← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 193

Sashe 69

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Gabadaya gidan Baba Sa"idu haka suka tashi zuciya ba sukuni,Wasu sun samu barci da yar natsuwa ammh akwai wadanda basu runtsa ba ciki har da Amina domin yadda taga Rana haka taga Dare ita ba kuka take ba Domin zuciyarta ta kekashe bata ma jin yin kukan abu daya ta sani bata son tuna inda kaddaranta ta jata ta kaita domin in tana tuna yau ita ta haramta ga Aminu sai taji gabadaya Duniyar na juya mata,Abu daya yake mata nauyi acikin kirjinta Aminu shi take so ta san wani hali yake ciki ammh babu dama sannan sai Aba da Yaya wanda bata taba tsammamin Fushinsu zai dameta ba abu daya ke damunta Shedar iskanci da suka Zargeta dashi sauran bata damu ba Domin ta aikata ammh abu daya ke sata bakinciki yadda aka kasa Fahimtar abubuwan da suka faru kan yadda suke..!
Tun bayan data idar da sallar asuba bata jirga daga inda take zaune ba ta kalli gabas da katon hijabin haddarsu bangon Dakinsu ta kurama ido ita ba kuka take ba ammh kana ganinta kasan bata cikin natsuwarta cikin kwanakin nan gabadaya Amina ta Zafge sai idanuwa fuskarta tayi wani iri tayi zuru zuru Hamida da Hanne ne ke tare da ita acikin Dakin Domin Ya zeenatu ta fita Kitchen ita bata koma barci ba.
Hanne ce ta gaji da ganin Amina ahaka yasa tatashi tsam ta koma kusa da ita tadafata tana fadin"Amina don Allah kiyi hakuri..Ki yi hakuri..Haka Allah ya kaddara miki!
Kamar bazata tankata ba tama yi Tunanin bata jinta yasa ta kara Girgiza kafadanta tana Fadin"Ameena kina jina kuwa..?
Sai alokacin Amina tayi motsi da bakinta Cikin wani irin Sautin da Hamida da Hanne zasu iya Rantsewa da Allah basu taba jin Amina cikin wannan Sautin ba..!
Asaman lebenta mganar ta fito cikin karyewan zuciya da Rayuwa tace"Ina jinki Hanne..Tun jiya keda Hamida kuke maimaita kalmar nayi hakuri..Tawa kaddaran kenan baku Tunanin na Haddace wannan..?
Tafada Lokaci Daya tana sakarma Hanne manyan Idanuwanta cikin wanu yanayi na neman ma tallafi Dayasa Hanne saurin kauda kanta Tana fadin"Na sani..Ammh ki sani mai hakuri shi ke da riba watarana..Ko Hamida..!?
Hamida da duk jikinta ba Dadi tace"Sosai ma Hanne..!
Tana jinsu gani take su din suna cikin Farinciki tunda rayuwarsu bata yi musu juyin waina kamar yadda tayi mata ba..!
Kara murmusawa tayi wanda kana ganinsa zakasan ba Annuri ko jin Dadi acikinsa tace"Hakane..Nagode bazaku je hadda bane..?
Ta fada tana son kauda mganar domin tasan bazasu taba gane wani Hali take ciki ba..!
Hanne ce tace"Bazamu ji dadin zuwa baki ba Amina ki saki jikinki..Sati mai zuwa sai mu koma tare..!
Amina taji kamar tayi kuka alokacin Dama dama ace baya zata dawo Da tafi kowa jin dadi bata samu zarafin mgana ba Hamida tace"Ni kaina bazan ji dadin zuwa ko"ina ba baki ba Amina..Tare muka tashi muke komai tare..Wh damuwarki tamu ce Amina don Allah kiyi hakuri..!
Tana Fada sai kuka hakama Hanne sai ta rumgume Amina tana kuka hamida ma tazo suka hadu suka Rumgumeta suna Fadin"Amina wlh mu zamu shaidarki..mun sani Fahimtar hakane basu yi ba..!
Amina cikin wani irin kuncin zuciya tace"Wlh ban taba iskanci ba..Bantaba kadaicewa da Wani Namiji ba da sunam alfasha ba..Abunda ya faru ranar Tsausayi ne..Wannan itace kaddaran daman datake jiran bawa koda yaushe..?
Itace kaddarata sannan kuma natabbata na Fita zakkan da ake yawan Fadi akaina Tunda gsshi ni Tawa Rayuwar ta kare ba yadda ta kowa take karewa ba..Hanne da Hamida kun ji dadinku bakinciki bai gauraye jin dadinku ba..Wlh ayadda nake ji dama ace Ban hadu da Aminu ba dama komai kamar mafarki ne..!
Take fada sai kuma ta fashe da kukan da ba Hawaye daga gani abun yana Fitowa ne daga kasan ranta ne
Haka suka hadu suna ta kuka kamar wasu yara bame lallashinsu cikin wannan yanayin sukaji muryan Ya Zeenatu tana Fadin"Jawaad wai lafiyan ka kuwa..?
Me yayan zatayi maka Dakake ta mata wannan uban kiran..!
Muryan Jawaad sukaji a Tsakar gida yana Fadin"Ya zeenatu tun dazu nake tashinta taki tashi..!
Tana daga kofar kitchen ta Hararesa yana Sanye da zani da alamu wanka yayi Cikin dan fada tace"Bazaka je ka shirya ba sai Idi ya tafi ya barka ko..?
Cikin Tura baki yace"To ai ban ga Jallabiyata ba shine nake ta tashin Mama ta Daukomin taki tashi..!
Domin kaf gidan nam Jawaad kadai ke kiran Yaya Mama shi har alokacin sunan Yaya bai kama bakinsa ba..!.
Ya zeenatu da mamaki ya kamata tasan yaya bata barcin safe In ta idar da Sallar asuba sai gari ya waye tana Lazimi koda bata ga fitowarta ba Tasan tana da Bayi adaki kila ciki tayi Hidimarta ammh cikin son kwantar da Hankalin Jawaad yasa tace"Kila barci ne ya Dauketa bayan tayi sallah jeka ka Duba cikin Dirowa kila ka gani kayi sauri fa..!
Har ya juya sai ya juyo yana Fadin"Batayi sallah ba fa ya Zeenatu..!
Dam gabanta ya fadi cikin Fitan hayyaci tace"Bangane ba..!?
Cikin yarintarsa yace"kuma fa bata motsi..!
Karaf Sai a kunnen Mamanmu Dake zaman jiran wannan sakon ya isketa Mikewa tayi bakinta kamar ya Tsage Cikin Yar dariya tace"Komai ya kamallah..!
Daga haka ta gyara yanayinta Lokaci Daya tana fitowa alamun barci a idonta tace"Zeenatu me ya faru nake jin hayaniya..!
Zeenatu da Hankalinta ke tashe tace"Mamanmu jawaad fadi yake yaya bata motsi fa..?
Ido ta zaro tana fadin"Bata motsi kamar yaya..?
Tafada cikin bayanna Firginta Wanda ya fito dasu Hamida Daga daki har da Amina Da suke jin meke faruwa gabanta ke fadi jikinta ke rawa tana Fatan ba wani abu bane zai kara kutse Cikin Rayuwarta ba..!
Ya zeenatu ce kan gaba wajen shiga Dakin Yaya har bedroom dinta jawaad suka kara samu akanta yana jijjigata yana faman fadin"Mama ki tashina ina jallabiyata..?
Yake fada ammh ko gizau dukkansu kamar an dasasu sun kasa karisawa gareta tana kwance sambal Cikin Hijabinta,fuskarta tar ta kara wani Haske sai dai abu daya ya Sandarar dasu shine ganin Idanuwanta suna kallon Saman Dakin ammh kuma bata Motsi gabadayansu kamar an Sassake jikinsu haka suka kasa karisawa..!
Jawaad daya gansu ya sauko yana jan Hannun Mamanmu yana fadin"Mamanmu taho ki gani..!
Haka yake fada kamar rakumi da akala haka ya jata har gaban gadon yaya inda take kwamce daidai Lokacin da sukaji sallaman Ya Jafar Ya zeenatu kamar walkiya ta fice da Sauri kamar ta kifa a tsakar gida taga ya Jafar Bayansa Aba ne,Kaya ne ahannun Ya Jafar da bargo da Filo sai Kwandon abinci,Bata Tsaya ko Gaida Aba ba tace"Aba ya jafar kuzo ku gani Yaya bata NUMFASHI..!
Dukkansu haka mganar ta shigesu Aba kuwa dakyar ya iya Tsayuwa da Kafarsa Meke faruwa ne..?,Tabbas wanu abu ya faru ko kuma zai faru Domin Tun jiya yake fama da Faduwar gaba da yanayi mara Dadi sai ya Danganta haka da Kila abunda ya faru ne na Amina ammh kalaman Zeenatu sun saka gabbansa kara Saki Cikin wani yanayi.
Ya jafar ne ya tsaya yana fadin"Bangane bata Numfashi ba..?
Aba bai Tsaya sauraransu ba ya taka ya shiga Dakin yaya jafar na ganin haka ya watsar da kayan Hannunsa yabi bayansa Zeenatu sai ta kasa Binsu kafafunta sun kasa Daukanta koda batasan Mutuwa ba Ta tabbata yaya MUTUWA tayi..!
Ba wanda yasan da shigowar su Aba sai dai ganinsu kawai akayi Kamar Daga sama Hamida da Hanne da Amina sun rirrike hannun juna cikin wani yanayi Mamanmu tana ganin Aba sai ta fara sauya yanayinta Taga yadda take kallon yaya tana Sakin Mirmishin jin dadin.
Kan jikinta ta fada lokaci Daya tana Fashewa da kuka sai kuma ta Mike ta Nufi Aba tana nunamai yaya Lokaci Daya tana fadin"Sa"idu duba ka gani..Kamar yaya ta MUTU fa bata motsi..!
Kalmar ta Mutu shi ya shiga kunnen Amina da wani yanayin da har Abada bazata manta dashi ba..!
Aba kuma sai ya Ture Mamanmu ya karisa gaban Yaya ya jafar na bayansa Cikin wani yanayi Kallonta yake yi yana kokuwa da Numfashinsa Allahu akbar ashe ashe mganar da sukayi jiya itace ta bankwanansu Allah ya jikanki Hadiza ya fada acikin ransa kafin ya Dago hannunta da yayi sanyi karau har ya fara sandarewa na dan Lokaci kafin ya saketa Mamanmu ta Dora hannu aka tana fadin"Ta Mutu ko..?mun shiga uku mun Lalace wayyo ni Balaraba..!
Kan Yaya tayo da Sauri Aba ya Riketa yana fadin"Natsu mana Balaraba..Wa ya ce miki ta mutu..?
Cikin dan Daburcewa tace"Bata Mutu ba..?
Kallonta yake da dukkan zuciyarsa yana Faman karanto duk addu"an da tazo bakinsa shima natsuwarsa ke neman kwacemai yasa ya Saketa yana Fadin"Jafar je kazo da Mallam..!
Da haka ya koma jikin Wardrope din Dakin ya jingina kansa yana jin kamar zai fadi Jawaad da ya fara kuka ya isa garesa ya Rumgumesa yana Fadin"Aba kace mama tatashi..!
Sai Sa"idu yaji kamar ya Sulale kasa Ya sume saboda yanayin Dayake ciki rumgume Jawwad yayi kawai yana fadin"Kayi hakuri jawaad..!
Haka kawai yake fadi zuwa Lokacin Kukan Mamanmu ya cika Dakin su hamida ma sun fara ita da Hanne banda Amina da ta kasa Fassara yanayinta ji take kamar ta Bude ido Taga komai ya koma mafarki ne..!
Sai dai ina abunda take gani gaskiya ne domin ba Dadewa sai ga Ya Jafar da Baba Mallam sun sake shigowa Cikin Tsashin hankali Aba na ganinsa yace"Dubata Mallam ta rasu ko..?
Baba Mallam bai Sauraresa ba sai da ya isa kusa da yaya ya kalleta na wani Lokaci ko bakasan mutuwa ba in ka kalli yaya zakasan ta amsa kiran Mahallicinta Cikin Fargaba yake da Tashin hankali Tun zuwan jafar dama ga Damuwar abunda ya faru gabadaya shi kanshi Baba Mallan fata yake yaya bata rasu ba baisan da wani ido zai kalli Sa"idu ya Fadamai Hadiza ta rasu ba..!
Hannunta ya rike na wani Lokaci kafin ya saka kunnensa Saitin zuciyarta na wani Lokaci cikin Sanyin Jiki ya Dago yana kallonta kafin ya Juya yana kallon Aba da kaifaffun idamuwansa da na ya jafar suke kallonsa da su Hamida Mamanmu kuma Sai kuka take rusawa..!
Aba ya kalli Baba Mallam yana Fadin"Ta rasu ko..?Don Allah in ta rasu ka fadamin..Na yarda da Allah ke kashewa kuma shi ke rayawa..!
Baba mallam yayi mamakin Kalaman Aba aransa yaji salama Cikin Dattakomsa yace"Kayi hakuri Sa"idu..Allah yayi ma Hadiza RASUWA..!
yafada Lokaci Daya yana Dafa kafadarsa alamun Lallashi abun mamaki bai ce komai ba illah matsawa da yayi ya shafe idonta sannan ya Dagata ya cire mata Hijabin jikinta ya Lullube kanta dashi Lokaci Daya yana Fadin"Allah ya jikan ki Hadiza..Allah ya kyautata zuwanki...Allah ya Sadaki da Mala"ikun Rahma hakika ke yar aljannah ce Laifin da kika aikatamin da ganga da wanda kika sani da wanda baki sani na yafe miki Duniya da Lahira Allah ya yafe miki kema yasa ki kwanta Cikin kabarinki Cikin Salama ke da kika tafi baki Gaggawa ba..Muma da muke duniyan Jiranta muke Allah yayi miki Rahama Hadiza..!
Chapter 69 · 0% Book details