← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 193

Sashe 116

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Atare Hamida Da Hanne suka Hada baki wajen fadin"Shiwa..?
Amina ta kallesu kafun ta ce"Bansani ba..!
Lokaci Daya tana juya musu ido Dariya suka kwashemata da shi Hamida tace"Soyayya ruwan zuma ka sha ka bama masoyi..!
Amina taki cewa komai ta kyalesu suna ta mata iskanci Hanne ta taya Hamida suka gyara ma Amina kayanta suka jera nasu suma da suka zo dashi suka tsinke da labarin makarantar su da Amina sai dai ta tambayi wance da wance sai jin Dadi take yi Amina ta Dauka Aminene ta tafi kenan sai ta gane cewa har yanzu Aminene na nan Rayuwa ce ta sakata tayi sanyi nan da nan kewar makaranta ya kamata Cikin Jin Dadi tace"Ai ranar monday nima zan koma in ji ya Danmallam..!
Hanne tace"Naji yana fadama Hajiya.!
Hamida tace'Yauwa gwara ki Dawo Wlh daga Unity har islamiya ba Dadi baki Amina..!.
Amina tace"Nima bakusan yadda nake kuka in na tunaku bane kamar in yi Tsalle in gani agida..!
Hamida tace"Wlh muma Hajiya take Lallabamu da mallam in sukaga muna kuka ko mun Damu Saboda baki nan..!
Hira ce kawai ta Tsinke kamar bakin su bazai gaji ba Daga Dakin Amina Kitchen sukaje suka Bude Hanne ta Sassaka ma Amina su Samosa da danbun namanta a Fridge kar ya lalace suka kuma jera maltinan aciki Duk da akwai lemuka kala kala aciki Sannan suka Diba samosan Hamida ta soya musu.
Sai alokacin sukaje sukayi sallar mangariba Amina kamar an bata Kujeran Hajji Saboda murna yau gata ga Hanne ga hamida
Bayan sun idar da salla su ka koma Falo sukaci Takeway din nan suka hada da samosa suka kuma sha Tea suka Dora da maltina ransu Fes gashi akwai Wuta basu Dauke ba Amina bata manta da shan mganinta ba bayan sun yi sallar isha"i ta Dauko Zata sha su Hamida suka tambayeta tace tayi Zazzabi ne basu matsa mata ba Tunda daman sunga ta rame kadan sai suka yar da da mganarta..
Afalo suka baje suna Hira Hanne ta kuna kallo gabadaya Tasoshin na wa"azi ne dana addini Ta kashe ta Dawo ta zauna tana fadin"Na manta gidan ustazai ne nan ba"a kallo..!
Hamida ta yi Dariya kafin tace"Ko agidanku ai ba kallon kike ba..!
Amina tace"Gulma da iyayin Hanne mana..ku wai ina Sa"adatu ne..?
Hanne tace"Tana nan mun manta da mun mata mgana mun zo da ita..!
Amina ta Harari Hanne kafin tace"Wlh da kuwa daga ke har ita ba matsiyaciyar da zata shigomin gida..!
Hanne ta Bude baki ita da Hamida kafin su kalli juna su hada baki suna Fadin"Uhm masu gida da miji..ammh nan ana kuka ana ba"a so..!
Ashe dai ana son ya Danmallam din..!.Hanne ta karishe Fada tana Dariya Amina ta karkace baki tace"Allah ya isa Tsakanina daku..Kuma Wlh wuta..!
Suka karisa mata da bal bal..!
Suna Dariya ta tashi tana jefansu da filon Kujera tana fadin"Munafukai kawai..!
Sai da suka gaji suka koma suka zauna Hamida tace"Wato Hanne Halin mutum zanen dutse Amina ko ta Sauya akwai wasu hallayanta da Har Abada bazata sauya su ba..!
Hanne tace"Kamar Taurin kai da Tsiwa da Fada..!
Amina ta kallesu ta harare su batayi mgana ita kanta ta zata ta koma Ruwan sanyi ammh Sanadin zuwansu yasa ta Fahimci Aminene bata Mutu ba Doguwar suma tayi ta Fara Farfadowa yanzu.
Sai kusan goma na Dare suka je suka kwanta achan dim ma wata Hirar suka Dasa tuna irin abubuwan da sukayi suke yi suna Dariya Amina in ta Fara Dariyan mugunta har da Hawaye yau gata ga Hanne da Hamida suna kwance waje Daya Amina ce a Tsakiya Hamida tace"Wai har yanzu baki daina shegen tsoron nan ba..Ke in ba kin kwakwume mutum ba bakya iya barci..?
Hanne tace"Ga ya danmallam sai ta Rika kwantamai abaya in suna barci..!
Amima ta balla musu harara kafin ta juya ta yi Daidai hannunta kan Cikin Hanne kafanta kan kafafun Hamida suna Tureta tana kara Dorawa Dole suka gaji suka kyaleta Daga haka sukayi addu"an barci suka kwanta.
Dayake sun riga sun saba da tashin asuba kiran sallar farko suka tashi suka yi alwala sukayi Raka"atul Fijir sukayi sallah sannan suka koma barci su Hanne an samu waje sai goma na Safe suka tashi suka shiga Kitchen sune har store sai da suka Bude babu abunda babu na kayan abinci kamar ma ba"a Dade da Zuba su.
dankalin Turawa Amina tace su soya da kwai haka kuwa akayi Hamida ta Fere Dankalin ita da Amina Hanne ce mai soya kwai wajen Rabin Kires suka soya yazo yayi musu yawa ga Tea nan suka Ragesa cikin su ya cika Hanne tace"Ko zamu kaima megadi ne..?
Hamida tace"Ke ina ruwanki ga matar gida batace ba..!
Amina data gama shan mganinta ta koma ta kwanta saman Cafet Cikinta ya Cika tace"Uban matar gidan ce Ina ga da wannan gajerar matar yayan Hanne kike mgana itace mai gidan..!
Dariya sukayi kafin Hanne tace"Kema me gidan ce wlh..Gashi Dalilin ki har mun Dankwali arziki ko ba Haka ba Hamida..!
Ta Daga mata kai suna Dariya har da ta tafawa Amina tayi karamin Tsaki kafin tace"Yan iska kawai..!
Sukace sun ji ba bakomai karshenta saman Dining suka maida suka rufe amjima zai musu amfani.
Amina Daganan barci ya kwasheta su koma sai suka tashi Hamida ta gyara Dakin da suka kwana da Kitchen Hanne ta gyara Falo suka goge shi Tas sun nemi burner nasa Turaran wuta basu gani ba sai suka kunna na Tsinke Gidan ya Dau kamshi Sai da suka gama Amina tatashi ganin aikin da sukayi ne yasa tayi mika tana Fadin"Dadina da Kawayena akwai aiki kamar Dawakai..!
Baki suka saki suna kallonta Hamida tce"Zaki ga Dawakai nan da jibi in muka tafi in kika fara yi da kanki..!
Amina tamarairaice kafin tace"wai ku nan da gaske tafiyar zaku yi..?
Hanne tace"Wlh Hajiya tace Ranar Lahadi idi zai zo ya Daukemu..!
Amina tace"Tare dani kenan domin kafar ku kafata..!
Suka Sheke da Dariya kafin Hanne tace"Wa ?ai kin zo kenan yarinya har Abada..!
Hararansu tayi ta tashi ta shige Dakin nan ta gansa tas har da Tiolet Hamida ta wanke shi Tas kwanciya tayi kan gado tana kara jin Dadin ganin su Hanne Tare da ita.
Su kuma basu kwanta ba Wanka sukayi Hanne ta farayi sannan Hamida da suka ma Amina mgana bayan sun Daketa tatashi Tana masifa Hanne tace"Ki tashi kiyi wanka malama sai ki kwanta..!
Amina ta koma ta kwanta tana fadin"Jiya nayi wanka..Wlh ni yau bazan yi ba haba kamar wata
kwado..!
Basu yi mamaki ba Saboda susan Amina bata shiri da wanka Hamida tace"Amina da fa da yanzu ba Daya bane..Ke yanzu matar aure fa kazanta bana ki bane..!
Ko kallonsu batayi ba Hanne tace"Ita ta sani..kishiyoyi dai har Biyu gareki kuma Duka yan gayu ne sannan ya Danmallam bai shiri da kazanta..!
Hamida tace"Kuma bazamu ji Dadi ya raina mana ita ba ko kishiyoyinta su ran mata ba..!
Amina ta Dago kanta kafin tace"Da ku da Kishiyoyin duk naci ubanku na Zauna Lafiya..!
Hamida ta kalli Hanne suka Hada ido suna kunshe Dariyansu tana ganinsu tayi banza dasu daman Hanne da Hamida akwai gulma sun kware wajen munafunci.
Haka Amina ta wuni batayi wanka ba sun gaji da mata mgana sun kyaleta da Rana basu yi girki ba sauran kwan daya rage suka ci suka kuma kara soya samosa suka ci suka hada da maltina da Daddare kuma suka Tarun ma Dambun mana suka ci suka kwanta Washegari Hamida da Hanne Dakyar suka ga Safe suka kwana Murdawan Ciki da Zawo Amina Daman akwai Lafiyan ciki bakomai ke bata mata Ciki ba.
Haka ta Dinga musu Dariya Hamida tace"Hanne Amina wlh muguwace tasan cikinta ita lafiyansa kalau ba sai tace kada mu ci da yawa ba..!
Hanne daman nada ulcer tana Mai da Numfashi tace"Ni sam na manta inda Ulcer ma..!
Amina me zatayi ban Dariya Cikin Dariya tace"Hajiya ni tace ku kawo ma abu ammh Saboda maita ku sai an ci komai daku kadan kuka gani..ma..!
Haka ta wuni yi musu Dariya Ranar ban da Tea basu iya cin komai ba sai da Daddare da suka ji sauki Zawon ya Tsaya da ciwon ciki sannan suka Dafa Doya sukayi miyar kwai suka ci suka kwanta.
Washegari ma barcin su suka sha sai sha Biyu suka tashi suka karya da Sauran Doyan jiya suka gyara gidan Amina na zaune tana kallonsu An samu Amina tayi wanka jiya ammh yau kam tace bazatayi ba ta gaji sudai sukayi suka Sauya kaya Daganan aka Fara Tunanin me za"a Dafa.
Amina tace Hamida tayi musu wainar Fulawar datake yi agida mai Dadi Tunda ga Yajin da Hajiya ta kawo mata .
Nan da nan suka yarda da mganar Amina suka Dunguma zuwa kitchen suna neman Faluwa sun sha mamaki Fulawa buhu Guda ko kwata ba"a taba ba Nan suka Diba suka kwaba suka saka kwai ma"ishi suka yanka albasa Hanne tayi Gireting din kayan miya da suka gani Cikin Freezer harda nama wanda Amina tace soya shi za su yi Hanne tace sai dai Ferfesu basu da lafiyan ciki..Amina na Dariya tace"A soya yafi Dadi..!
Hanne tace"Muguwa muguntarki ta kare miki Amina..!
Sai Dariya Amina ke kyatatawa har tana Hawaye.

********
Chapter 116 · 0% Book details