← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 193

Sashe 78

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amina kuwa sai washegari Hajiya ta ganta saboda sanda ta shigo gabadayansu sun yi barci Ya Abida ce kadai idonta Biyu tana karatu hanne ma ta Dade da yin barci.
Da safe ko gida bata koma ba kayan Hanne ta saka da hijabinta na Hadda Tunda guda Biyu hannen gareta.
Suka tafi Hadda Hamida bata je ba bata da Lafiya ciwon mara Ya zeenatu ke fadama da Amina taga bata ga Hamidan ba..!
Sai da yammah da suka Dawo Amina ta Dawo gida ita Da hanne suka Duba Hamida taji sauki ma,Hanne bata jima ba tayi musu sallama ta wuce gida Mamanmu daman jiran Amina take yi taji ya ake ciki tun Safe Aanty Amarya ta Kirata taji Labari mai Dadi ba wani bayani shiyasa Hanne na Tafiya taja Amina kuryan Dakinta Tana Fadin"Ya kuka yi da Mallam din..?

Amina ta Sadda kanta kasa kafin tace"Mammanmu na kasa..Bazan iya kallon Baba mallam nace bana son jininsa ba..Bai kamata na rama Tarin Alherinsa da sharri ba..Sannan in Aba yaji Wlh sai ya kusa kasheni agidanan..!

Ta karishe kamar tayi kuka ba Domin mamanmu ta kai zuciyarta nesa ba da sai ta kaima Amina Duka yadda Wani Takaicinta ya kamata ammh duk da Haka sai da ta Tureta tana Fadin"To Shikenan tunda kin kasa..sai kije..Sakina ta gasaki don Ubanki..bakuma zaki taba Daraja ba Tunda baya Sonki..Kuma matar Cushe bata Daraja .!

Yadda ta Zageta ta kuma Tureta yasa tasan ranta ya baci da Sauri ta riko Hannayenta tana fadin"Ba haka bane mamanmu..Wlh na kasa ne bazan yi kallon Baba mallam nace mai bana son auran nan ba..!
Mamanmu da kanta har ya fara ciwo Saboda takaici tace"Shikenan na fita Acikin mganar nan..Ba ruwana daman yancinki zan kwatan miki..!
Amina taji kanar tayi kuka kafin tace"To ke kije mana ki fadamai mamanmu..!
Hararanta tayi kafin tace"Saboda ni ce nake son rabuwa da shi ko..?ba inda zani ke kika sani ni sakamar min hannu Ke ji chan ki karata Wlh Amarya da Sakina bazasu barki ki zauna Lafiya ba.!

Amina tace"Tab..Sai dai ni ce bazan bar su zauna Lafiya ba Mamanmu..!
Ta razana gabanta na Fadi tace"Bangane ba..?
Amina tayi dariya kafin tace"To ai ba Tsoronsu nake ji ba..mamanmu ai Amina nake kirarina badai ta Mutum ba sai ta Allah su din banza!
Basu isa suyimin Abunda Allah bai min ba..!
Ta dade tana kallon Amina sai taga kamar Shagube tayi mata shiyasa cikin son tabbatarwa tace"ko kin fara son Danmllan din ne..?
Ta fada cikin Hararanta Amina ta Zaro Ido kafin tace"Ni..?Allah ya kyauta..ni Aminu kadai nake so..!
Ta Karishe Fada cikin wani yanayi Mamanmu ta sauke Numfashi kafin tace"Na Dauka kin fara son shi ne nace Ke kika sani..Domin Danmallam dai ya fara Tsufa auran wuri ne bai yi da kuma Haihuwar da bai samu ba..Kadan ne Aba din ku fa ya Girmesa..

Amina ta zaro idanuwanta suna shekk tace"Kai Mamanmu ko Aba fa bai Tsufa ba ballatana ya Danmllam..!
Mamanmu tace"Eyee..Kina son shi kenan Tunda ke baki ga tsufansa ba..?
Tafada tana Dungure mata kai Amina ta Dafe wajen tana fadin"Allah ya Tsari Amina..wannan ne zan so..Ya taba fa cemin banda natsuwa kuma ni wai kazama ce..!
Ta fada kamar alokacin yake fada mata Takaicin abun na Dawo mata Mamanmu ta kwace hannunta tana Fadin"ni sakeni..Kekika sani..Ba ina neman hanyar kwatan miki yanci ba kina bani kunya ba..Na barki dashi..Kin dai ji kazama yake ce miki Allah kadai yasan kuma wata kalma zai kara Jifanki dashi in ya ganki agidansa an riga an Tusamai ke..!
Amina ta Tura baki kafin tace"Sai na rama wlh..!
Mamanmu ta kalleta cikin Tunanin mafita ko mgana batayi ba ta Tura Kofar Tiolet din Dakinta tana Fadin"An kira sallah..!

Amina fita tayi ranta yadan yi sanyi ganin kamar mamanmu ta Dauki Zafi da Farko ammh Taji Dadi taga Daga baya ta saki ranta ajiyar rai ta sauke Tana jin kaso mafi yawa daga cikin Damuwarta suna yayewa Samun uwa irin Mamannu is a Bleessing..!
Mamanmu kuwa har Aba ya Dawo ta kasa samun wata mafita tana ganin ta bangaran Amina ba nasara Dole zata Jaraba ta bangaran Sa"idu ta Latsa ta gani ko zata ga Jini..!
Shiyasa koda ya dawo tayi wanka ta Shirya cikin riga da zani na Atamfa Hamida ta saka ta gyara Shashen nasa Dazu dataji Saukin jikinta Kayan abincinsa kuma tun kafin ya Dawo akai kai komai ciki.
Sanda ta fito duk suna Tsakar gida kan Tabarma suna Hira an kunna Gen akwai haske shiyasa basu shiga sun kwanta ba..!
Ganin bata ga Jawad ba yasa ta kalli Zeenatu Dake fama da karatu tace"Ina Jawaad..?
Hamida ce tace"Aba na shigowa ya makale masa..!
Mamanmu kamar ta saki Tsaki yaron nan zai zame mata ciwon ido sai ta rabashi da Uban taga ya zai yi shege kawai..!
Mirmishi ta saki kafin tace"Ni ina Dakin Abban ku. Ku kwanta da wuri ke Zeenatu saboda makaranta Gobe..!
Da toh suka amsa mata har ta wuce suka cigaba da Hiransu Amina da Hamida suke ta uban gaddama sai da Zeenatu ta Daka musu Tsawa tace sun dameta.!

Koda ta shiga Shashen Aba ta iskesa zaune shi da Jawaad suna cin Tuwom Shimkafa Miyar shuwakan data Girka Dazu da yammah Saboda Aba din Ranta ya kara baci ganinsa Dare Dare kan cinyar sa yana bashi Tuwon abaki Dakyar ta iya shigowa cikin Dakin tana kokuwa da yanayinta..!
Kan kujera ta zauna Tana fadin"Sannu da zuwa..Ka shigo ina wanka..!
Da yauwa ya amsa mata yana fadin"Haka yaran suka ce..!
Kafin ya cigaba da cin Tuwonsa yana Tambayan ko Jawad ya koshi ya Dagamai kai alamun eh Mamanmu tace"Daman Gulma ce irinta Jawad..Bai dade da gama cin nasa ba .!
Aba yace"Kinsan yaro..Ballatana ko abaya Jawad dani yake cin abinci ko da riga yaci nasa ne..!
Takaici bai barta tayi mgana ba Tana kallonsa har ya gama cin abimcin tatashi ta Dauki Faranti ta Fito dashi Ta mikama Amina tana fadin"Saka shi a Kitchen Amina..!
Da Sauri ta zo ta karba ita kuma ta koma ciki ta ga Jawaad ya gyara zama kan cinyarsa yasa ranta ya kara baci ta kalli Jawad tana Fadin"Jawad tashi kaje dakina ka kwanta..!
Tunda tun bayan rasuwar yay wani Lokacin in ya saka Rigima wajen Aba yake kwana ita kuma bazata iya Daukan wannan ba ta gama da Uwarsa kuma shi yazo ya rika sakata Damuwa ba..!
Aikuwa make Kafada yayi alamun bazai je ba Aba ya kalleta yana Fadin"Kyalesa in yayi barci sai ki kaisa..!
Takaici bai kara sa tayi mgana ba ta koma kan Daya daga cikin kujerun falon ta lafe ta maida hankalinta kan Tibin Dake falon cikin tashan Larabawa tana ji Aba ya maida hankalinsa kan jawaad yana Biyamai karatun da sukayi yau a makaranta Tun tana jinsu tana Gumduma ma Jawaad zaki aranta har ta fara barci Sama sama taji Aba na Kiran sunanta ta Bude ido tana kallonsa cikin Mamaki yace"wai har kin yi barci..?
Har jawad yayi barci na mika shi wajen Zeenatu nace yayi Fitsari kafin ya kwanta..!
Mikewa zaune tayi Dakyau tana sosa idonta kafin tace"bansan sanda barcin ya kwasheni bane..!
Kai ya gyada kafin ya wuce ciki yana Fadin"Bari nayi wanka..!
Da toh ta Bisa kafin tatashi tabi bayansa Yana shiga wankan ta Fitomai da jallabiya da gajeran wando ta koma ta zauna tana jiran fitowarsa Daya fito ya ganta sai da yayi mamaki cikin mamakin yace"Baki kwanta ba..?
Kai Tsaye tace"Eh ina son mgana Dakai ne..!
Bai damu ba yace"Bari nayi shafa"i da wuturi ke kin yi ko.?
Da sauri tace"Eh saboda bata so yace sai tayi alhalin ba Damunta yayi ba Khamsul salatin ma dole take yinsu.
Sai da ya saka Jallabiyan ya Shimfida Darduma ya tada salla har ya idar tana zaune ganin haka yasa bai Tsawaita addu"a ba ya juyo yana kallonta kafin yace"Ina Sauraranki..!
Gyara zama tayi tana Tattaro Jarumta da wani Kalan Tsausayi tace"Abban Jawad daman kam mganar Amina ce..!
Cikin dan Fargaba yace"Amina..?me Aminan ta sake yi kuma..?
Da sauri tace"Kwantar da Hankalinka batayi komai ba..Kawai ni ke son mgana Dakai kam Auran da mallam ya hada Tsakaninta da Danmallam na wajem Hajiya..!
Kallonta yake yi ko Kiftawa bai yi ba cikin mamakinta yace"Ina jinki..Sai me ya faru kuma..?
Mamanmu ta gyara zama tana Fadin"Tsakani ga Allah Abbansu baka ganin an kwari yarinyar nan..?
Cikin kosawa yace"Ina jinki..jeki kai Tsaye kan mganarki..!
Mamanmu bata Lura da yanayin kallonta da yake yi ba ta cigaba da Fadin"To gani nayi shi ba sa"anta ba In fa aka duba ya kusa haihuwanta in da auran kauye yayi..Ina Amina zata kai shi..?Sannan ga tarin Kishiyoyi har Biyu Abbansu a shekarun Amina batasan Dubarun zama da Kishiya ba,Shiyasa naga bari nayi maka mgana gaskiya aduba wannan al"amarin..!

Kallonta yake yi yana kokuwa da bacin Ransa kafin cikin Kaushin Murya yace"Ita Aminar ne tace miki bata son Dubarun zama da kishiyoyi ba..?To don Ubanta agidan nan Tsakanin mata Biyu ta taso..Gidan Baba Mallam kuma Hudu garesa reras gayamin wani karatu ne ya Ragemata bayan na wadannan gidajen..?
Sai mamanmu ta Daburce cikin Inda inda ta fara fadin"Ai kasan yarinya ce..Allah na Tuba ko hamida girman jiki ne..Ammh sai wannan shekaran ne suka shiga sha shida fa..Ina zata kai Umar..?
Akwai zalunci gaskiya..!
Kai Tsaye yace"Naji an zalunceta..Yanzu me kike so ayi..!?

Ta zata ya yarda da mganarta ne yasa Cikin Fara"a tace"Yauwa..Mallam kawai zaka je ka fadamawa baka son wannan Hadin na tabbata zai saka Danmallam ya saketa..!

"KE BALARABA..!

Aba ya Daka mata Tsawa da sai da ta Tsorata cikin Bacin rai mai Tsanani yace"Ita Aminar ne ta aiko ki kizo ki Fadamin naje na samu Mallam na Fadamai bata son auran Umar..?Tana so ya saketa..?
Mamanmu Sai taji ta kasa mgana Mikewa yayi cikim bacin rai yana Fadin"Dake nake mgana..!
Cikin kwantar da Murya tace"ba yadda ka Dauka bane..Wlh basu dac..!

"daman waya ce sun dace..!
Chapter 78 · 0% Book details