← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 193

Sashe 67

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tunda ta fara mgana wannan kamilar Fuska mai cike da Annuri da Tsausayi ta rine ta koma Bakar fuska mai Cike da mugunta da rashin Imani Cikin Wata Murya mai cike da Amon Takaici da Bakinciki tace"Da sanina Bazan bari haka ta faru ba Madina..!
Wlh ban sani ba..Kamar yadda kikaji abun Daga sama nima haka najisa..Shammatan mu Mallam yayi..Shammata mai girman da bamu Taba Tsammani ba Madina..!
Dagachan bangaran Agidan Baba Mallam ashashen Anty Amarya itama Cikin Tsakiyar Bedroom dinta tana Tsaye gaban makeken madubin Dakin nata tana kallon Fuskarta Data wani yarkace na Wunin yau kawai tun bayan Samun Labarin Daurin auran Amina da Umar..!

Cikin Muryanta mai Fadi da ba kowa ya santa da ita ba tace'"Lalle ko ya shammaceni Dayyaba..Sai da na Riga na gama Tsara komai..na gama Tunanin matsala tadaina shigomana cikin Aikinmu ashe suna chan suna Shirya ganina akasa..To basu isa ba..In a zaune suka kwana Ni Madina a tafe na kwana nayi alkawarin yadda bansamu Mallam ba ta bangaran Sakina Da Umar sai na Juya ragamar Mallam da duka abunda ya mallaka..Karya ne..Bayan sakina ba wacce ta isa Umar ya sota har ya Hada Jini da ita Sakina kadai keda Alhakin Haihuwa da Umar ita kadai ce Zata Haifama Mallam Yunus Bazanga Jika,Abaya nayi Sakacin da Har Ya"ya Biyu suka fara Fitowa daga Tsatson Nazir nayi sakaci Dayyaba..Sai dai kinsan aikin da mukayi ya"yan Nazir baza su taba Tasiri a wajen Mallam ba..Kacokan Burina na wajen Abunda Sakina zata Haifane..Sai da nace miki Mu kauda yarinyar nan Dayyaba kika ki bani goyon baya ta rasto cikin Aikin mu batare da Mun gayyaceta ba gashi nan yau Rana Daya ta Fadomin cikin Tsarina Tsarin da bazan taba bari ya Rushe ba Koda hakan na Nufin za"a rasa rai ne..Na kasa gane miki ko kin fara Sauya Ra"ayi ne na Sauya Duka Tsarina Dake..Kila kin hakura da Abunda Sa"idu yayi shekaru yana Kunsamiki ne shi da wannan Munafukar matar tasa..Ko kuma kin shagala kin Fara Kaunar wannan Hatsabibiyar yarinya Dake nemam batamin Shirina..!

Fuskar MAMANMU nake gani ta koma Jawur idanuwanta sun kala sun sauya Launi jijiyoyin kanta har sun Daga Saboda Bala"i cikin wata gigitaciyar Tsawa tace"Dakata Madina..!
Har Abada ni Dayyaba bazan manta Da Bakimcikin da Sa"idu shi da Hadiza suka Dade suna kunsamin ba..Wannan Kaunar wannan Tsausayin da Soyayyar da nake gani acikin Idanuwan Sa"idu kan Hadiza saura kadan su kaini kushewata Har Gaban Abada bazan yafe musu wannan ba..Sai sun Dandanan gudarsu bana yafiya.. ni din nafi Rama Sharri da Alheri..kamarni Sa"idu zai kallah gaban Ya"yana da Matarsa ya SAKENI madina kan wannan Shegiyar yar tasu..?Yarinyar da duk cikin ya"yan Hadiza nafi Tsananta saboda iyayanta sun fi sonta..Sa"idu ya Dade yana kunsamin Bakinciki ya fifita soyayyar Hadiza Fiye da tawa sannan yazo ya fifita ya"yan Hadiza Fiye da ya"yana Saboda Ban Haifi namiji ba ko..?akoda yaushe in na Bude ido na ga Jafar sai naji kamar na kashe kaina..Meyasa na barsa araye ban saka malamin mu ya Kashesa ba..Da yanzu ba haka ba Madina Da yanzu na Dade da kunsa ma Sa"idu da Hadiza bakin cikin da Har su koma ga Allah bazasu manta ba..Duk Saboda Cikar Burina na aro Fuskar da ba tawa ba Madina..Ina zaune cikin wadanda nafi Tsana ina Fifita ya"yam makiyiyata Fiye da ya"yana ina Faman kare ma wanchan yarinyar da bata da wani amfani a wajena...Madina Dukkanmu mafita muke nema saboda haka koma menene ki Fadeshi zan yarda zan amince zuciyata zafi take madina Amsa kuwar Sa"idu nake ji yana Fadamin ya Sake ni Saboda wannan Shegiyar yarinyar ina so suma su Dandana ina so suji yadda na daukii shekaru ina ji acikin raina..!

Anty Amarya tayi Mirmishin Dayafi kuka ciwo kafin tace"Sakacin ki ne Dayyaba..Tun Lokacin da aikin malam ya Tsallake Jafaru ya koma kan Amina nace a kaudashi kika yi yarda..Da yau baya Raye Da wane d'a Sa"iidu zai yi takama..?yau gashi dan Zaki ya Girma harda albarka Haihuwan wani karamin Zakin Dayyaba anya ke naki Tsarin ba Doguwar Tafiya bace..?
Da Sauri Mamanmu tace"Bana kallonshi a Faduwa Madina..Jafar da Abunda ya Haifa ba su da wani amfani kadan nake jira na karar da su..Yanzu ni Sa"idu zan fara mgani Tukunnah so nake naga bakimciki da Rauni acikin Idanuwansa Madina..!

Kai Tsaye Anty Amarya tace"Za"a rasa rai...YAYA ZATA MUTU...!

Mamanmu tace"TABBAS YA KAMATA TA MUTU..sai dai naso sai ta gama shakan bakincikin da na Dade ina Tanadama mata madina..!
Anty Amarya tace"Yanzu Lokacin Daya kamata ta Mutu ne Dayyaba..Mutuwar ta ne kadai zai sa kiga wannan Bakincikim acikin Idanuwan Sa"idu..Mutuwarta ne zai sai nima naga Sa"idu ya koma abun Tsausayi ya dade yana min katsalanda Shi da Hajiya Babba..Zamu fara ta kansa ne kafin mu dawo ta kanta da Saninsa aka Aurama Umar Amina..Da saninsa ta shigo Tsarina nima wannan Damar nake jira da Zan Dandana ma Sa'idu koda Rabin abunda nakeji ne game dashi..Komai na ke kokarin samu Shi da Hajiya babba sai sun tare ni Dayyaba..!
Cikin wata irin Dariya tace"TABBAS yakamata ta Mutu...!
Zata mutu..!
Anty Amarya tace"Zan kira mallamin mu Dayyaba zan sanar dashi ya yanke mata wa"adinta kafin wayewar gari bazan jira ba..bana son wannan karon asamu matsala..!
Mamanmu tace"Nima haka..Wayewar garin gobe Ranar mu ce..Na kosa na kosa naga wannan bakimciki akallon da zan ma Sa"idu..Babban kuskuransa shine ya Fifita komai na Hadiza akaina..Babban Raunina Ina SON SA'IDU..!
Anty Amarya tace"Shikenan kada ki damu ki Dauka an gama..Mganar kudi akwai wani abu a hannunki..?
Mamanmu tace"ki kamallah komai in mun hadu zamu warware komai..!
Anty Amarya tace"Shikenan..Mganar yarinyar nan baki ce wani Tsari zan kaita ba..?
Mamanmu ta saki Dariyan Nishadi kafin tace"Ban damu ba Madina..Ni Kaina na sani Dagani sai ya"yana..Ki kaita Duk Tsarin da kika ga Dama..Koda Tsarin na MUTUWA NE..!
Anty Amarya tace"Tsarin bana Mutuwa bane..Zata sha wahala ne kawai sai daga baya mu kaudata..Tsarin da na kai Balarabiyar nan Tsarin zan kaita Dayyaba..Hotuna zasu zama wajen Umar har Abada Sakina ce Zata Cigaba da amsa matsayin mata awajensa..Wannan alkawarin ne..!

Mamanmu ta jinjina kai tana Fadin"Hakan yayi daidai..Daga gobe komai ya Dawo hannuna..Daga Sa"idun har ya"yan nasa..basu san Wacece Dayyaba ba..Balaraba Ita suka sani..!
Dukkamsu Dariyan suka sheke da ita Dariyan cin nasara da samun Duniya lokaci daya suna yanke kiran atare..!
Abunda basu sani ba wani abun Allah ya Riga ya kaddaran Faruwansa bakin Alkalami ya Riga ya Bushe..!
Tabbas za"a rasa rai..Sai dai basu isa su Dauki ran wani ba..Daman chan ita ran Lokacinta yayi ne..!
Suna gama wayar ta Wurgar da wayar saman gado ta fara Zagaya Dakinta Cikin kaushin murya take fadin"Allah Sarki Yaya..Yau za"a amsa kiran Allah..!
Wayyo wayyo..!
Haka take ta fadi sai kuma ta kece da Dariya kamar mahaukaciya kafin ta koma ta Duke kuma sai ta saki kuka Lokaci Daya tana Fadin"Ba haka naso na zama ba..Sa"idu kai ne sila..Na soka Tun kafin ka fara son Hadiza..Me na rasa baka taba sona ba..?Kasha bansan auran biyayya kayi dani ba..?
Kasha bansan ka Tattara Zuciyarka ka bama Hdiaza ba..Wannan son shi ya ja maka kai da ita..Wannan Tsausayin shi zai kasheta Sa"idu..Ba Laifina bane..Laifin SOYAYYARKA CE..Bantaba son wani Namiji yadda na SOKA BA
Koda bazaka soni ba nayi alkawarin baka isa ka so wani ba..Komai na ya"yanta ya zarce nawa..Duk yadda naso hakan bata Faru ba sai da na zama koma baya agidanka..Kasha bansani bane.?bakayi karya ba nasan Amina ta fara soyayya da wani..bakayi karya ba..Nasani naki fadamaka Saboda Daman ina son damar da zata kara Ruguza rayuwar Hadiza..ban so abunda ya faru ya Tsaya nan ba na so ne Tayi Cikin shege na Tsawartsaku gabadaya..ba Laifina bane..Yaya ki yafemin Sa"idu ya ja miki MUTUWA..!

Take fada tana Hawaye Lokaci Daya Dadariya tana Tuna ranar data fara kama Amina tana waya da Aminu acikin bayinta bata nuna ta ganta ba..Hakan ya mata Dadi Domin bata kaunar cigaba Daga bangaran Hadiza ita da ya"yanta Tundaga Lokacin Da gangan take ijiye wayarta Har Aminan take samun Daman Dauka ta kuma fara Bibiyan Motsinta abunda kowa baisani ba Hatta Haduwar da take yi dashi duk tana sane..Taso ta shirya wani abu ne..Taso ta yi amfani da Amina ta Tsarwatsa Yaya da ahalinta sai dai Mallam ya shammesu matuka shammatam da basu taba Tsammani ba..!
Abunda bata sani ba..Ba Mallam bane Allah ne ya Rubuta abunda ya Faru Daki Daki..Su basu isa su Hana Al"amarin Allah ya Faru ba..Zanen kaddaran ya zama kuma bawa bai isa ya goge shi ba..!
Chapter 67 · 0% Book details