Sashe 61
Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Raina ke hannunsa bazan aura ma Amina wannan yaron ba..Jafar Amina bazata samu abunda Take so ba..bata isa ba..! Yafada yana jin wani Takaichi da Bakinciki Ya Jafar Cikin mamaki yace"Dama kasan shine Aba..? Aba ya jinjina kai yana Bama Jafar Labarin abunda ya faru bai gama ba Ya Jafar ya Finciki Amina ya Fara Dukanta yana fadin"Kafin ki kashemana Uba ke zaki fara Binsa Amina..! Dukanta yake yi kamar Allah ya aikosa Ba wanda ya hanasa Yaya kuka take tana rike da Aba Dake fadin"Hadiza kamani muje ciki..Jiri nake gani..! Ya Zeenatu ma kuka take tana Fadib"Mamanmu ki cece Amina ya jafar zai kasheta..! Mamanmu Dukewa tayi tana Fadin"Jafar kadaina Dukanta don Allah..Jafar kabari..! Take fadi ko jinta bayayi sai ma Karisawa da yayi ya karyo ganyen Bishiyar Dake Tsakar gidan ya Shiga Lafta ma Amina wacce bata kuka ko kadan sai da Zuucii awannan gabar ta gagara tana jin kada ma wani ya Ceceta abarta ta Mutu ta huta ta saka Mamanmu kuka da Yaya,Aba ma yana kuka Saboda ita ai bata da wani amfani acikin wannan Rayuwar..! Hanne ce Jikinta na Rawa da wayar Hajiya Dake hannunta ta Kira Baba Mallam wanda mamaki ya kamasa ganin Hajiya gefensa suna Hira Cikin mamaki yace"Yau kuma Zolaya kike ji ne Abu..? Kallonsa tayi kafin tace"Xolayar mene Mallam..? Wayarsa ya nuna mata yana Fadin"Kirana akeyi da wayarki fa..! Cikin mamaki tace"To lafiya..?Wayata tana Daki ns barta fa! Jin haka yasa bai ce komai ba ya Daga Kiran kukan Hanne ya fara ji tana Fadin'Baba Kazo gidan Baba Sa"idu..Ya Jafar zai kashe Amina Duka kazo da sauri..! Baba Mallam Zumbur ya Mike Cikin tashin hankali yake tadin"Hajiya Wani abu ya sake faruwa..Muje gidan Sa"idu..! Hajiya ta fara salati Hankalinta tashe ta Rarumi hijabinta ta saka Baba Mallam na kan gaba suka Fice Daidai Anty Amarya ta fito zuwa shashen Mallan taga fitarsu Cikin gaggawa tasan ba Lafiya itama sai ta Rufa musu baya ganinsu sun shiga gidan Baba Sa"idu yasa aranta tasan ba Lafiya Domin Baba Mallam baya zuwa gidan Baba Sa"idu haka kurum wani abu bai faru ba. Cikin azama tabi bayansu Domin tana son Taga abunda ke faruwa..! Abunda Su Baba Mallam suka gani Sai da Hankalinsu ya tashi Ya Jafar yayi m Amina Dukan kawo wuka Baba Mallan ne ya karbe sandan Hannunsa yana Fadin"Jafaru ashe baka da Hankaki ban sani ba..? Ya jafar na haki yace"Baba Mallam so take ta kashemana iyaye da bakimcikinta..Shanshancinta ya wuce Tunanimku yau fa ganinta nayi a nan kofar gida Rumgume jikin wani kato Mallam..Amina fa nawa take..? Har ta gama lalacewa haka bamu sani ba..Shine kafin ta kashe su gwara ita ta Fara Binsu..! Karaf manganganun akunnin Anty Amarya Data shigo Salatinta kawai akaji Tana Fadin"Innalillahi wannan yarinyar Tabbas zakka ce..Iskancinta nata har yakai haka bawanda ya sani..? Kallinta kawai sukayi kowa ya kasa mgana Hajiya Amina ta Duka ta Rumgume jikinta Duk ya Fashe da Duka Fadi take"Jafar kayi dukan ganganci..Ba haka akeyi ba..! Mamanmu na gefe tana ta kuka ita da Zeenatu harta Jawaad Dake barci hayaniya ya tadashi ganin Dukan da Ya Jafar kema Amina sai shima ya Fara kuka..! Baba Mallam Hankalinsa ya tashi Ya kalli Jafar yana Fadin"Ina Sa"idun..? Da kyar yace"yana Dakinsa..! Baba Mallam ya wuce gaba yana Fadin"Hajiya ki taikama Mamana..Kai kuma muje Ciki..! Da haka ya tasa Jafar suka shiga Falon Aba Hajiya kuma Da Mamanmu suna Hawaye suka Daga Amina da Idanuwanta basa Buduwa Sai faman wash Wash take da kamanub kuka Kilama ya Tardagata inji Hajiya Zeematu ta kama musu suka yi Dakin Mamanmu da ita sai Lokacin Hamida da Hanne suka fito ganin Halin da Amina ke ciki suka Hade kai suna ta kuka Anty Amarya Fadi take"Ruwan zafi za"a Dafa ayi mata gashi..Allah ya kyaita bai mata karaya kinsansu in suka Fara Duka kamae mahaukata..! Hajiya taji kamar ta Make bakinta sai dai batayi mgama ba batama san ya akayi tasan wani abu na Faruwa ba domin Anty Amarya sai dai ta Fadama wani Halinta..! Ashashen Aba kuwa Baba Mallam suna shiga suka gansa kwamce kan kujera Takure yana rawan Sanyi Fadi yake"Hadiza sanyi nakeji ki sakamin bargo..! Baba Mallam ya Duka agabansa yana Fadin"Ashh Sa"idu me zan gani haka..? Yana jin muryan Baba Mallam ya Bude ya Rarrafa ya tashi Zaune yana Cijewa Baba Mallam ya rikesa Hannunsa ya kamkame yana Fadin"Baba don Allah ina so cikin Almajiranka masu karati ka Tallata Amina in akwai mai so..Bana so wunin gobe ya kare ban aurar da Amina ba..Ina jin tsorom wani abu ina Fargaba kada watarana Bakimcikinta yayi ajalina..! Baba Mallam yace"Baza "ayi haka ba kana cikin Fushi Sa"idu. Mu Tsaya mu bincika zuwa gobe zan yi mgana da Mamantawa kan yaron Dake zuwa wajenta in har ya Chanchanta zan bashi Mamana..! Jikin Aba na rawa yace"A"a Baba..N riga nayi Rantsuwan ko bayan Raina Amina bazata samu abunda take so ba..Bata isa ta fita Zakka ba..Kada ka Saurarera Nidai ko Waye ka aura mata ta bar gabana na Daina ganinta ko zam samu Saukin Abunda nakeji..! Baba Mallam yayi shuru yana kallon Baba Sa"idu ganin haka yasa ya kara Rike hannunsa sai Hawaye sharr yana Fadin"Kada kace A"a Baba Mallam Kayimin wannan alfarman a mtsayin ka na Uba gareni ka yafemin in har ahalima suna goga maka bacin suna ka yafemim..! Ya karishe Fada Cikin kuka,Da Jikin kowa saida yayi sanyi Baba Mallam yace"Kul..Kar na Sake ji..Kai jinina ne Sa"idu har gaban Abada..Kada ka Damu Zan aurar da Mamana kamar yadda ka Bukata sai dai bazan mata auran kaskasaci ba kafin waye gari Allah zai bayyanamana Mijinta mafi Alherinta aduk inda yake Sa"idu kayi hakuri kada ka aibatata kila ita irin Tata Kaddaran kenan..! Aba bai Sake mgana ba Tari ya Sarkesa kamar zai sheka Ya Jafar da Yaya suna Rike dashi yaya kuka kawai take Yadda take ji aranta baya Misaltuwa ita ta Haifi Amina Radadin da kowacce uwa take ji in Wani Daga Cikin Danta ya zama zakka..!