← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 193

Sashe 63

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Gabadayansu Dariya sukayi Saboda yanayin yadda sukayi mganar Aba ma sai da ya Murmusa bai ce komai ba yana kallon Yaya basu sani bane aduniya ita kadai ce macen da yake Fatan Har aljannah ta zama matarsa Saboda kyawawan Hallayarta Tunda suka zama miji da mata shekaru aruaru bai taba ganin Ranar data Daga Muryansa sama da tashi ba..Yana kokarin Boyewa ne Sai Hadiza matsayinta Daga Allah ne ko ya Boye Kaunarta bazai taba Boyuwa ba Tana da wani irin girma acikim Idonsa da Rayuwarsa da ba wanda ya sani ita yake kallo yana jin zuciyarsa na Sauka Duk da cikin Halin Dayake ciki ita kuma kanta na kasa tana da kunya ballatana gaban Hajiya da Baba Mallam..!
Yaci kuma Ferfesun duka ya Cinye ya Dora da kayan marmari sai gashi garas dashi sai dai kallo Daya zakayimai kasan yana cikin Damuwa,Ya Jafar daman bai shigo ba sai gasu shi da Nasir sun shigo suka kara gaida Aba daganan su Mamanmu sukayi sallama dasu Jafar zai maidasu Gabda zasu fita Hajiya ta dawo wajen Baba Mallam daya mikama Jafar takwaransa yana jadaddamai yazo zai bashi wani mgani Jafar din ya Juya kenan Hajiya ta kalli Baba Mallam tana Fadin"Mallam naji bakace komai ba Har yanzu..?
Kallonta yayi yana Mirmishi kafin yace"Nazir ya Kirani da Safan nan yace yana ta kiran wayarki baki Dauka ba..Sai daga baya Abida ta Daga kiran tace baki nan kina gidam Sa"idun..!
Kauda mganar yayi ta sani tace"Ina na sani..Gida na bar wayar..Suna Lafiya ko..?
Yace"Lafiya lau..Shehin ne dai ba Lafiya yacemin kwanansu Biyu asibiti Ciwon ciki ammh sun dawo gida shine nake fadamai nima ina asibiti ga yayansu Sa"idu ba Lafiya..!
Hajiya tace"Assh..Allah ya Sauwake in na koma na natsu zam kirasa..!
Kai ya gyada mata bai ce komai ba,sai ta kalli Aba da hankalinsa baya kansu ya Lula Tunanin Halin da Amina ta Jefasa Cikin Damuwa Hajiya tace"Sa"aidu wannan Tunanin babu Riba cikinta..Ka kwantar da Hankalinka ba wata mtsala insha Allahu..!
Aba ya sauke Numfashi kafim yace"Hajiya in ban aurar da Amina yanzu ba..Watarana Jidalinta zai iya ajalina..Kinga Hadiza bata mgana ko..?
Na rantse tafini jin Dacin Amina tafini Sanin Ciwonta Domin itace uwa gareta ina Tsoron yadda take shanye abubuwa watarana Amina ta Dauko abunda zai yi sanadiyar zuciyarmu ta Buga Dukkanmu mu fadi mu mutu..!
Hajiya ta kama baki tana Fadin"Assh..Haba Sa"idu bama zai taba Faruwa ba..!
Tari ya farayi sai kuma jikinsa ya fara rawa Da Sauri Hajiya tace"Mallam yace komai zai daidaita ko ba Haka ba..?
Tafada tana kallon Mallam din wanda ke kallonsu bai ce komai ba Rawanin kansa ya gyara kafin yace"Insha Allahu..Zan Daura ma Amina aure in an idar da Sallar azahar da yardan Allah..!
Baba Sa"idu da Hajiya suka kallesa da mamaki Aba ya rausayar dakai yana Fadin"Ina fata da bada wannan Lalattacen yaron da suka gama Lalacewa bane ko..?
Baba Mallam ya yi mirmishin su na manya kafin yace"Bashi bane Sa"idu..!
Hajiya tace"To waye ne Mallam..?
Sai da ya kara Murmusawa kafin yace"Da wanda Allah ya kaddara..Shine dai wanda Allah daman ya Rubuta Mijinta ne dashi za"ayi..!
Hajiya daman tasan bazai fada ba Tunda bai iya fadamata ba kuma bai Fadama Sa"idu ba to Tattabata bazai Taba Fadama kowa ba..!
Aba ne yace"Kada ka Tursasama Mutumin Kirki sai ya aureta Mallam..Ka hadata da irinta sannan ka Sanar da kowaye halinta Baba..Kuma ina so aje a gwada Amina kada yazo wajen Lalacewarta ta Samo wata cuta..!

"SA"IDU..!

Baba Mallam ya katsesa Cikin Tsawa da Bacin rai kafin yace"Kul na Sakejin wannan mganar daga bakin ka..ina da yakinin Har Abada acikin zuru"ata baza"a samu bara Gurbi ba...Duk da Allah na Jarrabatan bayinsa ta kowani Fanni Ammh ta wannan gabar ban yarda ba..Amina bazata taba Rusa Tarbiyarmu ba Sa"idu ba abunda zan ce ma wanda zai aureta illah ya Rikemin ita Amana kuma in Cucuta koda abayan Idanmu ne Ban yafe MASA BA..!
cikin kaushinsa ya karishe mganar da ta ja Hankalin Aba da Hajiya suka kalli juna bai kuma basu zarafin mgana ba ya kalli Hajiya yana Fadin"Kinsan suna jiran ki ko?
Kai ta gyada kafin tace"Shikenan Allah ya kara afuwa..!
Har ta juya zata tafi Baba Mallam ya Kira sunanta ta juyo Cikin bacin ran da bai barsa ba yace"Ki fadama su Balaraba kada wata cikinsu ta kira yaran nan dake gidan auransu tace zata Daga musu hankali ko Husai ban yarda afadamata ba..!bana so a adaga musu Hankali..!
Hajiya tace"Insha Allahu ba wacce zata ji..!
Kai ya gyadaa mata ta juya ta cigaba da Tafiya har takai kofa zata fita ya Kira sunanta wannan karon a Taushashe ta juyo tana Fadin"Mallam..!
Kai Tsaye yace"Umaru ya kiraki kuwa..?
Cikin mamaki tace"A"a rabona dashi Tun shekaranjiya da safe..! lafiya kuwa.?
Mirmishi yayi kafin yace"Bakomai..Allah ya kaiku gida Lafiya sai na dawo.!
Hajiya ta jinjina kai kafin ta Fice ya bita da kallo Daman ai yasan bazai taba Kiranta ba Shi ya Haifi Umar ammh yana Daraja kyakyawan Dabi"ansa..!
Aba ne yace cikin Raunin Murya"Kayi hakuri Baba..!
Hannu ya dagamai kafin yace"Nace ne kada na sake jin irin mganar makamancin wannan abakin ka..Ba hakuri nace ka bani ba..!

Cikin Sauri Aba yace"Insha Allahu..
Sai alokacin Baba Mallam ya saki Fuska yana Fadin"Allah yayi maka albarka kaida zuru"arka Sa"idu.Har Abada ban taba Nadamar samunka Cikin zuru"ata ba..Ka warke da wuri ban shirya rasa Da"a na farko ba..!
Ya karishe Cikin barkwamci Da sai da Aba ya Murmusa Lokaci Daya Hawaye suka cika kwarmin idonsa yake Fadin"Nagode Baba..Nagode Ban taba jin kai ba Uba kake gareni ba..Ina Alfahari dakai..!
Baba Mallan yayi wani kayattacen Mirmishi kafin yace"Nima ina Matukar alfahari dakai Sa"idu..!

*******

Tana cikin Tiolet din Bedroom dinta taji Ringing din wayarta Allah yasa ta Gama wankan ta Dauro babban zaninta ta fito wayar tana kan Mirror dinta ne Jikinta yana digan ruwa takai Hannunta saman wayar wanda taga yana kiran nata ne yasa taji gabanta ya Fadi..!

"MALLAM..!
Chapter 63 · 0% Book details