Sashe 36
Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammh Tundaga kan su Zubairu har ma da Mutanen gari da abokan arzuka suna wajen Sun ci abinci sannan sai aka gaggaisa aka Dauki Hotuna Saboda Tarihi. Gabadaya Iyalan Baba Mallam Fararan Shadda suka Sanya Sai illah Danmallam da ya Nazir ne suka saka Shadda mai Ruwan kasa Babban Riga da Hula Aikin hannu kuma iri Daya wannan aikin Baba Sa"idu ne shi ya Dimka musu su Hudu Cikom su Baba Mallan ne wanda ya Dora Rawaninsa kan Hularsa mai Tsana sakar yan Maiduguri wato Zanna Bukar. Angwayen kuma kowani Tawaga da nasu irin Tsarin Shigar Cikin Burgewa basu wani Dauki Lokaci ba Misalin Biyu da Rabi na Rana Motocinsu suka Fara Dawowa Kofar gidan Baba Mallam,Saboda Daukan Amran kamar yadda ka"idan take mata na cikin gida Ana ta Haraman Hada abubuwan Daya Dace kada a manta da wani abun Amaren Shashen Hajiya Babba suka kwana kuma ba"a fito dasu ba sai da aka Daura aure dukkansu sun saka Shadda Fara mai aikin Gold sannan hijabinsu har kasa mai Ruwam Gold ne da Takalmansu,ayayinda su Hajiya kuma Shaddar su mai Ruwan kasa ce suma Dukkansu har da su Mamanmu Da yaya a ka"idan Biki su kayansu iri Dayane Baba Mallam ya hana Sauya kala sannan Tundaga kan su Amina har kan su Abida shaddarsu Kalan Sararin Samaniya ce Kuma Dinkin su Duka iri Dayane da kalan aikin zaren mai ruwan zuma suma Duka Hijabinsu mai ruwan zuma Tunda saka gyale sai da su gani wajen wasu Tundaga kan na gaba dasu har iyanzu ba wani wanda har ya gama zamansa yayi aure yasan yadda ake saka Mayafi wannan Tarbiyan Baba Mallam ce Hijabinki har kasa da Safa Nikab ne bai saka musu Dole ba wacce tayi Ra"ayi ta saka abunsu. Hatta masu auran suma sum yi shaddarsu sai dai kowacce kalan ta ta Dinka. Sai bayan an gama Daura auran Angwayen sun tafi cin abinci mallam da Aba sun gama sallaman baki wajen yadan Ragu da maza kana Hajiya Babba da Hajiya uwa suka taso Amaran zuwa gidan Baba Sa"idu domin suyi sallama kowace na Lullube Cikin Hijabi tana kuka yara irinsu Amina da basa jin mgana suna Bin bayansu rii,su ya Abida kuma suna Shashen Haj.Nasara nan suka Sauke kawayen Amaran in sun zo Duk su ba wani gayya suke yi ba yawanci Duk yan islamiyan su ne sai yan Hadda ko yan makarantar Bokonsu sai Daidai kowa ya sani su kansu sun isa gayya a sha"aninsu. Dakin Mamanmu aka fara kai su bata wani Tsaya ba suma Dayake gidan yana Cike ne,addu"a kadai ta yi musu da Nasihan Hakuri kafin tace a kai su Dakin Yaya. Hajiya Babba tace"zamu bar miki Zulaihat ku kebe a matsayinki na Uwa gareta..! Mamanmu Dariya tayi kafin tace"A"a Hajiya..Ni Uwar Amina ce inda yau auranta akeyi bama sai kin ce mu kebe ba..Ammh Ai Zulaihat Diyar yaya ce ku mika mata ita Dakinta ta kara mata Fada ita da Sauran yan"uwanta..! Ana ta Dariya Kowa wannan karamcin na Mamanmu yasa take da kima a idon kowa Musamman Mutanen Gusai Dangin Aba,ba musu aka Kwashesu sai Dakin Yaya tayi musu Nasiha matuka tare da Fatan Alheri Suna ta kuka banda Sadiya kanta dai na kasa. Amina da Hanne da Zafira da Hamida suna Dakin Domin duk inda aka saka Kafa nan suke saukewa sai ana Tafiya su rika jama su ya Aisha Hijabi suna leken Fuskarsu ba wanda ma yake Lura dasu. Zafira tayi ma Amina Rada tana Fadin"Wanchan fa naga bata kukan Rabuwa da gida ne..! Amina ta kalli Sadiya kafin tace"Diyar Anty Amarya ce..Yayar Sa"adatu..Ai bazatayi kuka ba yar na gada ce..! Zafira tace"Tab wai ina ma Sa"adatun ne yau duk ban ganta ba..? Amina tace"Tana Shashensu mana .Ki bari zamu ganta ai duka za"a kaisu..! Zafira tace"Yauwa sai na kara ganin Balarabiyar nan..! Amina tayi Dariya tana Fadin"Basabam bam ba..bakauyiya..! Ita dai Dariya tayi Hamida da Hanne suna gefe suna jin duk nasihan da ake mu su ya Zulaihat Banda Amina da Hankalinta ba bashi a wajen. Basu wani jima ba Saboda Baba Mallan yace karfe uku kowacce zata mika Gidan Mijinta Gabadaya Har dasu Mamanmu da Yaya da su ya Jalela da Mutanen gusai aka Dumguma gidan Baba Mallam Dakin Hajiya Nasara suka yada Amaran itama Amtsayinta na uwa zatayi musu Fada da Nasiha,alokacin ne ya Zulfa ta hango su Amina Cikin mamaki ta tabo Jawahir tana Fadin"Jawa kalli yaran nan..? Ta kallesu kafin tace"Baki gansu ba..?ai tun dazu suna kugu da manya ko su Abida basa wajen nan sai su nayi mgana Hajiya tace a rabu dasu..! Zulfa tace"Amina ta wani juya ido..Kamar wata babba..! Jawahir tace"Ko an koresu sai Amina ta Rika Labe kamar baki santa ba..? Zulfa tace"Allah ya shirya..! Jawahir tace"Ameen. ! Su bama su san suna yi ba suna chan ta Gulmar wata Kanwar Haj.Nasara da take da kiba katuwa ce Amina na Danne Dariyanta kasa kasa tace"Chabdijam..Wayaga Him..Buhun Masara..! Tana kallonsu suna Dariya kasa kasa Sai ta kallesu sai su kauda kai ganin hakane yasa suka koma Daga kofar Shigowa suna Dariya nan ma basu Dade ba suka fita zuwa bangaran Anty Amarya,chan suka iske Danginta Na Duste har da yayin angon Sadiya wadanda zasu tafi Amarya sun zo su Sakina am ci wani Leshi mai Tsada an kashe Dauri Sarood ma ta saka Leshi iri Daya dana Sakina mai Ruwan Maroon da Kwalliyar blue gabadaya Cikin Dakij nan sai da ta Haskawa kowa yadda tayi wani kyau kamar ka ijiyeta kayi ta kallonta Masha Allah. Zafira tace"Tsarki ya Tabbata ga Allah..Amina kinga kyau..! Amina tace"Gaskiya kayan sun mata kyau..Ji Anty Sakina da ta saka Wlh kamar akuya..! Tafada tana Dariya Hamida ta Zungureta tana Fadin"Kiyi a hankali Tana kallonmu kada ta gane..! Amina na Danne Dariyanta tace"Kalleta..Sai kiba take karawa ga Gajarta kamar akifeta da kwarya..! Hamida tace"Amina ki bari..ba kyau kushe Hallitar Allah fa..! Amina ta balla mata Harara Tana Fadin"Anki a barin kabarinki Daya Dani ne..?nifa Hamida kin isheni Wlh badama ayi abu sai ki ce Amina kamar Ni kadai ce uwar Laifi..! Hanne tace"Mu dai don Allah kada ku fara wannan Fadan..! Amina tace"Gayamata ta Daina ambaton sunana..In ba Haka ba taga Tijara ganin idonta Wlh..! Hamida ta tabe baki kafin tace"Daga Fadin gaskiya..? Kuma da kike mganar Tijara.?har akwai Sauran Tijaranki da ban gani bane Amina..! Amina ta Hura Hanci kafin tace"Tab..ai baki ga komai ba Hamida..! Hanne ta raba Fadan da Fadin"Ku ga Sa"adatu chan..! Jin haka suka koma inda ta Nuna musu Daga bakin Kitchen din Anty Amarya suna ta Fito da kwalaye suna Tarawa anan Tsakiyar Falon itama Less ne ajikinta,mai Ruwan kasa Iri Daya dana Jikin Sabeeha ta gansu yasa ta zo ta wuce ta gabansu Amina ta kalleta kamar taga kashi kafin ta Mele baki tace" Aikin mur in ji tusa..! Zafira tace"Ita bata saka irin kayan ku ba..! Hanne tace"Ko Anty Amarya ai bata saka irin nasu Hajiya ba..Itafa komai nata Dabam take yi ita da ya"yanta Baki ga yawancin Danginsu da less ba kila su nasu ankon kenan..! Zafira tace"Hala Baba Malam bazai yi Fada bane..? Hanne tace"Ina ma zai Lura yana Fama da Jama"a..Kuma kinsan Hajiya ba ruwamta da wannan..Daman Anty Amaryan ne akwai kai kara da ance kace..! Amina na jinsu kafin tace"Ko Uban me zasu saka Wlh basu fimu ba..! Hamida tace"Infa..Bama zasu Fimu ba Wlh..! Anty Amarya suke kallo da take ta Dafa Duka kawunan Amaran tama ta musu Nasiha da saka albarka. Basu jima ba suka fito bayan sun bar Sadiya anan Shashen itama Ikram shashen Haj.Nasara aka maidata Su ya Abida basa nan wai sun tafi gidan ya Jafar Ya Uzairu ya tuka su zasu Dauki wasu kayan Amaran Dake chan gidan Ya Aisha da ya Zulaihat Shashen Hajiya Babba aka maidasu,Sannan Hajiya ta fice zuwa Babban Store din gidan Inda su ya jafar da ya Nasir ke jiranta aka Bude aka Fara Fito da Buhun hunan Shinkafa taci da na Tuwo sai garan kayan abinci bangaran su Taliya da Sauransu sai manyan Bombi na su kayan fulawa da Akayi ma kowaccensu. Harda da manshanu sai da aka saka ma kowacce Dukkansu garansu kowacce abu Biyu ne wani uku,Harda da su kuka Kubewa yaji,Fulawa da Sauransu kayan Kamshi Hajiya Babba ta saka su Baba Lami sun Dakasu kowacce an Dibar mata har da kayan Miya Tattasai Bushashe Tumatiri na angwangwani aka Siyan musu. Sun Raba kayan gida Hudu kowacce aka kwashe mata Daya su ya Shamsu ke Fita dasu suna Lodawa a Motocin angwayen. Hajiya Babba ta koma Shashenta ta Fito da wasu kayan Kitchen da zannuwan gado masu kyau na Saudiya,guda Biyu Daya na Aisha Daya na Zulaihat kayan Kitchen dim Biyu aka Raba duk da an siya musu wasu wannan karin ne saboda kayan aiki basa kadan,Bangaran Anty Amarya ma suna ta fito da kwalaye ita harda Nakiya suka kara ma Sadiya sai bangaran Haj.Nasara itama Danginta suna ta fitowa da wasu kayan Sai ga su ya Abida daman Tururuka suka Dauko na Ruwa da na Turaran Daki,Na Aisha da Zulaihat ne ta rika ta bama nasu sadiya ta bama iyayensu mata. Kowacce Angwayen sun zo da Danginsu guda Biyu da zasu tafi da Amarya Ya Aisha Mata uku suka zo Daga barayin mijinta Daga kaduna ya Zulaihat kuma mace Daya,Sai ya Sadiya ita gasunan da yawa tunda Abun gidane Ya ikran kuma algaita Tuni ya Cika kunnin Mutane Tawagayan ya"yan Sarki manyan uku suka zo tafiya da ita. Anriga an gama Loda Duka kayan Daga bangaran Duka Motocin guda Daya,Daya Kaduna Daya Jigawa Daya Dutse Daya kuma nan Gumel Cikin gida ma duk an gama Shiryawa Ya Rage saura Falon Malam Dashi da Aba sai Sauran manya yayyi irin su ya Danmallam da su ya Jafar Daga Falon Baba Mallam shi zai fito da kansa ya Mika kowacce Motar da zata sadata da gidan Mijinta bayan ya mata Fatan Alheri. Su Amina sun kasa sun Tsare a Kofar Shashen Anty Amarya suna Hiransu Sama sama,Jidda ce ta fito ta gansu Cikin mamaki tace"Ku kuma lafiyanku kuke tsaye anan..? Hanne ce tace"Bakomai muna sin Tafiyar Amare ne..! Jidda Tayi Dariya kafin tace"Ai Daga kan su Abida sai ku Duka Mallam ya Hadeku mu aurar daku rana Daya..Wannan fa ban gane ta ba..? Ta