← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 193

Sashe 43

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsawon kafa ne kawai Kafada ya Daga kafin ya Nufi Cikin shagon Dutse zasu koma yanzu nan Kati ya yanke ma Ogansa acikin waya suka Tsaya su siya to lokacin ankirasa a waya ya Dauka sai Ya kasa jira ya fito da gansa zuwa Cikin Shagon..! Amina bata kara mgana ba ta fara tafiya da Hamzari ya sha gabanta yana gyara zaman Jaket din Dake Jikinsa Cikin Mamaki da Budewar ido Amina tace"Malam lafiya?Mtsamin Daga Hanya tunda bata gidan ku bace..! Mirmishi yayi har sai da Fararam Hakoransa suka bayyana Cikin Muryansa yace"Wani ya taba Fada,miki kina Burgesa..? Yafada yana kallonta Cikin wani Salo Sai kuma taji mganar ta shigeta Cikin Sausasauta Murya tace"Ni AMINA ba wanda ya taba cewa ina Burgesa..Ni ai bana Burgewa kowa.! Wayarsa ya saka Cikim Aljihun Jaket dinsa Lokaci Daya yana Fadin"To yau Ni AMINU BUBA..kina Burgeni...! Ido Amina ta zaro tana kallonsa mganar ta shigeta kanta ta kara nunawa kafim tace"Da gaske ina Burgeka..? Kai ya gyada mata Sai ta washe bakinta kafin tace"Nagode..yau na fara ganinka ammh naji Dadin Haduwa Dakai domin kai ne Mutum na Farko Daya fara cewa Amina Aminene na Burgesa bazan manta da wannan ba..Thank you..! Tafada tana Juya idanuwanta cikin bayanna Farimcikinta Shagala da kallonta yayi baisan ya Furta"She is Beautufull...! Bai an kara ba yaga tana Shirin Tafiya da Sauri yace"Ya zaki tafi kuma ki barni..? Da mamaki Amina tace"Bangane ba..? Mirmiahi yayi kafin yace"Ke yar nan garin ce..? Da kai ta amsa mai cikin mamakinta da kuma kara ganin yarintarta yace"Ammh baki sanni ba..? Amina tajuya ido kafin tace"To a ina zan saka bawan Allah..? Da sauri yace"Sunana Aminu..Aminu Buba..! Nayi matukar mamaki da baki sanni ba Shekararki nawa ne..? Amina tace"Shekarata goma sha Biyar da Wata Goma saura wata biyu na cika Sha shidda..! Tafada tana Kirgamao da hannu Dariya ta kamasa har sai da Wushiryansa ta bayyana. Tsayawa tayi tana kallonsa yadda yake Dariya abun sha"awa. Cikin Matse Dariyansa yace"Amina..Amina kina Burgeni..! Zan so na rika ganinki koda yaushe ko domin ki rika sakani Nishadi Aji nawa kike a makaranta..? Kunya Amina taji yasa ta sunkuyar Dakai kafin tace"SS1 sai monday ammh zamu fara zuwa..! Yana mata Dariya yace"Kice Jjc ne...! Amina yan matan SS1..! YAadda yake Dariyan ne ya fara Kular da ita yasa ta Hade ranta Nura Daya Fito Daga shagon tun dazu ya gaji da ganin wannan Drmar yayi gyaran Murya yana Fadin"Oga lokaci fa na Tafiya....! Hannu ya Dagamai kafin ya fiddo da wayarsa yana mikama Amina Lokaci Daya yace"Sakamin Lambarki..Amina ai daman kawar Aminu ce ko..? Yafada yana Dariya itama Dariyan Tayi Domin Farat Daya taji ya burgeta kamar yadda yace itama ta Burgesa. Noke Hannu tayi kafin tace"Ni ai bani da waya..! Ido ya zaro kafin yace"Duk girmanki Amina saura fa wata Biyu ki kai shekara goma sha Shidda! Ya karishe Fada Cikin Zolaya Da sauri Ta kauda kai tana Mirmishi Kara Tura mata wayar yayi yana Fadin"Ko lambar Antynmu Babu Amina..! Amina tace"Tab..Bafa mai waya agidanmu Daga yaya sai mamanmu to ta yaya ma Jawaad ya jefata ruwa .Ta mamanmu ce kadai ta rage sai kuma ta Aba..! Da sauri yace"To sakamin ta mamanmu ko Aba din..! Ido ta zaro kafin tace"Tabdijam..Rufamin asiri ba ruwana kaga mallam bansan ka ba sai anjuma..! Kafin yayi mgana ta wuce da Sauri harda gudu Kiran sumanta yake yana Amina..Amina ita ko Waige batayi ba sai dai ta kule ya Daina ganinta sannan ya Dafe kansa. Nura ya kariso yana Fadin"Oga Oscar na Kira na fa kuma nasan kai yake nema..Sannan ka koma mota kafin mutane su farga Dakai..! Lokaci Daya yana mikamai katin Daya siyo Airtel na 1k Mtn ma haka bai tsayama karba ba ya wuce Ya bude gaban wata Farar Bugatti ya shiga yana Fadin"Nura bana son mita..Kyale Oscar tukani muje kawai..! Kai ya girgiza yana mamakin Yar yarinya karama Oga ya zauna yama bata Lokaci a kanta kafin ya Zagaya ya shiga Mazaunin Direbs ya Tada Motar sukar bar Layin da gudu kamar zasu tashi Sama. Koda Amina ta koma gida sai da Mamanmu tace"Amina ina kika Tsaya..! Amina tace"Mamanmu chanji ne Babu..! Da wannan karyan ta Kashe mganar Duk Surutunta ta kasa bama ko Hamida Labarin Haduwarta da Aminu buba kamar yadda yace sunansa Ranar duk in ta Tuna sai tayi Mirmishi ita kadai a kallah yau ita Amina ta samu wanda yace komai nata na Burgesa ashe itama Macece kamar kowa wannan yabon ya xauna aranta da Har Abada bazai fita ba. Ko washegari a hadda bata yarda ta Fadama ko Hanne da bata boye mata ta kasa bata Labarin Haduwarta da Farin mutanin da ya kasa barin Ranta Ko yaya ta Tuna dashi sai ta murmursa acikin Ranta. Da suka tashi Sallah ne Amina ta kalli Hanne suna wajen alwala Tace"Hanne ashe nima ina Burge mutane..? Hanne na kuskure baki sai da ta Furzan da ruwan bakinta kafin su hada ido da Hamida suka kwashe mata da Dariya Duka Amina ta Dirkama Hanne a baya tana Fadin"Bana son iskanci ban tambayi Hamida sanin Halinta yar black stomarch ce..! Hanne na Dafe inda ta Daketa tana Fadin"Muguwa..Uban wa zaki Burge..? Hamida ta Karbe da cewa"Sai dai ki Gunduri mutane Jidalinki Amina wlh bAmai iya Daukansa sai mu da muka Saba..! Hanne tace"Wlh wani waje duka zataji in taje tayi..! Dariya suke ta mata ita kuma bata su take ba Hankalinta ya tafi Tana Jin Muryan Aminu sanda yake Fadamata Tana Burgesa ita din abar Burgewa..! Daga Ranar bata kara musu mganar ba sai dai yana Ranta Lokaci bayan Lokaci yana Fado mata acikin Ranta. Har tazo Ranar Monday suka fara zuwa makaramta Sun samu Dalibai irin su da suka Cigaba da Unity sannan akwai Sabbin Dauka kamar yadda aka saba Amina ta cigaba da abunda ta saba sai ma abunda yayi gaba ta addabi Dalibai da malamai Sai kuma akayi Rashin Sa"a aka hadasu aji Daya da Sa"adatu Hanne da Hamida Ajinsu Daya. Amina kamar ta mutu saboda Bakimciki tace ma Hanne"Naso aji Daya aka hadamu hanne..Sai dai ban da Sa"a anhadani da Shegiyar Sa"adatun nan..! Hanne tace"Ina Ruwanki da ita..? Amina tace"Ta shiga Harkata Dakuwa zatayi..! Sa"adatun bata shiga Harkan Amina Saboda Anty Amarya taja kunnenta Sosai kan Amina shiyasa ko Aminar Zata takaleta bata bi ta kanta. An hadasu Aji Daya da Zainab Isa Kawar Amina sai suka Kulle atare Sit dinsu Daya Dalili kuma tana Aro mata Littafan Hausa na kishiyar mamanta take Sato musu ta kawo makaranta su karanta ita Zainab Amina take kawo mawa,ita sai agida ta ke shigewa Dakinsu ta Boye ta karanta sannan bayan su Hanne Zainab isa ta jure Gwagwarmayan Amina da Jidalinta. Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah su Amina sun mika cikin Zangon karatunsu na Farko a SS1 dinsu cikin salama da kwamciyar Hankali kamar Amina tayi sanyi Saboda ta Rage Tonon Fada sao dai jidalinta da Masifarta sai abunda yayi gaba Dakyar Hajiya ta rokar musu Baba Mallam ya bari Idi Direba yakai su gidam ya Ikram Dukkansu har da su ya Abida su Amina an sha Murna har Fada sai taja su hanne suka shiga da karambaninta. Abida tace"Kai amina bala"i wlh watarana sai takai kanta inda zata mutu..! Ya Ikram tace ko ita sai da mijinta take shiga Gidan Sarki batama san Hanya ba sai ga Amina tana kutsa kanta Kusfa kusfa,Chan suka mata wunu sai yammah suka dawo suna Santin Haduwar gidan kamar aturai Amina tace"gaskiya gida biyu suka tabamin kyau..Daga gidan ya Danmallam sai gidan ya ikram..! Hamida tace"Gaskiya gidansa shima ya Hadu tsarin daidai kamar aturai..! Haka dai suka santin gidan Har Mamanmu na saka baki tana basu Labarin Tsaruwan gidan Sadiya Dake Dutse Amina tabe baki tayi batayi mgana ba sai da Hamida tace"Kai zan so naje ngani mamanmu..! Yaya na gefe tace"Naji kamar ance cikin watan man zata bi mijin chan kasar Dayake aiki..! Mamanmu tace"Nima haka naji Haj.Nasara na tadin ita da Haj.Uwa..! Amina tace"Ni kam ban sha"awar zuwa..Nasan bazai kai yadda nake Hasaahe tsaruwa ba..Shiyasa naga yau Sa"adatu nata wani yamutsa Fuska araina nace an ga inda aka fi su..! Hamida tace"Kai Amina baki son zaman lafiya..? Balla mata Harara tayi kafin tace"Eh din ke kuma an tabo masoyiyarki..! Ganin zasu fara fadan nasu ne mamanmu ta Tsawarta Ya Zeenatu na Gefen Yaya tace"ZAman lafiya ko na Minti Daya ne Amina bata kaunarsa..! Amina na jinta ta Daga kanta sama aranta tana Fadin"Eh din..! Nan dai mganar tatashi ta koma Tsakanin su Mamammu da su Hamida Amina bata kara saka baki ba Kada tata ta karayin zafi. Ana cikin haka acikin Satin Matar ya Jafar ta Haihu Anty Shamsiya. Su Amina Sai ana gobe suna suka samu zuwa barka shima din su Yaya da su Hajiya sukabi da zasu barka mamanmu ita ke zuwa tana Ma jarori wanka wanda yaci sunan Baba Mallamm. Suna zaune Jaririn na Hannun Hanne Amina ta karkato tana Fadin"Wlh bakinsa Sak na uwar ne..! Hanne ta Zunkuleta tana Fadin"Ba Ruwana Amina..kada taji.! Amina na Danne Dariyanta ta Dago tana Fadin"Mamanmi kalli jaririn nan yana karami bakinsa babba..! Hamida da Hanne da suka san mganar suka yi tsumu tsumi. Hajiya Uwa ce tace"Banda abunki Amina ai jariri ne yana girma zai Sauya..! Mamanmu tace"Mai sunan mallam fa Shamsiya ce Sak..Kila sai nan gaba zamu ga Jafaru..! Akayi Dariya Shamsiyan na gefe batave komai Amina nata Dariya sai da suka fito zasu tafi Hamida ta jawota Tana fadin"Amina wlh ki bari ba kyau kushe hallitar Allah..! Hanne tace"Kuma bata son me zata haifa ba! Amina ta toshe kunnenta tayi gaba Tana Fadin"Nagode da wa"azi Malama Hamida da malama Hanne..! Kyaleta sukayi ganin bazataji ba Washegari sun so su koma Mamanmu tahanasu tunda ya Jafar din yace ba suna ba Taro an dai yanka Raguna Mallam yaje yayi barka da kansa. Ranar kwatsam sun je makaranta sai ga Zainab tazo da karamar wayar Tecno mai memomary,Tsohuwar ta Anty ta ce aka bata akwai Memory aciki ita Amina waya ba Damunta tayi ba Shiyasa bata Damu ba Acikin yan ajinsu akwai masu yawa Ranar an tashi Break Taji Zainab na ma wata Saratun ajinsu mganar ta Turamata Sabbin Wakoki Tana Daga sit dinsu tana karatin Wani Littafin da Zainab ta aro mata mai
Chapter 43 · 0% Book details