← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 193

Sashe 37

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fada tana nuna Zafira Wannan karon Hamida ce tace"Daga Gusai take Diyar kanwar Aba ce..! Jidda tace"Goggo Husai..? Hamida tace"A"a Mamata..! Jidda ta gyada kai kafin tace"Allah Sarki naji ma ance goggon na kwance Zazzabi ya Rufeta ko..! Hamida tace"Eh Tun jiya da yammah Shiyasa ma baki ganta tare da su Yaya ba..! Jidda tace"Allah ya sauwake in an wuce da Amaran zan shiga na gaisheta..! Daga haka ta koma cikin,Hanne ta Tabo Amina tana Fadin"Baki ce komai ba..! Amina tace"Yan mganar basa kusa..ai duk cikin ya"yan Amarya ina girmama ya Jidda ba ruwanta..Mara kirkin sai Sa"adatu itama ya Sadiya ba baya ba akwai gulma..! Dariya suka saka Zafira tace"Wai ni ban gane wacce matar Ya Danmallam din ba..! Hanne tace"Anty Sakina..?gatanan mai Less iri Daya dana Anty Sarood..Gajera..! Zafira tace"Naga wata Doguwa Fara kusa da ita..! Hanne tace"Ba ita ba wannan Anty Aliya ce matar abokin Ya Danmallan ne ya Aliyu..! Amina tace"Ke don Allah..?oh na tuna ko wanman abokin nasa mai zuwa gaida su Hajiya wani Dogo baki haka..! Hanne tace"Shifa matarsa ce Dazu suka zo da safe ai kinsa kawar Anty Sakinan ne. ! Amina tace"Ke kam matar abokai..! Dole su zama kawaye kuma Halimsu yazo Daya itama sai kiga tana maka kalloj kashi kashi..! Hamida zatayi mgana kenan sai ga Kanwar Haj.Nasara ta fito mai kiban nan tana Tafe jikinta na rawa waya ce a kunnenta ta fito tana mgana sai Goran Ruwa Dake hannunta. Mai su Amina zasu ba Dariya ba gwara su Hamida suna Rufe bakinsu kada taji ammh Amina Da karfi take Hamida ta Daketa tana Fadin"Dillah Amina kiyi a hankali kada taji..! Amina na Dariya tace"Jar uba kalli Wuyanta..Timama kenan..?Wlh ko Buhun Dawa albarka Markadi..! Daidai sanda Matar ta Juyo tana kallonsu daman tun dazi da suka shigo taga suma mata Dariya yanzu ta fito tama waya tana jin Dariyansu. Tana juyowa suka shanye Dariyansu ta Harari Amina kafin tace"ke wa kike cema buhun dawa..! Amina ta zaro ido ta kasa mgana Tana Danne Dariyanta. Hamida tayi Saurin cewa"Ba Dake muke ba..! Da Sauri Amina tace"Ai buhun dawa.!naga kin ma fi buhuj masara kina..Dankari..! Matar ta Zaro ido kafin tace"ni..? Amina na Dariya tace"Ku kalli Duwawunta asama Hanne..! Matar ta nufosu gadangadan tana Fadin"Kaga min yan isks yara marasa Tarbiya..! Kafin kace me sun Zura a Sittin Amina ce kan gaba sai hanyar waje suka Nufa suna Dariya Ta riga ta saki jikinta Tana kuma Gudu tana waigen su Hanne Dake bayanta sai ji tayi Ta buge Mutum agabanta Da kuma karat Faduwar wani wanda ya bada Sauti Tus...chas..! Baya tayi da Sauri bayanta ya Bugu da Goshin Hanne Dake bayanta Sauran Kadan su Fadi Hamida ta Rikesu tana Fadin"Zaku fadi ba..! Sai alokacin Hamida ta ga wanda Amina taci karo dashi ta kuma Lura da yadda Haraban Gidan ya Cika da maza bayansu ya Jafar har da wasu bakin Fuska ma. Salati ta saka ranta Jikinta ba inda bai Rawa hanne kuwa datagama Fahimta koma baya ta koma tana Kifta ido. Amina kuwa Tsoro ne ya kamata sanda ta Dago ido ta ga Ya Danmallan agabanta Fuskar nan tasa ba Annuri ko Kadan Cikin Shigarsa wacce ta kara Fitomai da kyansa da Zatinsa Lokaci Daya da kwarjinsa. Shikadai ne bata iya Hada ido dashi bazata iya jure kallonsa ba Tunda suka Hado taji gabadaya bakinta ya Mutu gabbanta sun saki ta yi Saurin Sadda kanta kasa tana Bin waayarsa Tadata watse akasa kenan lokacin data ci karo dashi Tayi sanadiyar Faduwar wayar. Kamar wacce aka kai kasa haka ta durkushe ta fara Tattara wayar tana Fadin"Bansani bane..Kayi hakuri..! Su Hanne suka saki baki suna kallonta Hankalan mutanen Dake wajen ya Dawo kamsu har su ya Shamsu sun matso da ya Nazeem kallonta yake tana Tatarra wayar tayi Daidai yace"Amina ce ko..? Wlh Yaya kaci Ubanta yarinyar sam bata da Hankali..! Bata kara mgana ba sai ta Tattaro wayar ta Mike bata yarda ta Kallesa ba ta mika wayar kanta na kasa. Danmallam Cikin Takaici yake kallomta ya kasa karban Wayar wai meyasa yarinyar bata da natsuwa ne..?ji yadda ta kwaso gudu kamar wata ballagaza kamar wata Namiji..? Ganin yaki karba yasa Abokinsa Aliyu Dake Gefensa ya saka Hannu ya karbi Watsatsiyar Wayar yana Fadin"Ba kyau gudu acikin gida..! Yafada yana kallon Amina acikin Ransa yana Tunamin ko kanwar Danmallan ne to bai santa ba. Sai da yayi mgana ne Amina ta Dago suka Hada ido da Aliyu sai alokacin tasan ba Ya Danmallam ya karbi Wayar tasa ba. Gabadaya taji ta muzanta ne ganin da Maza awajen yasa ta Ja kafafunta zata wuce su hanne kuwa suna gefe sun Rakubre kamar wasu marayu. Ba zato kawai taji wani Dogon Hannu mai Laushi ya Riko Duka Kafadunta da karfi ya Dawo da ita gabansa Cikin Mutuwae jiki ta Dago manyan Idanuwanta ta Sauke a nasa da suka Fara Sauya Launi saboda bacin rai. Ya Jafar suna chan nesa suna Hira da wasu abokansu ya su ya Nazeem ne ke kusa ya Nazir kuma yana chan gefe saman manyan Darduman da suka shimfida a Haraban gidan yana kallon meke Faruwa ammh bai maida Hankali ba Chart suke da Hidaya matarsa Tana Fadamai Hayaniya ya Isheta sai yake tambayanta tana ina..?tace tana Bedroom din Hajiya inda ta Sauka shi bai ma tsaya lura da abunda ke Faruwa ba. Kamar mayen karfe haka suka Tsaya suna kallon Juna shi yana mata kallon Haushi da Takaichi ne ita kuma tana kuma ta kasa Sauke idanuwanta ji takr kowani gabobinta suna yin Sanyi kamar yana Hukuntasu duk Rashin kunyata yau sai da aka ga Tsoro a cikin Idonta Lokaci Daya kuma Jikimta ya fara rawa. Ya Shamsu ne ke fadin"Yaya ka bari ni na Chasa su basu jin mgana Daman Abida ta kawo karas jiya Wajen Walima suna ta Satan Takeway kamar baza"a abasu ba kuma Shugabar su Amina ce gatanan batajin mgana ta Raina kowa..! Awannan karim a Saman Labbansa ya Furta"Sata again..? Meke damun yarinyar nan..?tana si ta zama Wata gangarriya..! Sai alokacin ta iya Sadda kanta tana jin kamar kafafunta bazasu iya Daukanta ba. Cikin Muryansa mai Sanyi Da Zaki yace'"Miye kowani abu sai ace ke..?kece Satan nama..?abinci..?rashin kunya Kazanta sannan Main din shinr Rashin Natsuwa..?ke kadai ce agidan..? Ina ce su Hannati age Mate dinki ne..? Why..? Ya fada yana Jijjiga Kafadanta kafin ya Saketa da karfi yana Fadin"Abunda ke Raba Mace da Namiji shine Natsuwa da kamewa..Duk macen da bata da Natsuwa sannan kazama ce ita..Sunanta ba Mace..ba sunanta ballagaza..! Yafada yana jin Bacin Ransa na Sauka da Hannu ya nuna su Hanne yana Fadin"Daga ina kuke..?ina zaku cikin maza awaje..? Hanne kamar tayi kuka tace"Ba..ba ko"ina..! Hannu ya daga ya nuna su dashi yana Fadin"Duk yaran Dake cikin gidan nan ko yara kanana iyayensu basu bar su sun zo suna guje guje ba sai ku..?Ku yara ne..?wato duk iskancin ku da ake Fada akanku gaskiya ne ko..? Hanne ta kwaso Rantsuwa tana Fadib"Wlh Yaya..! Shutup..! Ya katseta da Karfi Cikin Bacin rai yace"In kun raina su Jafar ni sai na Ladabbar daku kafin na koma ku bar ganin bana Duka ima na Fara Dukan yarinya sai na Fasa mata jiki..Comom Ku wuce ko ku koma cikin gida Wlh ko da Wasa na ga Fuskar Daya Daga Cikin bama awaje ba anan Haraban sai na Karya mata kafa Daya..! Ku wuce ku bama Mutane Waje..Wawayai kawai kun girma bakusan kun girma ba..! Ai kafin ya Rufe baki su Hanne sun juya Sumai sumai sun wuce Amina ce kanta na kssa da idon kowa ke kanta ta kasa gaba ballatana baya Sau Biyi kenan ya Taba Tozartata na Farko BacMutane ya Abida ce kadai sai su Hanne yau kuma bayan su Ya Nazeem har da Bakim ido.. ya sake kiranta Barauniya,Sannan yasake ce mata kazama kuma yau harda ballagaza Gabadaya sai taji Ruwan Hawaye sun cika idonta aranta Fadi take"Ni ba barauniya bace..kuma ni ba ballagaza bace..! Ammh ta kasa Furta haka afili Tama kasa wani motsi. Aliyu ne ya Dafasa yana Fadin"Cool Shehi..Bana som Fushin nan naka mara kyau..! Ya Nazeem ne ganin Amina taki tafiya yace"Au ke bazaki wuce bane..? Ya uzairu yace"Duka fa take so ya Nazeem ba"a shiga Jikinta bane..! Mamakin Tsayuwarta yake Cikin Daga Harshensa yace"Bazaki wuce ba..? Yafada kuma yana Daidaita Fushinsa Da Sauri Aliyu yace"Amina wuce ki koma Cikin gida kin ji ko..? Ya fadi sunanta kamar yadda yaji an Fada Bata Dagi ba kamar wacce muryansa ta bata gwarin gwiwa maimakon ta Juya sai ta fara Tafiya kawai da Sauri ya Shamsu yace"Ke ina zaki..? Daman wanda zata Huce akansa take nema wanda yayi mata yafi karfin ta Ja dashi yasa jin muryan Shamsu ta waigo cikin Fada tace"To gida zani..! Tafada Lokaci Daya tana Sakarmai Idanuwanta tana kuma Murdamai baki harda Harara sai kuma Hawaye dukkansu sun gani Shamsu ya Zaburo yana Fadin"Ke ni kike juyama baki..?zan karyaki in na rike ki..! Amina ta Tsaya kyam tana Fadin"gani..Kada kabarni da rai ya shamsu don Allah..! Tafada tana kallonsa da Jajayen Idanuwanta.. Danmallam yakalleta ta fa Daina bashi mamaki Aliyu yace"Kai shamsu kyaleta..baka ga yanayinta ba inajin ba ita kadai bace..! Ya Nazeem yayi Dariya bai ce komai ba Salo Salom iskancin Amina wanne wanne basu gani ba Ya shamsu yace"Wlh lafiyarta Kalau..Duk Salon rashin kunyarta ne Daman bata tsoron kowa ta bari nazo ta ganu..! Ya fada zai nufeta yaji Danmallam ya Dakamai Tsawa yana Fadin"Shamsu kyaleta... Ke bar nan wurin..! Ba musu ta juya bayan ta karajuyama Shamsu baki tana kunkuni ta wuce tana Sharan kwallah Danmallam ya Saki Siririn Tsaki yana Fadin"Kazama kaawai..! Ya Uzairu yace"Yaya da ka bari Shamsu yaci Ubanta..Ko"ina ta Addabi mutane chan ma bata bari Baba Sa"idu ya Huta koda yaushe Fininarta..! Hannu ya Dagamai yana Fadin"Nace ku bar mganar ko..? Dole suka koma suka zazzauna shi kuma sai Sakin Hucu yake Kafadarsa Aliyu ya Dafa yana Fadin"Allah huci Zuciyar Shehi..Ungo wayarka kila sai ta Hau kan Teburim mai gyara..! Karba yayi Lokaci Daya yana ganin yadda Sreen din wayar ya tashi aiki. Karamin Tsaki yaja kafin yace"Yarinyar nan bata jin mgana..kamar ballagaza bata da natsuwa ji asaran da jamim Wayar nan fa sai dai na Sauyata ta gama aiki..! Aliyu yace"Is ok..Kayi Hakuri muna da kudin Siyan
Chapter 37 · 0% Book details