace"Gulma dai..Gani suke sun fi kowa ji yadda Sa"asatu take..! Hanne tace"Kalli ma yadda take shigema Anty Sarood .Gabadaya sun kwaceta ni ko ganinta banayi..! Amina ta Kurama Inda Anty Sakina da Anty Sarood ke zaune Dukkansu Cikin Shigar Jallabiya baka Sakina ta saka farin hijabi bai kai kasa ba ammh Sarood bata saka ba Bakin Gyalen Jallabiyan ta nada akanta baka ganin komai sai Walwalin Fararan Hakoranta. Sakina na mata mgana tana Dariya wasu Dangin Anty Amarya suna kusa dasu suna ta Hira kamar Sakima na Fassara mata abunda suke cewa ne.. Amina tace"Wlh ba don Allah suka jata ajiki ba..! Hanne tace"Baba Mallam nata yabon Anty Amarya da Sakina..! Amina ta tabe baki batace komai ba. Suna nan zaune ana Rabo yan ajin su ya Abida nata Fama da jama"a kada su mike su Yamutsa wajen. Mariya tazo gabansu da buhun Take away din tana Fadin"An baku..? Amina ta ballata mata Harara kafin tace"Mu bama yunwarsa mun cisa agida har mun gaji..Wannan sai ke in an gama Rabon har sata sai ayi aje gida aci a kora da ruwan lemo an Dade ba"a Hadu ba gida babu makota sai Dai dai..! Mariya ta kallesu Tana mamaki Hamida tace"Bamu mariya ba"a bami ba..! Tayi yar Dariya ta Dauko musu leda uku .mai Ruwa da lemo ta miko kenan Amina ta kabar dashi ya zube akasa Mariya ta Dago tana kallonta Lokaci Daya tana Fadin"Miye haka Amina..? Amina tace"Bansani ba..Mun ce bamu bukata ko..? Ko kuma Hamida wlh ki fita Daga idona..Kina sawa wadanda basu kai ba suma raina mu..! Mariya kwashe ki hada da wanda kika Sata..! Mariya ta Duka tana kwashewa Cikin yar Dariya tace"Ko ba ku yi haka ba..Kowa ai yasan ku ba wata Tsiya bace Haushi dai kukeji an bani Rabo ku ba"a Kiraku ba..! Amina ranta ya baci tana Kokarin mikewa Hanne ta rike ta tana Fadin"Kyaleta..ana jin kunyi fada kinsan ce za"a ce baki da gaskiya..! Amina ta koma ta zauna tana Fadin"Bari mu koma Hadda wlh sai na Watsa ma Mariya mari in ban Daki bakinta ba Ranar asabar Allah ya Tsinan..! Cikin su ba wanda ya kara mgana suna nan zaune ba wanda yabi ta kansu Zafira tace"Amina kin hanamu karba..gashi yana neman karewa bami samu ba..! Amina tayi shuru kafin tace"Ku tashi muje..Koda bala"i sai mun Diba..! Binta sukayi har zuwa ajin Biyu inda aka Sauke duka kayan Rabon su ya Abida ne ke ciki suka Labe awaje suka Fito bata gansu ba suna ganin haka suka shiga ciki ya Umaima ce aciki sai wasu Daga cikin yan ajinsu sai ya Zeenatu suna mgana da wata. Umaima ce ta gansu batayi musu mgana ba tana zaune tana Duba Wani abu a Littafin Azkar din dake hannunta. Ganin haka yasa Amina ta kallesu a Hankali tace"Duka..Dauka..zura da gudu..! Sun san yaran yasa suka Bita tana Dukawa suma suka Duka suka Dumbuza Ledojon suka Zura aguje Sai alokacin su ya Zeenatu suka juyo suna kiransu Zeenatu ta rike baki tana Fadin"Ya Umaima su Amina ne ko..? Kai ta gyada batayi mgana bata son Hayaniya saboda ciwonta. Badiya yar ajinsu ya Abida tace"Aminar gidanku ko"ina sai ta nuna Hali..! Sai ga Abida ta shigo tana Fadin"in na rike su Amina sai nayi musu dukan Tsiya..! Ya Zeenatu tace"Ki hadasu da ya Nazeem ne yaci ubansu..! Kyafci tayi tana Fadin"Ku bar badawa hakanan..bari agama Walima sai mi fara Shirya na malaman mu ki hada musu da abun Rabon duka Zeenatu..! Suka amsa mata kafin ta fice Chan ta hango su Amina akarshe suma cin abunsu hankali kwance suna Dariya kai kawai ta girgiza domin tasan in tayi mgama zasu Raba Hali ne gaban Mutane. Mariya ce tazo gabansu tana Fadin"Kunci kun barsa ne naga har da Sata..?ama ci hannu baka Hannu kwarya..! Amina ta balla mata Harara tana Fadin"Mariya in baki bar nan ba na Rantse na mike bazaki ji da Dadi ba..! Mariya ta saka musi Dariya tana Fadin"Kudai ku ci kawai..! Harda gwalo Amina tace"in ba dagi bakin yarinyar chan ba ba sunana Amina ba..! Zafira na Tura Donut bakinta tace"Daga gani irin yan Shisshigin nan ne..! Amina tace"Kamar kin sani..Tusa kai ba kwarjini..kamar mayya..! Har Malaman da zatayi Wa"azin tazo suna chan baya suna Ciye ciye,Daya Daga Cikin matar wani abokin Baba Malam ne Sheik Ahmad Hadeja Ta iya Wa"azi sosai kawar Hajiya Babba ce ta na hallarta Dukkan wani Mahadara na mata sannan Har programme tana yi agidan Radio da Tv akan mata ta kuma yin Wa"azin aure irin wannan in gayyaceta Motace ta Lalace musu ahanya Anan garin Gumel din suke zaune. Nan ta fara Lacra