← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 193

Sashe 122

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana Dauka ko Sallama batayi ba ta Fara fadin"Habibi..!
Rai ya bata kafin yace"Bana fada miki..Ki daina daukan wayata baki min Sallama ba..?
Tuna haka yasa tayi Saurin mai Sallama ya amsa mata yana tambayanta lafiyanta tace"Lafiya lau Habibi ya aiki..?
Yace"Alhamdulillah ya naji kamar kina kwance ne..?
Gyara kwanciya tayi kafin tace"Wlh kuwa ban tashi ba..Tunda nayi sallar asuba na koma barci..!
Cikin mamaki yace"To Haka Aminar ke tafiya makaranta bata yi kari ba kenan..?
Sakina ta bata rai kafin ta tabe baki Tace"Wacece haka..?
Yana jinta sai bai tanka ba Sanin Halinsa yasa tace"Kace min wannan kazamar matarka taka..Ohon mata Daman na Fada maka bazan dinga mata Bauta ba, ba zamanta nake yi ba..!
Sai kuma yaji bai ji Dadin sunan Data kira Amina ba Duk da shine silar saka mata sunan sai yaji bai Dace ba Domin karshen kazanta kenan ya Ratsa Amina ahakanta,aiko kazanta ya kare.
Tattare naman goshinsa yayi bai yi mgana ba yana kokarin Daidaita yanayinsa Sakina ta cigaba da Fadin"Da Safe ake zuwa Daukanta makaranta ni bana ma sanin Tafiyarta..Sannan bata Dawowa sai yammah ranar jumma kuwa in tatafi makaranta da saafe sai Lahadi da yammah take dawowa sai mu yi kwanaki bamu hadu ba in ma mun Hadu bata min mgana sai kallon banza Habibi yarinyar nan ta gama Rainani bata da kunya Ranar fa Har Zagin Ubana tayi bayan tafiyarka ba Dadewa..!
Yana jinta bai ce komai ba aransa yasan Amina zata aikata A dan Sanin da yayi mata da labarinta dayaji Sama sama Zata aikata sai dai bai yarda ba Sakinar ce ta fara Zaginta ba yasan ta Sarai Itama Sakinar bata da Hakuri.
Yana jinta tana cigaba da Fadamai Rashin mutumcin Amina shidai bai ce komai ba illah"Kiyi hakuri zan kirata zan mata fada..!
Sakina tace"To tana da waya ne..?
Kai Tsaye yace mata"A"a chan gida zan kira abata na mata fada..!
Sakina taji Dadi yasa ta gyara kwanciya tana kara shigewa Cikin blamket tace"Habibi yaushe zaka zo ka Daukeni..?
Ni in bazaka zo ba sai Su Jafar su Nemin Visa na taho..!
Yana jin mganarta yamata shuru Sai da ta fara magiya tana Fadin"Don Allah Habibi kayi Hakuri na tuba nabi Allah na bika..Wlh Daga yau bazan kara saba Umarninka ba..!
Ta karishe Fada Cikin kukan Shagwaba Saboda ko jiya sun yi mgana da Anty ta tabbatar mata da cewa mallam ya sanar da ita Umar zai zo ya Dauketa Dolensa..!
Shiyasa ta tadamai da mganar ita a Tunaninta komai ya zama yadda suke Fata abunda basu sani ba ba kowani Lokaci Allah ke basu nasara ba akwai lokacin da aikin da suke da yakini a kansa zai basu mamaki..!

Sai da ya gama jinta sannan yayi gyaran Murya yana fadin"Sakina na Fada miki abaya zan kuma kara Fadamiki a yanzu..in har ni mijinki ne mai baki Umarni ki bi to bazaki Dawo madina yanzu ba..Sai nan gaba in kin gaji da zaman gumel din..!
Sakina jikinta ya fara rawa  gabanta na Fadi ta ce"Habi..!
Bata karisa ba ya katseta da Fadin"A wanchan Lokacin sai da nace kada ki zo..Kika jin mganata kikace sai kin zo..Biki nawa ake yi baki san zaki je ba Zan ce miki ki shirya mu taho..?
Abaya bake kika bani Shawaran Dauko ki na kawo ki garin nan ba Ni nayi Ra"ayin haka,kamar ni nace ki Hakura da zuwa Bikin su Abida Tunda ba an gama sha"anin bane akwai wasu masu zuwa kika jin mganata kika kuma Zuga Sarood itama ta Tada min rigima Duk Saboda nace ki Zauna bani da kudi sosai sai wani lokacin..!
Sakina ta kwaso Rantsuwa bai bata Dama ba ya cigaba da Fadin"Ita mahaifinta ya Dakatar da ita bata Biyoni ba..Ke kuma kika Biyo ni kikazo to kuma Miye na jin Zafi Domin nace sai nan da wani Lokaci zaki koma..?
Ai kina son zaman nan din ne shiyasa nayi miki abunda kike so..Wlh itama Data sake ta Biyoni Dukkan nan zan barku nayi Tahowata lokacin da na Sanu Dama da Hali sai nazo na Taho Daku a kallah dai nayi muku abunda kuke so kada kuce nayi miki rashin Daidai..
Kinsan Wlh rantsuwa ce ko..?
Sakina sai in na Samu Lokacin nazo sai mu koma Tare in kuma kika ce zaki Biyoni bansani ba to ba da Izinina ba..!
Daga haka ko cewarta bai jira ba ya Katse kiran yana Faman kokuwa da Bacin ransa Sakina kuwa kamar tayi Hauka haka ta mike tana Laluban wayar Anty sai dai bata Sameta ba Kasa Zama tayi ta mike tana Safa da marwa acikin Dakin tasan Waye Umar kaifi Daya ne in yayi mgana baya Sauyata ammh sai da ts saki jiki da Anty da ta tabbatar mata da cewa zai zo su koma Tare,sai dai wannan Jadadda mganar tasa yasa ta kara Sarewa a baya ma acikin ranta har ta Tsara in bai zo ba zata yi Visa da kudinta ta bisa sai dai ya ganta ai tasan Hanya ba inda bazata kai kanta ba A madina ba.!
Sai gashi furucinsa ya sa wannan Tunanin ya bace mata tasan kuma tunda yace bada yawunsa ba in ta Sake ta taka wani abun ne kuma zai Faru na Dabam wanda bata Fata wayar Anty Amarya tayi ta Kira kamar zatayi hauka bata Sameta ba

Shi kuwa yana katse kiranta ya Kira Aliyu saboda yanayin Yan"uwansa duk suna Nageria ne yasa yake saka Kudi mai yawa saboda yafi Sauki shi ya Kirasu da su Dagachan su kirasa.
Kiran farko Aliyu Dake wajen aiki shima acikin Office dinsa ya Daga kiran yana Fadin"Ango..Kaga angon Amina Larabawan Madinatul munawwara..!
Umar yayi Dariya kafin yace"Taka Sallamar kuma kenan..?
To Allah ya shirya Sallamu Alaikum..!
Aliyu na Dariya yace"Wa"alaikas salam Shehi mun tashi lafiya..?
Daganan suka gaisa kamar yadda suka saba kafin Umar yace"naji hayaniya kana wajen aiki ne hala..?
Aliyu yace"Eh wlh tun Safe ma.!
Umar yace"Daman mgana nake so mu yi..!
Tana da muhimmanci sosai..!
Aliyu yace"To ina jinka ai ina Office dina ne.!
Umar ya gyara zama kafin yace"Matsalace dani na rasa wa zan Tunkara shiyasa na zabi na Fadamaka..!
Nan ya fadamai Halin da suke ciki shi da Sarood.
Aliyu ya Saki baki ya Rufe sau ba Adadi bai sani ba kafin yace"Bangane ba ita Sakinar kuma Lafiya kalau kake in ka Rabeta..?
Umar yace mai eh Aliyu yace"To Amina fa ka jarabata ka gani..?
Sai ya kasa mai mgana sai da yaji Shuru sannan Aliyu yace"Common Mutumina Saboda mu gano matsalan ne yasa kaji ina Tambayanka..!
Sai da ya Runtse kafin yace"Itama Lafiya kalau..!
Aliyu yayi ajiyar rai kafin yace"Umar kune malamai ya"yan malamai adan Sanina da ilimina na hasaso wani abu..!
Umar yace"Me ka Hasaso..?
Aliyu yace"Al"amarin ka kamar Sihiri kamar kuma shafan Aljanun mutanen Boye..!
Umar yayi shuru yana wani Tunani kafin yace"Sihiri kuma..?
A"a sai dai in Shafar aljanun in na rabeni bazan musa ba..ammh ni kam wazaimin Sihiri ni bani da abokin Fada kai Sheda ne Aliyu..!
Aliyu yace"Hakane sai dai shi Rayuwa bata ga haka..Kana zaman zamanka baka Damu da kowa ba wani na chan yana Bakinciki da duk wani Cigabanka..!
Umar yayi ajiyar rai kafin yace"Sai dai shafar Aljanun Aliyu..Bazan musa ba Ammh ina Tunanin ko ta bangaran Sarood ne..?
Ina da yakinin yadda na tsare kaina da addu"a azakar Safe da Rana da Karatun Qur"ani da Ibada aljanu bazasu Shafeni ba insha Allahu..!
Aliyu yace"Duk zai iya yuyuwa hakan din ma.!
Danmallam ya Dafe kansa kafin yace"to menene mafita.?
Aliyu yace"Ni dai a  a shawarata ka Shawarci mallam na Tabbata shi zai san wani abun da bamu hango ba..!
Umar yace"Ina jin kunya fa..!
Aliyu yace"Lalura ce Shehi..Sannan Maallam ba kunya Tsakaninku..!
Umar ya jinjina kai kafin yace"Hakane Shikenan zan yi Tunanin hakan nagani in munyi mgana zan kiraka kaji yadda mukayi Dashi..!
Daganan sukayi sallama bayan Aliyu yace yana jiransa.
Duk yadda Danmallan yaso ya Kira mallam sai yaji ya kasa yafi dai yadda da mganar Aliyu na shafar Aljanun yafi kuma yarda data bangaran Sarood ne ya yanke shawaran in ya koma gida zasu yi magana yasan wasu mganguna anan madina na irin haka da kuma addu"o"in Tsarin Shafar mutanen Boye zai saka ta Jaraba ta gani in abun bai yi ba bai da wata Mafita sai na kiran mallam din.
Aliyu kuma mamaki ya cika sa na wannan lamarin ya fi karkata ga Sihiri ne saboda wani abokin aikinsa da suke Tare anan hakan kusan ya Faru dashi da ya kara aure shi ma Ba wani motsi  tun yana shuru har mgana ta kaima Manya Mahaifiyarsa ce yar gidan malamai nan aka gano Shihiri ne sannan kuma ana Zargin Uwargidansa tayi mishi da aka Mike Tsaye da addu"a da mgungunar karya Sihiri Tuni aka wuce wajen shima yaso Shehi ya yarda da mganar sa ammh sai yaga bai amince ba sai ya bar sa a Inda Tunaninsa ya karkata sai dai yana Fatan In ya kira Mallam din adace.!

********

Bayan sati Daya..!
Chapter 122 · 0% Book details