← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 193

Sashe 35

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

******

Anty Amarya na Falon Shashenta Cike da baki,Wayarta Dake hannunta ta Fara kuka tana Dubawa sai da gabanta ya Fadi agogon bangon Dake Dakinta ta Duba 12am na dare ta wuce Acikin Dakin akwai wadanda sukayi barci akwai wadanda basuyi ba.
Sulalewa tayi ta nufi Bedroom dinta nan ma cike da Mutane Dayan Dakin ta Nufa taga Sakina na ciki ita Sarood sai kawai ta Juya ta Fice Daga Shashen Har wata yayar Anty Amarya tana Fadin"Marliya ina zaki da wannan Tsohon Daran. ?Sha biyu fa ta gota..!
Ta fice tana Fadin"Yanzu zan dawo Ya Salamatu..!
Kitchen dinsu tana jin hayaniya su Lami tana aikin Miya zasu soya da Daran nan na abinci gobe nan zasu kwana ganin haka yasa tayi kamar zata je shashen Baba Mallan sai ta Shuge lungin Dake tsakanin Shashen nasa da Bangaran Dakunan mazan gidan.

Jikinta na Rawa ta Daga kiran har ta katse sake kira akayi Cikin Makale murya tace"Miye haka DAYYABA..?
Kinsan fa gidan cike yake da Mutane..!
Shuru tayi na dan Lokaci da alamun Tana Sauraran mai mganar ne Daga Chan bangaran
Kafin na ga ta saki wata Kayattaciyar Dariya kafin tace"Daman nace sai an gama wannan Hatsaniyar zan kiraki muyi mgana..Balarabiyar banza..?tasha gabana har ta sakani Fargaba..Tuni nayi mganinta Daman na Fadamiki bayan Sakina ba macen da zata Kafu a gidan Umar bayan ita. wannan Burina ne in ban samu mallaka Malam ba..Zan samu Damar mallakan abunda yake Takama Dashi Dagashu har Hajiya Babban atafin hannuna suke Dayyaba..!
Shuru ya sake biyo baya kafin chan kuma ta kara Sakin Dariya tana Fadin"Kema saura kiris...Ki kara Hakuri kawai..SA"IDU ma matsalata ce Dayyaba..Shiyasa na Hada hannu Dake ni Burina bazai cika ba sai Sa"idu ya bar mallan..Kema naki Burin bazai cika ba MAtukar HADIZA na Numfashi acikin gidan Sa"idu zamu mgana..Hanya Dayace...Kawai da zai sa komai ya Dawo hannuki...
Zamu mgana in Hankula suka kwanta..!

Kamar Motsi taji abayanta da Sauri ta katse wayar ta leka Shamsu ne ya Fito yayi alwala ya koma Dakinsu sai da ya Dade da shiga sannan ta fito inda Allah ya Taimaketa An kashe gen Duhu yayi sosai yasa ta Lalaba tana Waige waige ta shige shashenta Lokaci Daya tana Sauke Numfashi.
Sako ta Turama Lambar data kirata.

*Kada ki sake kirana..Sai ni na Kiraki da kaina..*

*Janafty*
[11/3, 2:05 PM] Sweet sis: *TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*🅿️13*

Karfe Daya da Rabi na Ranar jumma"a 1:30pm aka Daura auran su ya Zulaihat a babban masallacin Gidan Baba Mallam bayan an idar da Sallar jumma"a masallacin Daman Kaf anguwan da Zagayenta shine babban masallaci,Shiyasa bayan karattukan Addini da akeyi da kuma Duka Sallolin khamsin Salatu ana Sallar Jumma"a acikinsa.
Kamar yadda kowa ya sani ne al"adan gidan Baba Mallam Ranar jumma"a yake Daura auran ya"yansa To hakan ce ta kasance ayau din ma ana idar da Sallar jumma"a Daman kowa yasan da Daurin auran anguwan ta cika ta batse da manyan mutane kama Daga manya malamai Daliban Baba mallam,Angaye da duka Tawagan abokansu abokansu ya Jafar da Sauran Mutanen anguwa da kuma Jama"a da basa Wuce sha"anin Babban malami irin Baba Mallam.
Bayan an gama Daura auran Gabadaya Tawagan angayen da abokansu da su ya jafar da su ya Danmalam dashi da abokinsa kwara Daya Tal Daya gayatta wanda ko bai gayyaceshi ba zai zo tunda sun zama Daya tare sukayi makaranta Tundaga matakin primary anan Gumel kafin aiki ya maida mahaifinsa Dutse,suka koma chan cikin ikon Allah kuma sai suka Sake hadewa a Dutse a Wata Bording school ta maza Inda suka Dora matakin Secondary Dinsu.
Aliyu Ahmad Gumel yanzu haka Lacture ne a School of Nursing Dutse acikin makarantar ma yake zaune da Matarsa mai suna Aliya da ya"yansu Hudu sai mahaifiyarsa dake tare da Iyalinsa mahaifinsa ya Dade da Rasuwa shine kadai amini kuma aboki ga Danmalam wanda Tare ma suka zo da Iyalin nasa tana cikin gida wajensu Sakina,Kawaye ne ita da Sakina Tunda in dai suka zo garin suna zuwa Dutse wajensu sannan Aliyun yaje Madina shi da Sakina ashekarar da suka je Hajji sai suka Rankaya gabadaya suka isa makka suka Sauke Farali.
Gabadayansu cikin gari suka tafi wani kayattacen Waje inda sukayi Reception wanda Danmallam ya Dauki nauyin komai ya hana su Hajiya yin wani abincin Daurin auran Mallam ne kadai da Aba basu awajen,Suna sallaman baki mutanen bazangs da kuma yan gusai da ana gama Daurin auran suka juya
Chapter 35 · 0% Book details