← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 193

Sashe 52

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu wanda ya taba Lura da Halin da Amina ke ciki sai dai an fara Lura da ta na yawan Shiga bandaki ta Dade bata fito ba,Ranar Bandakin waje ta shiga tafi minti Talatin bata fito ba Da Daddare ne duk suna Tsakar gida abaranda suna shan Iska Aba ya Dawo yana Shashensa Yaya tatafi wajensa Mamanmu ce da ya Zeenatu da Hamdiya sai jawad Dayayi barci kan katuwar Tabarman da suka baza anan Baranda abincin Dare suka gama ci su ka koma Hirar Anty sakina da Tayi barin yan Biyu,Achan madina din ance ta Zubar da jini sosai sai da tafi asibiti Anty Amarya taso taje Baba Mallam ya hana yace akwai mahaifityar Sarood da ita kanta Sarood din suna kula da Sakinar sai dai ance Danmallam din zao zo akwai mganin Hausan da zai tafin ma Sakinar dashi. Duk Amina na cikin Bayin Tsakar gida tana jinsu suna waya da Aminu ya katse yace ta jirashi ya amsa wani kiran bata so ta fita kuma ya Sake kira ta shiga uku duk da wayar asilent take sakata kuma da sun gama waya take Goge Lambar tasa data Riga ta Haddaceta akanta. Tana nan Tsaye tsabar sakama rai bata Damu da inda take wajen Najasa bane,Hankalinta kwance take shigowa suyi wayarsu domin nan din ne kadai mafita inda Hankalin wani bazai zo kanta da wuri ba. Karaf taji Hamida na Fadin"Wai ina Amina ne..? Mamanmu tace"Ba ta na cikin Dakin ku ba..! Ya zeenatu na kishingide tace"Ina jin fa bata fito ba..Naga Daukan butatanta da shiganta Bayi indai ba yanzu ta fito ba to tana ciki..! Hamida tace"Kai meke damun Amina ne..? Kwanakin bata da aiki sai shiga bayi..Kuma sai ta Dauki Lokaci kafin take fitowa ko Basir ne ya kamata..!? Mamanmu tayi shuru kafin tace"Nima na Lura mgana ce kadai ban yi ba..! Ya Zeenatu tace"Ko basir din ne mamanmu..? Kinsan fa tana sska yawan kashi..! Mamanmu tace"Bari ta fito muji dai..Ammh yawan shiga bayin Amina bana Lafiya bane..! Duk Amina na jinsu sai jikinta ya Saki Yanzu wani amsa zata basu..! Bata gama Tunani ba Aminu ya sake kira sai ta manta da su mamanmu ta Dauka suka cigaba da Hirarsu. Bata da Tsammani taji Muryan Hamida gabda kofar Bayin tana Fadin"Amina..Amina..! Mamanmu shuru fa bata amsa ba..! Jin haka yasa Mamanmu ta mike tana gyara Daurin zaninta Lokaci Daya tana Fadin"Zeenatu ba Lafiya..Gayama Aba dinku da yaya na shiga uku ni Balaraba..! Take fada Cikin Rudewa Tunaninta Allah yasa ba masai Amina ta Fada ba basu sani ba Zeenatun ta Rude itama ta kwashi Sauri zuwa Shashen Aba ta Fadamai jin haka yasa Amina tayi Saurin katse wayar jikinta ya fara rawa saboda Sauri yasa sai taa danne wayar ta kasheta Gabadaya ta Turata Cikin Wandonta Hamida na shirin Turo kofar Makewayin Amina tayi Zaraf ta fito har tana Bangaje Amina. Sai Hamida ta saki baki tana kallon Amina datayi wani Fiki Fiki da ido. Daidai Lokacin da Mamanmu ta Kariso tana Fadin"Jijjiga Kofar makewayin Hamida a bude take..Ami..! Bata karisa ba ta ci karo da Amina Tsaye Cikin Sauke Numfashi tace"Alhamdulillahi..Wlh gabana ya Sare na zata kin fada masai ne..! Da sauri Amina tace"Masai kuma mamanmu..! Tace"Yo eh mana..Wajen awanki Daya fa da shigarki bayi baki fito ba..ni har na saka Zeenatu ta Kira babanku da Yaya..! Amina bata samu Zarafin mgana ba sukaji Muryan Aba yana Fadin"Balaraba meke faruwa ne..? Sukaji Muryansa sai Amina ta Rude da Sauri ta matsa jikin Mamanmu tana Wurga ido. Hannunta ta jawo zuwa Tsakar gida Hamida ta biyo bayansu Lokacin da Yaya ke fadin"Me ya samu Aminan..? Zeenatu tace ta shiga makewayin tun dazu bata fito ba..! Badai wanda ta shiga tun kafin Aba dinsu ya shigo bane..? Hamida tace"Shine..Yaya mu mun zata ko ta suma ne ma abayin..! Aba ya kalli Amina na Tsawon Lokaci yana Nazarinta yadda take Fiki Fiki da idonta ajikinsa yaji bai yarda da ita ba. Cikin kaushinsa ya Kira sunanta "Amina..! Sai da gabanta ya fadi da Sauri ta amsa"Na"am Aba..! Kai Tsaye yace"Me kike yi a bandaki har na tsawon wani Lokaci..? Kan Amina na kasa tana kokuwa da Fargabanta tace"Bakomai Aba.. Ya zeenatu tace"In baki da lafiya ne ki Fada a nema miki mgani..Wlh Aba kusan koda yaushe Amina cikin shiga Bayi take kuma sai fa an manta da ita take fitowa..! Kallonta kawai yake yi yana kara nazarinta Hamida tace"Ni fa na Fara Tunanin ko Aljanu sun shafe ta ne..! Har fa bayin Dakin Mamanmu tana shiga ni Ranar mada ta shiga na shigo sai na rika jin mganarta kasa kasa har da Dariya fa..Aba..? Kiris ya Rage Amina ta bata Dafe Kirji ba ta shiga uku Yaushe Hamida ta ji haka bata mata mgana ba.. Mamanmu ce tace"Mun shige su..Kuma shine baki Fadamin ba..? Hamida tace"na manta ne mamanmu..Ammh Tabbas Amina bata da Lafiya..! Kamar an Dasa Yaya da Aba haka suke bin Amina da kallo Mamanmu tana Salallami tana Fadin"Allah ya kaimu gobe zan shiga wajen Malam da kaina na Fada mishi Babansu kada fa ayi Shuru karamar mgana sai kaga ta zama Babba..! Ya zeenatu tace"Mamanmu gama Turaran Hayakin nan da Baba mallak ya bada kika taba Turarama ya Zulaihat da suka taba Bigeta a makaranta..? Yana cikin Dirowarki ki Turara mata yanzu agani in ma sune zasu bayyana..! Mamanmu tace"Yanzu kuwa Zeenatu..! Aba ne yayi gyaran Murya kafin yace"Ba fa wani Aljanun Dake Damunta..Ki tambayeta ko wani Cutar ne dabam..! Jin haka yasa da Sauri Amina tace"Aba basir ne..Zafi nake ji in naje yin bayan gida sai yaki fita..! Yadda ta fadi mganar yasa Dole ma ayarda Yaya ce tace"Ararrabi zaki sha yana mganin basir sosai..! Aba ya juya yana fadin"Ku jika ku bata sha in bai yi ba zan ma Nasiru mgana sai ya kaita taga Likita nan General..! Daga haka ya shige Falonsa,yaya kuma ta koma Daki ta Dauko Daddaken Ararrabinta da bata Rabo dashi ta Jikama Amina aruwa kadan ta bama Mamanmu hade da Sauran na Ledan tana Fadin"Tasha wannan yanzi..Gobe da safe ko atea ko koko sai ta kara sha insha Allah cikin zai saketa tayi bayan gidanta Lafiya lau..! Mamanmu ta karba tana Godiya ita ta tasa Amina sai ta Shanye duka tas tana yamutsan baki Saboda Bauri bata Damu ba Hankalinta ya kwanta Tunda ta isa barka asirinta bai Toni ba. Tundaga Ranar Amina ta Rage shiga Makewayi tana waya Aminun ba sai da aka kwana Biyu ta nemesa ta Fadamai Halin daake cikin Cikin Damuwa yace"Meena ki bar ni nazo naga Aba ko mallam..nagaji da wannan kumbikunbiyan..Da gaske nake yi ina sonki kuma auranki zan yi..! Amina sai ta marairaice tana Fadin"Ba yanzu ba Amin..Aba ko mallam baazasu taba Sauraranka ba Ko fa Ss2 ban shiga ba ko aka"idan gidanmu sai kin kusa gama Canday ake Fara mganar auranki yanzu kana gani ko su ya Zeena bamu ji komai ba Har yanzu kuma basa su wuce shekarar nan mai zuwa ka Kara Hakuri akwai sauran Lokaci..sannan Zamu Rage waya na kwana Biyu..Gudun Faruwan wani abu wanda bazai mana Dadi ba.. Zan nemeka in na samu Dama..! Bazai iya mata gaddama ba Saboda yana sonta kuma baya so ya sakata acikin matsala. Atsukin Taji ance ya Danmallan yazo abakin Hanne sai dai kwana Biyu yayi ya koma Allah kuma yasa basu hadu ba,Don ko gidansu bai shigo ba,Tadai ji su Yaya nata jajanta Lamarin suna Fadin yace Sakina tasha Wahala sosai yaso ma ya taho da ita Mallam ne ya Hana shiyasa Anyi haka da kwana Hudu Labari yazo kan ya Zulaihat itama ta zame a bandaki Ta fadi itama tayi barin Cikinta,Tana asibiti washegari kuma Yaya da Hajiya Babba da Hajiya Uwa Mallam yasa Idi yakaisu kano inda mijinta ke aiki nan suka koma sukaje suka Dubata ya Zulaihat taso ta dawo gida sai ta samu Lafiya Baba mallan yace maza Tunda uwar mijinta nan ne da kanwarsa sun isa su kula da ita tana ji tana gani su Hajiya suka Dawo Gumel suka barta. Sauran yan'uwa kuma sai a waya suka mata sannu da jiki har da su Amina da suka gama nacin abarsu suje Mallam yace ba wanda zai taka bama su har su ya Abida Dake gaba dasu jin haka yasa kowacce ta maida maitanta. Amina sun cigaba da mgana da Aminu sai dai tana shiga Bandakin waje koda yaushe,Domin haka Mamanmh ta Dinga Dura mata mganin Basir Asihiti kuwa sai da Aba ya Tambayeta ta warke ko kuwa sai sun je asibitin tace ta warke shiyasa sai ta sauya Taku. Sai dare yayi in suna Tsarkar gida da an fara Hira sai ta fara hammar karya tace barci take ji ta shige Dakin Mamanmu chan kurya ta Kirasa da kuma taji motsu ta kashe wayar ta Boye ta Lafe kamar mai barci ba wanda ya Taba Fahimtar wani abu na Faruwa. Idon Amina ya Bude tasan menene Dadin Soyayya,Domin karamce karancen datakeyi sun kara taimaka mata sosai,Bayam su Hamida ba wanda yasan Amina na karatun Littafan Hausa su kuma Aminanta ne bazasu taba fada ba,Sai dai koda yaushe suna mata Fadan ta Daina Abunda take yi ita kuma sai tace ina Ruwansu..! Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah gashi har su Amina suna shirun Fara Jarabawar third Semester dinsu ns shiga SS2,alokacin kuma sun kwarari wajen wata bakwai tare da Aminu aboye batare da kowa ya sani ba. Sai dai akwai ranar da asirinta ya kusa Tonuwa Aminu yazo taki karyan Tana gidan su Hanne Fitanta kuma ba Dadewa sai ga Hanne tazo nemamta Hamida tace ai yanzu Aminar ta fita zuwa wajenta. Hanne ta kalli Hamida cikin mamaki kafin tace"To bata je don ban ganta ba..! Cikin mamaki Hamida tace"Wasa kike ko..? Kusan fa duk jumma"a Aminar wajenki take kai har mangariba fa Hanne..! Hanne ta zaro ido kafin tace"Ni..? Yaushe ranar ne fa shima ana kiran sallar mangariba ta shigo sallah kadai tayi na Rakota gida..! Hamida ta koma ta zauna ta waige waige kafin tace"To wlh Amina na fita kuma tace wajen ki taje Yanzu ma fa bata Dade da fita ba..! Hanne tace"To abun mamaki ina Amina take zuwa..? Hamida tace"Wlh bansani ba mu jira ta Dawo mu tambayeta..! Wasa wasa Amina har bayan mangariba bata Dawo ba Hanne
Chapter 52 · 0% Book details