← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 175 OF 193

Sashe 175

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uzairu na jin haka ya mike yana Bin Hajiya Uwa da wani kallo kallon Tsana da Bakinciki kafin ya juya zai bi bayan Nazeem daya fara tafiya zai bar Falon da Sauri Hajiya uwa ta kira sunayensu suka tsaya batare da sun juyo ba. Haj.Uwa ta rarrafa zuwa inda suke Tsaye Cikin kuka take fadin"Meyasa zaku juyamin baya. ? Kada ku manta duk abunda na aikata Saboda ku ne..Wlh duk abunda na aikata Saboda ku ne..! Kuyi hakuri ku yafemin Don Allah..! Sai kuka har tana Dukewa saboda kuka,Nazeem ne ya juyo a fusace yana Fadin"kada ki kara jingina Zunuban ki da sunanmu..Tunda nake dake ban taba Fada miki ina son zama a Karkashin Baba mallam ba..Ko Uzairu ma nasan ba Ra"ayinsa bane Meyasa kafin ki fada wannan Halin baki zauna Damu kin tambayi Ra"ayin mu ba..? Me kika nema kika rasa..? Me Hajiya ta rage ki dashi ita da ya"yanta..? Me Baba mallam ya rage ki dashi..? Wlh Tallahi ban taba jin kunyar Hajiya da mallam ba sai yau mugin Halinki yasa na kasa Hada ido da yan"uwana..! Ya karishe fada yana Sharan hawaye Uzairu ma haka cikin Hawaye yace"Mommy meyasa kika Zabi wannan Rayuwar..? Baki taba Tunanin Sharri dan aike bane..?.inda ka aikasa nan ko min Daren Dadewa zai dawo maka..? Wlh ko Kaffara bazan yi ba Shiyasa kanwar mu Umaima take cikin wannan Jarabawar saboda irin abubuwan da kika aikata ne ta ke Fuskata..!mommy kun Cutar damu Kin sakamu jin kunyar Mallam da Sauran yan"uwanmu..Nasan Ya Nazeem bai Fada miki ya samu aiki da wani kamfani a Lagos ba,Sannan ni kuma ,masters dina zan koma bamu da burin komai sai muyi karatu mu nemi na kanmu Muma watarana mu taimakama iyayanmu da abunda muka Tara na Halaliyarmu..! Ya karishe fada Kamar zai Saki gunjin kuka kawai sai ya juya ya fice Nazeem ya mara mai baya Haj.Uwa ta bisu da Kuran sunanyensu ko waiwayo ba wanda yayi..nan ta durkushe tana wani irin kuka mai sosa rai Shamsu na Zaune ya mike shima cikin wani yanayi yazo gabanta ya tsaya sai ji kawai tayi ya Kira sunanta da Sauri ta Dago sai dai ganin kallonta Dayake Binta dashi yasa jikinta yayi sanyi. Kallon tsana da Bakikciki yake Binta dashi da tir da ita bisa yadda ta Aikata wannan abun kunya. Juyawa yayi kamar sauran zai fita Ta saka Hannu ta rike kafarsa ya juyo ya Fizge Kafarsa ya fice da Sauri yana Sharan kwallah Haj.Uwa ta Dora hannu akanta tana Fadin"Na shiga uku na Lalace..! Kaico na..Kai co na..! Wajen Nazifa ta nufa itama kawai sai ta kauda kanta tana kuka Haj.Uwani ta riko hannunta tana fadin"kema gujemin zaki yi nazifa..! Kada ku manta ni mahaifiyarku ce..! Duk abunda nayi yau saboda ku ..! Bata gama mgana ba Nazifa ta kwace Hannunta tana kuka Cikin kukan take Fadin"Ki daina kokarin dora mana Girman zunuban ki..Kin sakamu jin kunya Mommy..Nayi nadamar kasancewarki mahaifiyarmu ayau..Kin cucemu kin bar mana Tabon da har abada bazamu taba mantawa ba..! Tana gama fadin haka ta mike da gudu itama tabi bayan yan"uwanta tana gunjin kuka suka bar Hajiya tana wani irin kuka,kukan nadama da nasani mara amfani. Ita da Anty Amarya da Mamammu wanda ko Tsausayi basu bama kowa afalon ba. Baba mallam sai da ya Dauke kwallah a kwarmin idanuwansa kafin yayi gyaran murya yana fadin"Duk Sboda Dukiya ce yasa kuka kai kan ku ga Halaka..? Shirka acikin gidana da zuru"ata..! Allah ya tsaremana imaninmu..! Bayaso ya cigaba da mgana Rauninsa ya bayyana yasa ya Dakata,irin su Goggo Husai ne da su yakaka suka iya amsa da Ameen ko Hajiya kanta na kasa tana sharan hawaye. Mallam ya cigaba da fadin"Kun Saka ido kan Dukiyar da baku san Wahalar da Sa"idu ya sha wajen tarata ba..Rana iska damina yana Tsaye da Amana kan Dukiyata..Dai dai da Rana Daya bai taba gazawa ba..Sai yau rana Daya komai Dayake faruwa saboda ita ce..? Daman an ce Dukiya da mata sune abun shagala anan duniya..to bari in sanar daku abunda baku sani ba ko nace wasu basu sani ba..Gabadaya Dukiyata Rabinta mallakin Sa"idu ne..Rabi ne nawa shekaru kusan uku da suka gabata ribar da muke samu da nashi aciki..Na saka Lauyoyi sun yi Rubutu ko yau na Fadi na mutu Rabin Dukiyata na Sa'idu ne ya Chanchanta ya kuma Dace domin yafi wahala da ita Fiye dani dana mallaketa..! Ya karishe mganar cikin wani yanayi,Sai kallo ya koma wajen Baba mallam,Kar Baba Sa"idu da Ya"yansa su ji labari cikin mamakin jin kalaman Baba mallam.. Baba Sa"idu dake jikin Jafar ya Dago Cikin Rauni yana Fadin"Baba mallam ammh...! Hannu kawai ya Daga masa yana Fadin"Basai kace komai ba..Wannan ba mgana bace..Tuni an tabbatar dashi Tuntuni takardun komai yana nan a Rubuce..Sa"idu kai D'a na ne..Har yau gobe kana nan a matsayin Babba yaro na..Kafin na same su kai na Fara samu har gaban Abada bazan manta da karamcin Mahaifinka gareni ba..Kafin na Fara sanin kowa Ku na fara sani kai da Hajiya..Dole ku zama wani jigo nawa abunda baku sani bane ba boka ko mallam ba..nan Duniya ba wacce zata kai matsayim Hajiya a wajena..Hajiya ta zauna dani Tun ina amsa sunana Yunusa ban tara komai ba kuma ban da komai ban isa komai ba,ban kai ko'ina ba sannan ba wanda ya sanni..Itace ta wahala dani ta Zauna dani tun ina malamin zaure ta jure yawon gari gari da nake yi domin Da"awa sannan ta jure abubuwa da yawa akaina,Itace ta Fahimceni Fiye da kowa acikin ku..Sannan duk abunda na kawo mata Zata karbesa hannun Biyu bazata taba korafi ba,dukkan ku da na aure ku Hajiya bata taba Daga Bakinta akan hakan ba..Ban taba kawo mgana ta tsallaketa ba yadda ta Daukeni Allah ne kadai ya sani..Bayan ita sai Sa"idu Shima yazo ya wahala dani, wahalan da ko ya"yana basu yi dani ba..Har gaban Abada Hajiya da Sa"idu matsayin su bazai sauya a wajena ba..! Duk Kokarin mai kokari bai isa ya Ture abunda Allah ya kafa ba..Shiyasa duk kan sharrin ku ya koma kanku..Allah ya gani ban taba cutar daku ba..Ammh tunda kuka Zabi ku cutar damu bazamu ce komai ba..Sai dai zamu bar ku da Allah mai Fitowar rana da Faduwar ta,Kamar yadda ya Fallasaku yau..Sannu sannu zaku amshi Sakamakon a Hannunku..! Ya karishe Fada yana kauda kai Daga kallon Anty Amarya da mamammu Dake kuka kamar ransu zai fita. Gogggo Husai tace"Hakkin rai bazai barsu ba mallam..! Mallam yace"Tsakanin su da Allah ne wannan Husai..Basu isa su kashe rai ba..Saboda basu ke Kashewa su raya ba..Duka na Allah ne..Allah daman ya Rubuta Lokacin Hadiza yayi..Ko ba Sanadi zata rasu a wannan ranar..Allah ya rubuta Hakan Wa"adinta ya kare..Ammh sune Sanadin hakan Cutar da sukayi ma Sa"idu da ya"yansa kadai aka bar Balaraba da Marliya sai ya hanasu zaman Lafiya a Duniya..! Goggo Husai tace"Allah ya isarmu..Allah ya sakama Sa"idu..! Take fada tana kuka Yakaka na gefe tana jinjina kai mamaki duk ya cikata wannan aikin duk agidan malami kamar Mallam yunus..! Tsoron Allah ya kara kamata da tsoron rayuwa. ! Amina ko na jikin Danmallam tana Shesshekan kuka shi kuma yana ta lallashinta su ya jadwa na gaban Aba suna ta gunjin kuka. Mamannu ganin Aba ya juya baya su Jadwa ma sun juya mata baya suna kuka sai ta rarrafa wajen Zulfa kafin ta kariso ta mike ta isa gaban Aba ta Zauna tana kuka Daya bayan Daya suka koma wajen Aba da yan"uwansu suka zauna suna kuka suna Binta da kallon kyama..hamida ce ta mike tana wani irin kuka kallon Mamanmu take Idanuwanta sun juye. Mamammu ta rarrafa gabanta ta rike Kafafunta tana fadin"Hamida kema kada ki gujeni..Wlh sharrin shedan ne da Sharrin so..! Hamida ta yi wani mirmishi kafin ta Saki Dariya kamar mahaukaciya. Cikin Dariyan take kallon mamammu cikin wata murya tace"Tunda kike aikata wannan Muguntar naki baki Tunawa damu ya"yan ki ba..? Baki Taba Tunanin watarana abunda kika aikata zai taba mu ba..? BALARABA KO NACE DAYYABA..ki sani Duk abunda kika aikata kanki zai Dawo..Ba yaya kika kashe ba kanki kika kashe ba Amina kika lalata ma Rayuwa ba ya"yanki kika lalata ma Rayuwa Kika gurbatamu kika Wulakantamu..Duk abunda kika aikata tare damu ya"yanki zamu girbeshi..! Ta karishe fada cikin Kuka lokaci Daya da dariya kamar wata Mahaukaciya kowa sai ya koma kallonta cikin mamaki da Tunanin me ya Sameta .!? Mamanmu ta fara kokarin mikewa ta Rumgume Hamida cikin Fitan Hayyaci ta tureta Sai ta fadi kasa cikin muryan kuka tace"Kada ki kara tabani..baki sanni ba..Ban sanki ba..Tsakaninmu Dake sai Allah ya isa..Bazamu taba yafe miki ba kin cutar damu kin Cutar da kanki.Da izinin Lahi sai kin lalace sai Allah ya wulakantaki..Sai Allah ya Dai'daita Rayuwarki sai Allah ya tsarwatsaki BALARABA..! ta karishe fada cikin wani yanayin da sai da ta bama kowa Tsausayi Amina ta Baro Jikin Danmallan Tsausayin Hamida ya kamata kafin ta karisa wajenta Hanne ta isa ta rumgumeta tana kuka tana fadin"Hamida ki daina Fadin haka don Allah ki daina. ! Hamida na gunjin kuka take fadin"Ya zan yi Hanne..? Ina jin zuciyata kamar zata fashe..Kamar zan yi hauka.! Muryan Amina taji a bayanta tana Fadin"Ki rika maimaita innalillahi wa"inna ilaihirraju"un acikin ranki zaki samu Sauki..! Hamida ta saki Hanne ta karisa gaban Amina tana Fadin"Innalillahi wa"inna ilaihirraju"un Amina da wane ido zan kalle ki ina jin kunyarki..? Take Fada tana kama kanta sai tayi suu kamar zata fadi Amina da Hanne sukayi saurin tarota ta fada jikinsu haka suka kankame juna su uku suna ta kuka kamar ransu zai fita. Kowa afalon sai da ya Tsausayamusu suna yi su ya zulaihat nayi bamai lallashin wani. Mallam ne ya mike yana kallon Hajiya yace"ki Rarrashi yaran nan Hajiya..kukan ya isa haka..Allah ya Tsaremu..! Ta amsa da Ameen Idanuwanta sun kada kafin tace"Cikin wannan halin da suke ciki za"ayi Daurin auran..? Mallam ya gyada kai yana Fadin"Insha Allahu ba fashi..! Ba wanda ya kara mgana Baba mallam yana gyara Rawaninsa yace"Sa"idu tashi muje shashena..Tashi ga Kafafunka da izinin Lahi bazasu taba ganin gazawarka ba..Allah ya Dauke Hadiza ni kuma nayi alkawarin Zan aura maka wacce ta fi Hadiza komai da komai kamar yadda na aura maka ita da farko..! Aba ya mike da taimakon Jafar yana kokarin Daidaita yanayin sa yace"Nagode mallam..Allah ya
Chapter 175 · 0% Book details