← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 193

Sashe 57

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mgana Har Lokacin Yaya Dukan Amina take yi Cikin Tashin hankali ya karisa gabanta batasusan da shigowarsa ba mganarsa kadai sukaji Daga sama "Kada ki Sake Dukanta HADIZA...! Ya fada Cikin Kaushinsa kamar koda yaushe,Cak yaya ta Tsaya sai Lokacin Aba ya gansa Mamanmu na gefe tana kuka tana ganin Baba Mallam tace"Yauwa gwara da Allah ya kawo ka..Mallam kalli Dukan da suka ma Amina..? Kashemin ita zasu yi.? Aminar Baba mallam ya kallah Goshi na zubar jini baki ma haks gabadaya bakin ya sumtuma sun sauya mata kammami Tama Daina kuka sai Hadiyar rai kawai Daidai shigowar Hajiya Babba cikin tashin Hankali ganin yanayinsu yasa tace"Wai ke faruwa ne..? Sa"idu..? Ba wanda ya iya mata mgana Sai Lokacin Mamanmu ta iya mikewa Dafe da kugunta Baba mallam ya kalleta Sau Daya ya kauda kai Hajiya Babba ya kallah yana Fadin"Hajiya kama Amina..bari na kira Idi yakai ku Asibiti mafi kusa a dubata tana Zubar da jini..! Sai Lokacim Hajiya Babba ta Lura da Amina da sauri ta karisa ta Dagota tana Fadin"Innalillahi waye yayi mata wannan Dukan..? Zaku kasheta ne..? Amina kuwa ganin Hajiya yasa ta fashe da kuka tana Fadin"Hajiya ki fadama Aba da yaya..Wlh bana bin maza..Ki kuma fadamai ba Ruwam mamanmu don Allah ya janye Sakin da yayi mata..! Hajiya ta ji ta shiga Tashin Hankali Cikin wani yanayi tace"Innalillahi Wani"inna Ilaihirraju"un..! Baba mallam bai saurari kowa ba ya Fiddo wayarsa ya Kira Idi Direba daman gidansa ba nisa yace mai ya Fito akwai Fitar da gaggawa yana Gama wayar ya juyo yana Fadin"Hajiya kuje har da Balaraba itama adubata! Hajiya ta kalli Mamanmu yadda ta kasa Tsayuwa tana Fadin"Mun shige su ni Zainabu..Wai me yake faruwa ne..? Baba Mallam bai mata mgana ba Aba ya kallah wanda kansa ke kasa yace"Biyo ni Daki na..Ku kuma kuje Daga waje..Yanzu Idin zai iso..! Daga haka ya saka kai ya Fice Aba yabi bayansa Falon Aba suka isa Baba Mallam ya fara shiga Aba yabi bayansa su kuma Hajiya ta kama Amina tana kuka jini agoshi da baki Hamida ta kallah Dake gunjin kuka tace"Miko mata Hijabi Hamida..! Da sauri ta rarumo nata ta mika ma Hajiya ta saka mata Yaya kuma Ficewa Tayi Daga Dakin cikij yanayin da ba wanda ya gane. Hajiya ta kalli Mamanmu Tana Fadin"balaraba sako mayafinki muje..Allah yayi mana mganin wamman masifar data kunno mana kai da Daddaran nan! Zeenatu taje ta dauko ma Mamanmu Hijabi ta saka ta riketa Saboda Dakyar take iya takawa suka fita Kofar gida Har idi ya iso har ya fito da Mota suka shiga Hajiya da Amina da Mamanmu da Zeenati Hamida kuma Hajiya tace ta koma gida Wani karamin asibitin kudi Hajiya tace Idi ya kaisu Saboda kada su bata Lokaci. Achan Falon Aba kuwa suna shiga ko Zama Baba Mallam bai yi ba ya Juyo yama kallon Aba cikin wani yanayin Bacin rai Aba kansa ya maida kasa Domin in yana gaban Baba mallam baya iya Daga kansa saboda Biyayyah..! Shuru na wani Lokaci yaji Baba Mallam bai ce komai shiyasa ya Dago kansa a hankali kafin ya bude baki zai yi mgana Baba Mallam ya Daga mai hannu Cikin Dattakonsa yace"Bana son jin komai yanzu..Kafin na tambayeka me ya faru..Ka maida Balaraba Dakinta in har kana so na Saurareka..! Aba ya Dago kansa cikin wani yanayi yace"Baba m...! "Bana son jin komai kayi abunda nace in har na isa Dakai..! Dole yasa Aba yace"Shikenan..Na maidata Dakinta na Janye Sakin Dake Tsakanina da Balaraba..! Sai alokacin Baba Mallam ya sauke Nunfashi ya samu kujera ya zauna yanuna Aba gefensa shima ya zauna kafin yace"Ina jinki...Fadamin abunda ya faru tundaga farko..! Nan Aba ya Sunkuyar dakai ya Sanar da Baba Mallan komai ya karishe da Fadin"Abu daya yafi min ciwo..Meyasa Balaraba ta Boyemun..! Sannan da Taimakonta ta Lalatamin Tarbiyar Amina Mallam..Na tabbata da saninta..! Kallonsa kawai yake ya Dade bai yi mgana ba sai chan nisa ya fara mgana cikin Kaushinsa kamar ko yaushe"Sa"idu kaifa mai ilmi ne..To ina Ilimin ka yake..? Me Annabi yace..? Kada muyi Fushi..Kuma mu daina Saurin yanke hukunci cikin Fushi..Meyasa da haka ta faru baka bari kayi bincike ba kafin ka yanke hukunci ba..Kana da Tabbacin ita Balarabar ta sani..? Baka sani ba..Kun taru kai da Hadiza kuna neman kuyi kisan kai..? Yamzu inda wani abu ya faru mara Dadi wa gari ya waya Sa"idu.? Kan Aba na kasa yace"Kayi hakuri Baba Mallam! Mirmishi yayi kafin yace"Akoda yaushe ina Fada maka Duka baya Tausasa yaro..Sai ma ya kara karangarar dashi Nasiha da Lallashi je mafita Sa"idu ban ji dadi ba..Kana aibata yarka ina ji ajikina Ba aikata barna Lokacin kuruciyarmu ba..Muma Daga cikin ya"yanmu ba Zamu samu bara Gurbi ba Sa"idu...! Aba ya dago yana Fadin"Yaron da take waya dashi fa Mallam..? Ansan meke Tsakaninsu..? Baba Mallan yace"Komai menene alheri ne Sa"idu..Baka haikema ya"yan wasu ba kaima da yardan Allah bamai haikema ya"yanka da yardan Allah..Wannan ai ba wani abu bane Komai zai daidaita Zan yi mgana da Amina yaron da suke wayar zan nemesa naji abunda ke Tsakaminsu in Yana sonta da Gsske ni zan ce ya Fito in nayi bincike na gari zan bashi Auran Amina Kamar yadda na Saba..! Aba ya saki baki yana kallon Baba Mallam bai samu zarafin mgana ba yaji yace"Kiramin Hadiza..Itama na nuna mata ta Daina yanke hukunci Cikin Fushi..Sannan ku daina aibata ya"yanku Dafi ne garesu..! Ba Musu ya mike ya fice koda yaje ya isketa tana ta kuka,Ya kalleta Cikin wani yanayi kafin yace"Kizo Falo na Baba Mallam na mgana..! Da haka ya fice share Hawayenta tayi ta saka Hijabi ta shiga Falon ta samu Baba Mallam yayi mata nasiha sosai da jikinta yayi sanyi Cikin wani Rauni Yaya tace"Mallam Amina ta fitta zakka..Tayi Sanadiyar da saki ya shiga Tsakanin Mahaifinta da matar da ta Zamemata komai a rayuwa..! Mallam ba Amina ce agabana ba Kuka nake Saboda Alherin Balaraba ya koma Sharrin awajem Sa"idu..! Baba Mallam yace"Wannan ya wuce Hadiza...Sa"idu ya maidata Dakinta Yanzu nan..Mganar Amina kuma ba Ruwanka zan yi mgama da ita..,! Dukkansu basu kara mgama ba Domin Duk Abunda Baba Mallam yace daidai ne Yaya hankalinta ya kwanta Dataji cewa Aba ya maida Mamanmu sai alokacin taji Hamkalinta ya kwanta. Hajiya ce ta Kira Baba mallam awaya sukayi mgama basu ji me tace ba cewa kawai yayi sai sun dawo..! Suna mgana ya kallesu yana Fadin"komai lafiya..Amina goshinta ne ya fashe anyi Dinki sai Balaraba data Bugu kadan..suna hanyar Dawowa..! Kai suka gyada gabadayansu Baba mallam ya cigaba da musu nasiha yana Nuna musu illaj yanke hukunci Cikin fushi da aibata ya"ya da kalamai marasa Dadi sunan nan sai gasu Hajiya sun Dawo falon Aba suka shigo Gabadayansu Hamida ta Tsaya Daga wajen Daman tunda suka tafi ta ke kuka Tasani Amina tana da Judali sai dai bata taba Tsammanin Jidalin Amina yakai har ya huce yadda take tsammani ba Amina da pasta a goshinta bakinta kuma wankeshi akayi ya Kumbura mamanmu kuma mgani aka bata baba Mallam ya kalli Amina Dake Nanike da Mamamanmu kafin yace"Hajiya ki tafi da Amina ta zauna awajenki har ta samu sauki..Ke kuma Balaraba kiyi hakuri kin ji.. Sa"idu ya maidake Dakimki Don Alllah ina so har Abada bayan mu anan kada wani yaji wannam mganar..! Mamanmu tace"Insha Allahu mallam..Bakomai..! Baba Mallam yaji Dadi yana ta saka albarka kafin ya Mike shi da Hajiya wacce ta Riko Amina da hannunta ke cikin na Mamanmu kanta ta Dafa tana Fadin"Kada ki damu Har Abada ina nan a matsayin Mamanki Diyata.! Gobe zan shigo na Dubaki zan zo miki da kayanki..! Kai ta daga mata Zuciyarta ta Sauka Tunda Aba ya janye sakin da yayi mata radadin Dake ranta ya Sauka haka suka fito har kofar gida suka rakasu dukkansu Hamida ta rike ma Amina hannu sai haawaye Amina ta Rike Hamida tana Fadin"kuyi hakuri Hamida ku yafemin..! Hamida ta saka mgana har Hajiya taja Amina suka tafi wannan wani irin almari ne..? Bata fatan kara ganin mai kama da wannan Ranar. Achan gidan Baba Mallam kuwa Su Hanne duk sun yi barci Dakinta Hajiya takai Amina ta saka mata Ruwa mai zafi tace ta shiga tayi wanka ta gasa jikinta ita kuma ta Fice Shashen Mallam shi yake karanta mata abunda ya faru bataji Dadi ba ammh Tunda Mallam yace zai yi mgana da Amina shikenan komai zai Daidaita. Bata jima ba ta Dawo shashenta,Saboda Hajiya nasara tazo wajen Mallam koda ta koma Amina tayi barci Dayake an mata allura a asibitin Tsausayinta Hajiya taji wata Kaddaran bamu ke Dorama kammu ba Allah ne..! Hajiya shimfida tayi akasa ta kwamta ta bar Amina akan gadon sai Washegari ne su Hanne su ka ganta Shima Hajiya ce tace su shiga su Duba Amina bata da lafiya kafin su tafi makaranta Allah yasa ma suna Revesion ne su Amina su kuma su ya Abida suna Mock ne. Da suka Tambayi me ya sameta sai Hajiya tace Zamewa tayi a bandaki Hanne tafi shiga Damuwa da Halin da Amina ke ciki,Sannan kuma Amina ta Riketa tana Fadin"Keda Hamida nayi muku laifi ku yafemin Hanne..! Bata iya gane komai ba,Sai da Suka je makaramta suka hadu da Hamida ta Fadamata komai Hanne ta shiga Tashun hankali Fadi take"Take kin ji ko.Hamida..? Amina ta Debo jidalin Dayafi karfinta..! Hamida tace"So nake ta kara jin Sauki..Sai mu turketa ta Fadamama yaushe ta fara aikata abu bata sanar damu ba..! Hanne tace"Tabbas..! Da haka suka bar mganar sun fada a makaramta Amina bazata samu zuwa ba da aka shiga Har hamida gidan Baba mallam suka shiga ta Duba Amina har da su Sa"adatu da yake an Fada Aminar bata lafiya da ya Shamsu yaga bai ganta ba Hamida ta Fada acikin mota sanda Idi ya Daukesu Taji sauki sai dai Kumburin bakin kadan shima ya Sauka goshin ma yayi Sauki Mamanmu ma ta warware ta shigo har Fatan wake da Hanta tayo ma Amina Hajiya na mata tsiyan cewa ko ta mata kara ta bar mata Amina sai ta Biyota Mamanmu na Dariya tace"To karan me Hajiya..? Zan iya kara akomai banda Abunda ya shafi Amina..! Nan suka yi ta raha da Hajiya Amina taji Dadin ganin mamanmu ta Rumgumeta tana fadin"Mamanmu ki yafemin..! Mamanmu ta shafa kanta tana Fadin"Kada
Chapter 57 · 0% Book details