← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 193

Sashe 59

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwana Biyar da Faruwar abun ta kasa Daurewa ta samu Hamida da Hanne ta Rokesu su samo mata waya ta Kira Aminu ko hamkalinta ya kwanta Hamida ta kalli Amina tana Fadin"Amina kada ki kara jawo wani Jidalin don Allah..!
Hanne tace"In dai zata kirasa ta Fadamai ya rabu da ita zan Dauko miki wayar hajiya..Ammh da sharadin wamnan shine na karshe..!
Da sauri Amina tace"Naji Hamne..Naji..!
So take kawai tayi mgana dashi Hamida kamar zatayi mgana sai kuma ta fasa,Hanne taje ta Dauko Wayar Hajiya Amina ta shige Tiolet din Dakinsu Hanne su kuma suna Waje suna Tsaro kada wani ya shigo su Lalace.
Jikin Amina na rawa ta saka Lambar Amunu ta Kira tana Di..Di..Di..kamar Zuciyarta zata Fito gabda zata Tsinke Taji an Daga Cikin Sanyinsa akoda yaushe yayi sallama Amina Kafafun sun rawa kawai sai ta sakamai kuka yana jin haka zumbur ya mike Daga kan gadon Hotel din daya kama yana Fadin"MEENATA..aminatu..Alhamdulillah..Amina na shiga wani Hali..Tun washegarin abunda ya faru ina garinku Amina kullum ina anguwanku ina ganin yan"uwanki ina so nayi musu mgana na rasa yadda zan yi..Meena kina ina ne..?
Meena ina so na ganki ki taimakamin in banganki ba wlh zan lallace Meemata..!

*Janafty*
[11/3, 2:05 PM] Sweet sis: *TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*🅿️20*

Jin ta kasa mgana sai kuka take yi yasa ya kara marairaicewa yana Fadin"Meenata kina ji kuwa...?
Ki yi hakuri ki daina kuka ki bari nazo Domin nasan ta yadda zamu al"amarin Kinji ko..?
Gabadaya yadda yake mgana ya gama kashe ma Amina jiki Tsausayinsa ya kara kamata tasan yadda yake sonta tasan Halinsa bazai taba kwanciyar Hankali ba sai ya ganta sai dai bata da wannan Damar ayanzu komai ya gama Lalacewa.
Tana jinsa cikin Damuwa ya kara Fadin"In zo Amina..?Don Allah kada kice A"a..Ina son ganinki..!
Hawayenta ta share cikin muryan kuka akaron Farko tace"Bazai yuyu ba..Kayi hakuri Amin komai ya kare..!
Ta karishe fada cikin kuka Tsabar yadda kalamanta suka gigita yasa ya koma ya zauna gefen gadon Daya tashu Cikin wani yanayi yace"Bangane ba Meeenata..?
Me kuma ya kare tsakanina Dake..!
Amina na Danne bakinta da kuka tace"Komai daka Sani ya kare..Soyayya ta dakai ta zama Tarihi kayi hakuri ba Laifina bane..!
Sai kuma ta kara Fashewa da kuka kukan da Aminu yake jinsa kamar acikin Ransa.
Cikin Fitan Hayyaci yace"A"a Amina kada kimin haka..Kada ki ce zaki Rabu dani alokacin da nafi kowa Bukatarki kinsan bani da kowa sai ke sai Nenne wlh in na rasaki Meenata zan Lalace ki bari nazo na ganki..Ki bari na bayyana kaina Amina Ina sonki Rashinki babban Gibi ne ga Rayuwata Amina ki taimakeni..!
Yana mgana hawaye na Bulbulo mata kamar famfo batasan sadda ta saki kukanta da karfi ba,Lokaci Daya ta abude Kofar Tiolet din ta Fito tana Gunjin kuka,bata kashe wayar ba ta mikama Hanne da Hamida da suka yo kanta ganin tana kuka kan gadon su Hanne ta Fada ta na Sakin kukanta Wlh itama tana son Aminu kuma Rabuwa dashi babban Ciwo ne agareta ammh ya zatayi..?
Aba zai kasheta in ya kara jin Labari makancin wannan,Zai iya mata baki Watarana shiyasa take tsoro sai dai tana Tsausayin Aminu tasan yadda yake sonta da gaske ne zai lalace akanta in ta rabu dashi.
Hamida ce ta isa gareta tana Fadin"Menene Amina..?Don AllAh ki Daina kuka hakanan..?
Hanne ce ta Lura wayar na tafiya yasa ta saka wayar a speaker daidai Sanda Aminu ke fadin"Meenata kina jina..?
Don Allah kimin rai ki taimakeni na ganki..Wlh kwanana Hudu agarin nan Saboda ke in ban ganki bazan taba Samun natsuwa ba..!
Ayadda yake mgana kowa yaji sa sai ya basa Tsausayi Amina kara Fashewa da kuka tayi zuciyarta na suya ashe ashe akwai irin wannan Ranar da Farinciki zai koma bakinciki bata Tsammanci Ranar nan kusa ba bata zata zata zo yanzu ba..!
Hamida da Hanne jikinsu ya gama yin Sanyi Hanne ce tayi gyaran Murya kafin tace"Ba ita bace..sunana Hannatu ni yar uwartace..!
Da Sauri Aminu yace"Hannen Amina..Hannen Hamida ai na ganeki..Amina tana bani Labarinku..Don Allah Hannatu ki taimakamin naga Amina don Darajan ma"aiki Salallahu alaihi wasallam..!
Suka karisa gabadayansu Cikin tsausayinsa Hanne tace"Akwai matsala ne..abubuwa Dadama sun Faru wadamda bazasu fadu ba..Ina Kara Jadaddamaka Haduwarka da Amina bazai yuyu ba kayi hakuri..!
Tana shirin yanke kiran ne yayi saurin Fadin"Koda na minti biyar ne..?
Koda na ganta nayi mata sallama ne Hanne..?Amina itace ni Hannatu..Wlh in bata zan Lalace Hannatu..Nenne zata rasani zata rasani..!
Dagajin yadda yake mgana kuka yake gabadaya sai hanne ta kasa mgana Cikin Tsausayi take kallon Hamida wacce ta Zabga Tagumi Ta rasa mafita sai Amina Dake kallonta idanuwanta Jajir tana kuka Dagachan taji magiyarsa Cikin Raunin Murya"Ki taimakeni Hannatu..Nayi miki alkwarin wannan shine na karshe..Don Allah ina son ganin Amina..Don Allah..!
Hanne ta saki ajiyar rai kafin tace"Shikenan..Kazo da Daddare bayan Sallar isha'i..'
Cikin Rauni yace"Meyasa ba yanzu ba Hannatu..!?
Hanne tace"Ba dama ne..Kabari dai Daddare shima sai mun san yadda zamu iya ku hadun..!
Suna jin Saukan Numfashinsa kafin yace"Nagode kwarai..Nagode Hannatu..Bazan taba mantawa da karamcinki ba..!
Da haka Hanne ta Datse kiran Hamida tayi saurin cewa"Hanne kikasan me kika aikata kuwa..?
Hanne tace"Ya zan yi Hamida..?Tsausayi ya bani..!
Hamida tace"To yanzu ta yaya zasu hadu batare da wani ya sani ba..?
Nidai ina Tsoro fa..Yadda abubuwan suka Lalace In muka kara wani laifin ba Amins ba har mu bazamu taba Fita ba Hanne..!
Hanne shuru tayi batayi mgama ba sai chan tace"Zamu samu mafita Hamida..Kada ki damu..!
Amina dai kukanta kawai take yi Cikinsu an rasa mai Lallashinta gabadaya Tsausayinta ya gama kamasu suna Tunanin har yaushe ne Amina ta bari ta fara soyayya har tayi wannan Zurfin basu sani ba..!
Sai da suka gaji da jin kukan nata suka Fara bata hakuri kana ta Hakura ta Daina kuka sai dai idanuwanta sun kumbura ido ya sauya Launi saboda kuka har zuwa yammah sun gagara samun mafita Hamida ta kalli Hanne tana Fadin"Ki basa hakuri kawai Hanne..banga mafita ba..Waje fa kinsan su Baba mallam suna nan ta ina zasu hadu batarr da wani ya gansu ba..!
Hanne dai batayi mgana ba tana ta Tunanin mafita ba har akayi sallar Isha"i basu samu mafita ba Ya Abida ce ta shigo ta gansu zugun zugum Dariya tayi tana Fadin"Ku kuma Lafiyarku kukayi zugum kamar masu zamam makoki..?Ko Aminar ce taki Warwarewa har yanzu ku cigaba da Iskamcin naku..?
Cikinsu ba wacce tayi mgana itama bata Damu ba baki tatabe tana Fadin"Bakin Amina ya Mutu..Na Hamida da Hanne daman bai kai nata Tsini ba ssuma sun mutu..Allah Sarki..!
Ta karishe Fada Tana Dariya wannan karon Mirmishi kadai Hamida tayi mata Ta fice daman wani Littafin koyon Turanci ta Dauka cikin Jakar makarantar ta fice.
Hamida Bini bini ta kalli Hanne tana Fadin"Kin samo mafitan ne..?
Sai hanne ta Girgizakai Cikin Damuwa Hamida kan ce"Jikina na Sanyi..Ina ji kamar wani abu zai faru Hanne..!
Itama Hanne haka take ji ammh Tsausayin Amina take ji da Aminu Shiyasa ta kasa cewa A"a tunda Farko Tunanin wani abu tayi taja hannun Hamida suka fita Leke suka fara yi Domin ganin wadanda ke waje Allah ya taimaka ba kowa masallaci ma an Rufe ba Motar ya Jafar bata Ya Nasir kenan sun tafi gida Saannan Allah ya taimake su Aba ya Dawo da wuri ga Motarsa nan sannan sunji mganarsa afalon Baba Mallam da Hajiya Babba..!
Hanne ta kalli Hamida tana Fadin"Na samu mafita..In..!
"Su waye anan..!
Gabansu ya fadi da sukaji Muryan ya Shamsu Cikin Daburcewa suka juyo Hamida ce tayi mgana"Bakomai ya shamsu cikin gida zamu shiga..!
Yana Taaye Daga kofar Dakinsu yace"Cikin gidam ina..!
Da sauri Hanne tace"Zan rakata gida ne ya shamsu..!
Kamar zai yi mgana sai kuma suka ga juya ya koma Daki ya Dauko Buta Makewayin Dake bayansu ya wuce bai karama kallonsu ba ganin haka yasa suka Sauke Numfashi Hanne taja Hannun Hamida suka Fice daga gidan zuwa gidansu wayar Hajiya tun mangariba ta Dauketa tana Hannun Hannatu.
Gidan su hamida suka je suka zauna Har Aba ya dawo sannan Hanna tatashi tace zata tafi Hamida ta rakata mamanmu har tana Fadin"Hanne baki kwanciyar anan..!?
Da sauri Hamida tace"Mamanmu Amina zata bari inta kadai in ta kwana anan..!
Mamanmu tace"Kuma fa hakane..To maza ki rakata Hamida ki Dawo Dare yayi..!
Da haka suka samu suka Fice Aba na Shashensa Yaya ta kaimai abinci suka Fice akofar gida suka Tsaya Hanne ta Leka Wani lungin jikin gidansu Amina Dake da Duhu kadan Tunda Kofar gidansu dana Baba Mallam gauraye yake da Hasken Gen da aka kunna Hamida ta nuna ma wajen tana Fadin"ZAm kirasa yazo ta nan su hadu..Ni zan Tsaya anan ki shiga ki Fito da Amina yau Hajiya Shashen baba zata kwana zamu Tsaya Daga chan muna gadinsu kada wani yazo..!
Hamida ta kalleta cikin Tsoro kafin tace"Kina ganin ba Matsala..?
Hanne ta Sauke Numfashu tace"Insha Allahu..Ki fadama Amina kada ta bata Lokaci..!
Kai hanne ta gyada ita ta Fara wucewa zuwa gidansu Hanne ita kuma ta koma kofar gidansu Amina ta Danna Aminu kira Daman ta adana Lambar da sunan Amina.
Tana shiga kamar yana jira ya Daga Kiran kafin tayi mgana yace"Ina Hangenku tun dazu hannatu..Amasallacin gidanku nayi sallar mangariba ma..!
Hanne ta zaro ido ta fara waige waige Daga chan gaba ta hango hasken Mota kafon a kashe sai kuma aka Bude Mota aka fito Cikin son Tabbatarwa Hanne tace"Kai ne Daga nesa..Ka fito a mota..!
Cikin wani sanyi yace"Eh nine..!
Da Sauri Hanne tace"To ka kariso da Sauri..Yanzu Hamida zata zo da Amina..!
Daga haka ta datse kiran ta shigo gidansu Amina jikinta na rawa kada wani ya fito ya ganta Aminu da Sassarfa ya kariso duk ya rame kamar wanda yayi jinya yana Sanye da Riga da wando bakake ya saka wata Rigar Sanyi mai Hula ya Rufe kansa yana zuwa Hanne ta Leko sai da Tabbatar ba kowa sannan ta fito tana Fadin"Don Allah minti goma..Akwai Hatsari Aba na cikin gida hakama Baba Mallam sauran yayyinmu ma suna cikin gida kada ka bata Lokaci har komai ya Lalace don Allah..!
Hulan kansa ya cire fuskarsa ta bayyana Cikin Muryansa kamar ta waya yace"Insha Allahu Nagode Hannatu..!
Zatayi mgana kenan sai ga su Hamida sun fito Amina na bayanta da Hijabi tana Tafe kamar wata mara Laka ajikinta Allah ya taimake su ya Abida na Kitchen Hajiya kuma na shashen Baba Mallam suka samu suka Lallabo suka fito Allah yasa ba wanda ya gansu..!
Chapter 59 · 0% Book details