← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 193

Sashe 159

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yau ta kama laraba ne da wuri suka dawo daga islamiya saboda anyi rasuwa ne Baban wata yar ajinsu Samira yahaya ne ya rasu sai aka zabesu su goma sha biyar maza biyar mata goma sukaje gidansu samira gaisuwa,bayan sun dawo mallam Ahmad yace kowa ya wuce gida sai Ranar asabar.
Dayake sun cigaba da zuwa islamiya da Haddarsu kamar yadda suka saba suna dawowa ba su wuce gidan Baba mallam ba sai suka yada Zangonsu gidansu Baba Sa"idu Sa"adatu daman bata je islamiyar ba wai batajin Dadin haka sukaji Sabeeha na fadama kawarta mariyan ajinsu.
Mamanmu na cikin Daki ta baje a Tsakar falonta ta baje wasu Sabbin kaya sababbin Dinkunanta ne da tayi Domin da gaske take yi sai ta shiga ta Fita ta kece raini a wannan Bikin.
Tana cikin Duba Dinkunan taji Sallamarasu kafin ta kauda kayan sun Daga Labule sun shigo Da fara"arta ta Tabersu tana fadin"A"a Amare ne da kansu Ashe daga ina haka..?
hanne gefen Mamanmu ta Zauna yayinda da Hamida ta zauna kan hannun Kujera tana Fadin"Daga makaranta .!
Mamanmu tace"To naga kun tashi da wuri Lafiya..?
Hanne tace"Rasuwa akayi mukaje gaisuwa daganan mallam Ahmad yace kowa ya tafi gida sau ranar asabar..!
Mamanmu tace"Oh..Allah ya jikan musulmi..!
Suka amsa da Ameen kayan take Dagawa Bakinta Har kunne tana Fadin"Kayan da zan ci fitar Bikin ku ne fa..Kun gansu nan ba"a Dade da aikomin dasu daga wajen Dinkin ba..
Less din take Dagawa har Hanne ta amsa tana fadin yayi kyau Hamida kuma kayan take kallo da mamaki ita dai bata saba gani ba ko ana Biki mallam ke ma kowa kaya daga manya har su yara sannan kwananan mamanmu Facaka kawai take da kudi yawancin Suturunta duk ta sauya su Taoffinta kuma ta aika dashi Gusai Tana ta sota mata mgana kuma ta kasa bata san ta ina zata fara ba Sannan ko Jiya taje kasuwa ta nuna mata Dinbin kayan data siya mata na Kitchen da sunan ita ta siya mata alhalin Hajiya ke siyan komai bama haka ina Mamanmu ta samu uban kudi haka datake ta kashewa..?
Abunda bata sani ba Aba yake bata ko Da bai yi niyya ba da tace ya bata bazai iya mata gaddama ba ko nawa tace ya bata haka zai dauka ya bata.
Hanne ce kadai ta Daga kayan ta gani ta yaba Hamida kuma daga inda take tace sun yi kyau basu wani jima ba suka tashi suka koma Dakin su Hamidar Hanne kan gadon Amina ta kwanta daman ko gidan ta kwana nan take kwanciyarta Hamida kuma tana Tsaye tana ninke Hijabin jikinta Data Cire ta ga Hanne tayi tagumi tana Tunani.
Sai da ta maida Hijabinta Cikin Dirowarta sannan ta isa kusa da Hanne ta Dafata da Sauri Hanne ta Dago tana kallonta cikin wani yanayi Hamida ta sauke Nunfashi kafin tace"Haba hanne wai wannan mganar har yanzu bata daina damunki ba .!?
Hanne sai kwalkwal kamar zatayi kuka Cikin wani yanayi tace"Hamida ya Zanyi..?
Da wani ido zan kalli Amina in ta Dawo taji yadda abubuwa suka koma..!
Hamida tace"Na fada miki ki daina Sako mganar Amina a wannan mganar..Amina fa yanzu ba kamar da bane..Matar aure ce kinga kuwa Igiyar aure ai ya kore komai Hanne..Ayadda nasan Amina Zata fi son kwanciyar hankalinki fiye da nata Hanne ni shaida ce irin kaunar dake Tsakaninmu..!
Hanne ta Saka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta na wani Lokaci Hamida ta rike hannayen nata tana fadin"Dom Allah ki daina damuwa..Matar mutun fa kabarinsa Wani ai baya auran matar wani..haka ita ma matar wani bata auran mijin wata..Ga misali da Amina waya taba Zaton zata auri ya Danmaallam..?
Ammah dayake matar sa ce tun daga Launil Mahafuz ba gashi ya faru ba..Ki kwantar da Hankalin ki hanne Hajiya da mallam bazasu taba Zaba mana Abunda zai cutu garemu ba..!
Hanne ta cire hannayenta a kan Fuskarta lokaci Daya tana kakalo Mirmishi Hamida ta saka hannu ta Share mata hawayen tana Fadin"Bana son na ganki cikin Damuwa duk nima sai naji na shiga damuwa..!
Hanne tayi yar dariya kafin tace"Nagode Hamida..Na rasa Amina ammh baki barni nayi kewarta sosai ba..!
Hamida tace"dukanmu muka rasata Hanne..Kuma junanmu ne bamu bari kewarta ta mana illah ba..Sai dai Amina wata aba ce awajen mu da mantawa da ita abu ne mai Wahala..!
Hanne tace"Ni damuwata har da yarda za"ayi auran mu hamida ba Amina..!
Hamida tayi shuru kafin tace"Nima abun na raina..ko xamu je mu roki Hajiya ne don Allah Amina tazo mana Walima ko bayan Bikin namu ai sai ta koma inda basu san mu sani din..!
Hanne tace"Kin kawo shawara mu yi sallar mangariba sai mu shiga. !
Haka kuwa akayi suna Idar da Sallah suka ma mamanmu sallama wacce ta idar da sallah ta amsa musu da sai da Safe saboda tasan har Hamida ba lalle ta Dawo ba Jawad ma ya shigo ya Cire Kayan makaranta ya saka na gida ya fitaa masallaci domin wannan tarbiyan ta salla Cikin jam"i ko yaro karami ne yasan da ita agidan mallam yunusa Bazanga.
Sanda suka shiga shashen Hajiya sun sameta tana addu"a ne bayan ta idar da sallah sai da suka jira ta shafa Daman tun da ta ga shigowarsu sun wani uban buga Layi agabanta aranta ya bata mganar Amina ne domin shi kadai ke sakasu kaga sun zama kalar Tsausayi..
Tana rike da Cashabanta ta kallesu tana Fadin"Lafiya na ganku haka..?
Ko duk Tunanin barin gidan ne ya"yan Hajiya..!
Kansu na kasa suka gaisheta ta amasa Cikin Fara'arta tana fadin"Amaran namu duk sun rame sai dan wuya..!
Mirmishi kadai sukayi kansu na kasa kafin tace"Nasan da mgana a bakin ku ko..?
Hanne ta Dago tana fadin"Hajiya mganar Amina ce..haka za"ayi Bikin mu Amina bata zo ba Hajiya..!
Hajiya sai da tayi dariya Har Hakoranta suka bayyana Cikin Girgirza kai tace"Daman ai nasan Tatsuniyar gizo ai bata wuce ta Koki..Daman ai labarin kenan Amina..Amina ita ma tana chan duk mganarta da Zencenta Hanne da Hamida..Wannan kaunar junan naku Allah ya barta har ya"yan ku da jikokin ku su hadu a aljannah Firdausi..!
Suna Mirmishi suka amsa mata da Ameen kai ta gyada tana Fadin"Amina ce dai damuwar ko..?
Atare suka Daga mata kai Tana jan Casbahanta tace"To ku sha kuriminka..Amina na nan tafe da yardan Allah da ita za"ayi sha"anin auran ku..!
Ido suka zaro a tare suka ce"Da gaske kike yi hajiya..!
Cikin Yar dariya tace"Insha Allahu..Itama tana chan tana shiri..Bikin Hanne da Hamida bazai wuceta ba insha Allahu..!
Saboda murna sai da Hamida da Hanne suka rumgume juna kafin su saki juna suna ma Hajiya godiya ta amsa musu cikin sakin fuskar tana ce musu sai su sudaina ramewa Amina Zata Dawo haka suka fice suna Murna ammh bayan Hajiya ta gargade su kada su fadama kowa sukace ba wanda zasu fadamawa.
Ita kanta Hajiya bata isa ta hana Amina zuwa Gumel ba wannan karon Duk taso sai Amina ta Haihu ta Dawo da ita ammh Mallam ya nuna mata kada su kwari Amina da yawa bata da Zence sai na Hanne da Hamida in har sukayi aure bata zo ba abun zai mata Ciwo suma haka sannan Mijinta ma yabada goyon bayan su taho tare da Aisha shiyasa ta amince bayan tayi wani Tunani sai taga haka din shine Daidai.
Hanne da Hamida jin Labarin zuwan Amina wajen Hajiya Bakin da bazai musu karya ba yasa suka saki jikinsu Damuwasu ta ragu,Shiryen shiryen Biki kuma babu abunda aka fasa su dai basa wani shiru tunda basu da kawaye daman Amina ta fisu gayyar kawaye sai Sa"adatu su bama su fadin zasu yi aure da Bakinsu koma tambayansu akayi shuru suke yi abunsu.saboda lamarin yazo musu ne alokacin da basu taba zato ba ballatana Tsammani ba..
Daman ai haka rayuwa ta gada..Sau Tari abubuwa da dama suna Faruwa damu ne bamu tsammaci Faruwarsu ba..Haka lamarin Ubangiji yake.

******

*ABUJA..*
Chapter 159 · 0% Book details