Sashe 53
Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da Hamida sun fara shiga Damuwa har gida Hanne ta koma ta tambayi ya Abida ko Amina ta shigo tace bata ganta ba. Ta sake dawowa ta Fadama Hamida,suka Rude suna wannan Tarardadin sai ga su ya Jafar sun shigo Sai suka kara Tsurewa kada su Farga ba Amina inda Allah ya Taimakesu har suka fita basu Lura ba Aminan ba,Suna Fita ba Dadewa sai ga Amina suna Daga cikin Daki sukaji ya Zeenatu na mata mgana tace Daga gidansu Hanne take Ya zeenatu ta harareta kafin tace"Hannen ai kina fita ta shigo..? Ko wata hannen dai ba wannan taki ba..? Amina sai ta fara Kifta ido kafin tace"Dakin su ta barni na kwanta bansan yammh tayi ba sai yanzu..! Ko kara kallonta batayi ba Jikinta asanyaye ta karisa Dakinsu kaifafun idanuwan Hanne da Hamida na kanta Hamnunta take Boyewa Cikim Hijabinta kada su ga Zoben azurfan da Aminu ya bata yau batasan me zata ce musu ba. Ganin yadda suka Zuba mata ido ne yasa tace"Wai lafiya..? Wannan kallon kamar naci bashin ku..! Tafada Cikin Hararansu Adole sai ta barsa da mganar dake ransu. Hanne ce ta mike tana Fadin"Amina ina kika je..? Amina tace"Ina kuwa..? Ina zuwa akace kinzo gidanmu naga bazan iya dawowq ba na shiga Dakin ku na kwanta..! Hanne ta kalli Hamida itama ta kalleta suka koma suna kallon Amina datake wani Kifta ido alamun ba gaskiya. Hamida tace"Yanzu Hanne ta koma gida..Ya Abida tace baki zo ba..! Amina ta saki karamin Tsaki Lokaci Daya tana Cire Hijabin jikinta take fadin"Bata ganni ba ko Hajiya batasan na shigo ba..! Ruwanku ku yarda ko kar ku yarda..Ku Tsayama Zargina kukeyi na tafi yawon banza ko me..? Hanne tace"Bata kawo nan ba..Muna gujemiki matsala.. Kinsan Fita zuwa waje ba Tarbiyanmu bame Amina kada ki Fara Halin da kike Dade baki yi ba..! Amina ta Zabga ma Hanne Tana Fadin"Bangane ba..? Kinga Hanne don Allah ki kyaleni bama son Hayaniya..! Daga haka tayi saurin Fita Daga Dakin kafin su ganota Dakin Mamanmu ta Fada tana Kiranta. "mamanmu Mamanmu..Na dawo..! Tana fita Hanne ta kalli Hamida kafin tayi mgana Hamida ta Rigata da Fadon"Karya take yi wlh..Acikin idanuwamta naga Karya Hanne..! Hanne tace"Nima nasan haka To ina taje batasan Fadamana..! Hamida tace"Wayasanun mata..? Kila gidansu wannan Zainab isan taje aro Littafin Hausa kinsan Amina..! Hanne tace"Ai ba Littafi a hannunta..! Hamida tace"Zai iya yuyuwa bata samun bane..Ina zata Daya wuce nan..? Hanne tace"Hakane..! Daga haka suka bar mganar ammh kamar acikin sun kasa yarda da cewa Amina gidansu Zainab taje sun santa in ma chan taje zata gayamusu ammh abun mamaki yau Amina bata son Hada ido dasu suna Zargin akwai wani Sabon Al"amari game da Amina sai kuma basu san komenene ba..! Tunda Amina taga sun Fahimceta sai tace Aminu ya Dakata da zuwa gidan su Hannen Data ke Fakewa dashi an ganota yasa sai ya kwana Biyu bai zo ba sai su yi mgana ta waya. Watarana Ranar da ta zama mafarin bakaken Ranaku acikin Rayuwar Amina da bazata taba manta dasu ba. Ranar da suka gama Jarabawarsu ta Karshe wajen kwana Uku basu mgana da Juna ba tasan yana chan Hankalinsa atashe jinta shuru ita kuma bata samu damar Daukar wayar ba akwanakin Mamanmu na Makale da wayarta bata samun Damaj Dauka duk hanyar da zata bi tabi bata samu Dama ba. Sai Ranar da Daddare Allah ya taimaketa Mamanmu ta ijiye wayar saman Mirror dinta Tana Dakin Aba tana gyaramai yau ita ke dashi. Bata Kira ba sai da taji Dawowar Abi da kuma Kai da kawon Mamanmu ashashen nasa sai da taji tsit alamun Tagama Zirga zirgan sannan ta shige Kuryan Dakin Mamanmu ta Kirasa yana ganin kiran ya biyo baya Tana Dauka ya Sauke Numfashi yana Fadin"Da baki kirani ba yau Meenata..gobe sai dai ki ganni agidanku..! Tasan zai aika shiyasa ta fara bashi Hakuri suna cikin mgana taji kamar Muryan Ya Zeenatu tana mgana da Sauri ta katse wayar,ta koma ta Lafe kamar mai barci sai dai abun da ya bata Haushi Falon Mamanmu Ya Zeenatun suka Dawo ita da Hamida suna Hira maimakon da da suke Falon Yaya ashe kanta ke ciwo ta kwanta Shiyasa suka barta ta Huta. Sanin in bata Lallashi Aminu ba zai ballo mata ruwa yasa tatashi ta Fito Falo tana mika kamar mai barci. Cikin Muryan barci tace"kun dameni ina barci Hamida..! Ya Zeenatu tace"Sai ki sauya Daki malama..! Bata ma Tsaya ba ta Tura baki tana Fadin"Na koma Dakinmi ni da Dakin uwata an koreni..! Tana jin Hamida na mgana bata tankata ba ta koma Dakinsu sam Tunanin ta Rufe kofa bai kawo mata ba ta Haye kan gado ta kira Amini daman yana Jira ya Kirata suka cigaba da mgana Korafi yake mata kan ya gaji zai zo yaga Aba ko mallan ita kuma tana kokarin numamai Lokacin bai yi ba. Sam ta manta a inda take hankalinta ya Riga yayi gaba bata shigowar Kowa ba bataji motsin ba ko Tafiya kawai sai jin wata Gigitaciyar tswar Muryan Aba ta karade Kunnuwanta Cikin kaushinsa yace"Amina..Amina Dawa kike mgana awaya..? Ba Amina kadai Hanjin Cikinta suka yamutse ba har da Aminu Dake Sauranta ya Rude domin Baya son Amina ta shiga matsala..yama ji ya kara Daka mata Tsawar yana Kara Fadin"Nace da Uban wa kike waya da Tsakar Daran nan Amina..? Tsawar da har Yaya sai da tadata ita Daga barci Mamanmu Zani a hannu Ita dasu Hamida suna Rigen rigen shigowa Dakinm Bayan ya shigo gida ne ya manta bai kulle gida ba yasa ya kara Fita ya kan yi Dube Dubensa atsakar gida kafin ya kwanta in sun manta da wani abu ya Kaudahi yana jin Hiransu Hamida bai leka Falon Mamanmi ba sai dai har ya wuce ya rika jin tashin mgana kasa kasa yasa ya Dawo da baya sai ya Fahumci Daga Dakin yaran ne. Kafafunsa suka jasa ya isa Bakin kofar Dakin Tar yaji muryan Amina tana mgana mamaki da al"ajabi yasa ya Daga Labulen Dakin ya Leka ya ganta kwamce tabama kofa baya waya a kunnenta tana mgana duk da bayajin me tace cewa ammh yasan ko wata wayavr bata Alheri bane. Har ya tako ya shigo Dakin agabanta bata sani ba Bai gama jin jikinsa ya Saki ba sai da yaji Amina na Fadin'"Haba Amin dina..Kasan nima ina sonka..Kuma nayi maka alkawarin Rayuwa Dakai har Abada..! Baisam Tunyaushe ta Fara ba sai da jikinsa ya fara mazarin da karkawan wani Bala"i ko yace wani Kangarewa ne ya samu Amina..! Amina fa itace cikin Dare tans waya da wani Gardi tana Fadamai tana son shi yar Amina da batasan komai ba.! Ganin yadda Amina ta yi sumar wucin gadi ne ga waya a kunnenta ta kasa Sauketa Saboda yadda Hanjinta ya Cure waje Daya. Aba ransa ya baci baisan ya karisa gabda da ita ba sai da taji wani gishiri Gishiri wajen bakinta Mari ne Aba ya Kamtseta daahu sai da bakinta ya Fashe wayar ta fadi gefenta Daidai Sanda Aba ke fadin"Ba mgana nake miki ba..Nace da Uban wa kike mgana da Daddare acikin waya..! Amina sai ta Fara ganin hazo Cikin Daburcewa take fadin"Ba...ba..kowa Aba..ba kowa..! Ransa ne ya kara baci Bacin rai ya Kushemwi sauran Hakurinsa baisan sadda ya Hada kanta da jikin gadonta ba ya kuma kake kummm...! Lokaci Daya ya hada da marin gefen Kumatunta yana Fadin"Zan miki karya ne..? Nace zan miki karya ne..? Yake fada Cikin bayanna bacin ransa Ihu Amina ta kwalla Saboda Ziyartan wani azaba Dataju asaman kanta da Aba ya,kuma Tuni wajen ya Fashe sai jini Daidai Lokacin da Aminu ya Katse kiran bazai iya jura ba bazai iya Juran jin Kukan Amina ba. Innalillahi kawai yake maimaitawa ya kasa zama yana Zagaye kyakyawan Bedroom dinsa kano. Gabadaya su Hamida sun Rude sun kasa ma mgana Mamanmju ce da Sauri ta Dira gaban Amina Daidai Aba ya kara Daga hannu zai kara Sauke mata ta Tareshi tana Fadin"Babansu zaka kasheta ne..? Nace zaka kasheta ne..? Tafada Cikin Tsawa hannunsa na rawa ya Nunata yana Fadin"Kauce ki bani waje Balaraba..! Yau Sai yarinyar ta Fadamin Tun yauahe ta fara wannan lalacewar bansani ba..? Waya na kamata tanayi balaraba da wani kato tana Fadamai bazata iya Rqyuwa bashi ba wani shigen ne yake Lalatamin Tarbiya yarinya bansani ba..! Yake Fada yana saka hannu ya Ture Mamanmu gefe da hanzari ya Riko Amina tana Ihu ya jawota ya makata da kasa,Daman Sa"idu bai iya Fushi ba bai iya Duka ba in ya fara kamar zai kashe haka yake yi. Hamida da Zeemati suka Rike juna jikinsu na Rawa Hatta Yaya ta Rude Amina kuka take tana Dafe da kanta Aba ya saka kafa zai taka Amina yana Fadin"Zaki gayamin ko sai na kasheki na Huta..! Yaya bata bari ba ta rikosa da Sauri Tana Fadin"A"a kabi a hankali kada kayi Hukunci cikin Fushi..! Mamanmi kuwq Amina ta Tarairayo Jikinta ta fashe da kuka tana Taba jinin goshinta Lokaci Daya take fadin"Abbansu jini fa..Zaka kashemin Diyata ne..? Bai Saurareta ba wayar ya Dauko Daga Saman gado yana Laluban wajen kira Lambar Aminu ce ta karshe kuma ita ya Kira yana so yaji wani Lalallacen ne yana Tarbiya yana Daga waje yana kokarim Rusa komai..! Lokacin da Aminu yaga Kiran yana mgana da Nenne a Dayan wayarsa yana gayamata Halin da ake ciki ganin kiran yasa da Sauri yace"Nenne MEENA na kira..! Tana so tace mai kada ya Dauka kila ba Aminan bane ammh bai jita ba ya Datse kiranta ya Dauki na Amina. Aba a speaker ya saka wayar Daidai Sanda sukaji Muryan Aminu yana Fadin"MEENATA..meena Aba bai Dakeki ba ko..? Hankalina ya tashi! Su hamida suka kwalalo ido Amina ai sai taji miyanta bakinta ya Tsaya Cak yau kafin safe kila sai dai Buzunta Aminene sai ta Tarihinta Aba yaji kansa ya Sara Cikij kaushin Murya Da takaici yace"Ba Meenar bace..Uban Aminan ne Sa"idu..Waye kai..?Meyasa ka zabi ka Lalatamin Tarbiyan da nayi Shekaru ina ginata..! Nace meyasa..? Aba ya karishe cikin Tsawar data gigita su mamanmu Hatta Aminu dagachan bangaransa ya kasa mgana baisan sadda ya Datse kiran Ba shikenan komai ya kare. Wannan Ranar daman yake gudu. Yanzu ta ina zai fara? Ko yace ba yaudaran Amina yake yi bawazai yarda