← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 193

Sashe 104

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Adaidaita ta shiga yana ta Gudu da ita kamar zai bar garin gumel da ita sannan naga ya Tsaya bakin hanya inda ba yalwar giftawan abun hawa Fitowa tayi sanye da Hijabi Dogo har kasa ga Nikab a Fuskarta karamar Jakarta ta Dauko ta bashi kudinsa kafin ta fara tafiya ta mike wata Hanya tayi tafiya sosai kafin ta fara Hango ta tana zaune saman wani Dutse tana jiranta sai da ta tazo gabanta sannan tace" Aci balbal Fitilar sharri..Ko babu mai kina kai safe. Kwalba ko kin fashe da sauran sharri kibiyar ajali kike mai Ratsa rigar karfe..Madina ikon Allah gabanki Fari bayanki baki..!gaba salamun baya salamun damisa mai maida Fatar kura nama..!

Wata irin Dariya Anty Amarya ta saki Lokaci Daya tana mikewa tsaye hannu ta bama ta Tsayen suka tafa ji kake tas..kafin tace"Ban kai ki sharri ba Dayyaba..Domin ni daman chan ban taba aron Fuskar salihai ba..ke kuma fa kin fini zama kwalbar sharri..An aminta Dake kin ci Amana sannan a yarje miki kin yi ha"inci..!
Tare suka kara saka Dariya kafin ta yaye Nikab din data Rufe fuskarta sai ga Mamanmu ta bayyana..!
Cikin wani yanayi tace"Babu abunda zan ce da ke madina..Sai Allah ya Cika miki naki Burin..!
Saura kadan na gama mallakan Sa"iduna a hannuna madina kiris ya rage .!
Anty Amarya dake sanye itama da Dogon Hijabi tace"Kwarai naga alama..Ammh meyasa kika batamin Lokaci kinsan tun yaushe nake tsuggune anan wajen ina faman jiranki..!?
Mamanmu tace"sai da ya fita sannan na samu na fito daga gidam..Kinsan dai yanayin da ake ciki..Lokacin da yaya nan ne nake samun fita akai akai in nace zan shiga gidanku yanzu kuma gida ni kadai ce Hamida na makaranta ita da jawaad..Kuskure kadan zan yi sai kiga na bata komai..!
Anty Amarya tace"kiyi hanzari ina kan hanya ne..!
Ba musu ta Bude Jakarta ta Dauko Kudi masu yawa ta Damkama Anty Amarya tana fadin"Shashashan wai fa bani yayi nayi ma Amina siyayyan kayan amfani shine nayi sama dasu..!
Anty Amarya tayi dariya kafin tace"Shegiya Balaraba...!
Mamanmu tace"kul..Dayyaba nake in kika Kirani balaraba kamar kin Ragema Kwalba sharri ne..!
Tare suka kasa Dariya kafin Anty Amarya tace"Mallam fa ya fara korafin kin Daina zuwa yanzu sai dai nazo ni kadai kada ya fara Tunanin ko dan kin Samu Biyan Bukata ne..!
Mamanmu tace"ki kai masa wannan kudin na karin kudin aiki ne..Mganar zuwana kuma in zaki koma dani zamu koma nace miki nan da Sati Biyu zan je gusai bikin gidansu..Sai na Fake da Guzuma na Harbi karkasa..!

Anty Amarya tayi dariya sosai kafin ta Fito da jakarta babba ta Tura kudin aciki kafin tace"Shikenan bari nayi hanzari..bana so nayi Dare..!
Kallonta tayi kafin tace"Kwana zaki yi..?
Kai Tsaye tace"Eh in nayi Dare sai gobe zan dawo..Zuwan daman na Sakina ne so nake Mallam yayi aiki kan Umar ya koma da ita madina..!
Bana son zamanta da wannan shegiyar Yar taki..!

Mamanmu ta bata rai kafin tace"A"a fa ki bari madina..Allah ya Tsareni ni Uwar Zulfa nake da Zahra kuma uwar Hamida...!
Anty amarya tayi dariya kafin tace"Mamannu...Mamanmu ..!
Tana kwaikwayon muryan Amina aatare suka fashe da Dariya suka tafa Kafin mamanmu tace"Uwarta na kabari..!
Wani Tsari kika rakata ne ni ban kara ma bi ta kanta ba tun sanda ta bar min gidana..!
Anty amarya tace"Tsarin auran ya zo a banza ya kare a banza..Domin Sakina ta tabbatarmin ita da banza Duk Daya suke awajensa..Kinga kenan haka zata gaji da zama har mallam da Hajiya da suka kulla abun su gaji su Rabashi..Sannan nace ma mallam ya kara mata rashin kunya da Tijara tayimai ya Sako shegiya..!
Mamanmu tace"Ni kuma Daga Lokacin zan karata gaba..Bana son na kara bude ido na ganta agidan nan har Abada gidanan nawa ne ni da ya"yana..!
Anty Amarya tace"Kadan zaki jira..Burinki zai gama cika..!
Ni ce dai naga Tafiyata akwai Tsawo..Burina kawai sakina ta samu Ciki ta Haihu in hakan ta Faru kamar na gama cika duka Burina ne..!
Mamanmu tace"Kema lokaci kadan ya Rage..Dukkanmu wahalar mu bazata tashi a banza ba..!
Anty Amarya tace"Tabbas..Domin bazan gaza ba..Sai naga abunda ya Turema Buzu nadi..Zan tafi yadda ake ciki zan kiraki..!
Mamanmu tace"Ki sanar da mallam Sa"idu ya fara zuwa hannu..Ammh ina so ya zama ni nake fadi yana amsani..
Anty amarya tace"Kamar yan amshin Shata kenan..!
Gabadayansu dariya suka saka kafin su tako atare har bakin Titi kowacce Adaidaita Dabam Dabam suka hau Daya ta koma cikin gari Daya kuma ta Mika hanyar tashar garin na Gumel..!

_SHIN KINA DA LABARI AKAN HAƊIN SABAYA KOKUMA IN ƘARA MIKI BAYANI AKANSA DOMIN WANNAN HADIN INGANTACCE NE BA IRIN WANDA KUKA SABA AMAFANI DASHI BANE_

Shi wannan din SABAYA COCONUT FLAKES ne, duk wani hadi da ake nema na gyaran jiki akwaishi aciki duka hajiyata, naturally zaki cicciko babu abubuwan illa aciki.

*Ina ƴan mata da zawarawa kai harma da matan Aure? To ku matso kusa ga Sabaya wanda akayi hadinsa da coconut flakes kuma kun san kwakwa ba karamin taka rawa yake wajen gyaran jikin 'ya mace ba, SABAYA COCONUT FLAKES zai taimaka wajen ciko da duk wani lungu da saƙo na jikin mace, ta dawo mul-mul da ita tamkar jinin ƴan Chadii.*

*yana sa ƙirjin mace ya ciko sosai, idan ma ƙirjinki a kwance yake sabaya na iya miƙar dashi ya koma kamar na buduwar ƴar shekaru sha 18. Duk wannam aikin na SABAYA COCONUT FLAKES ne shi kaɗai 💃💃💃, bayan haka yana ƙara ni'ima a jikin mace gamida ƙara mata ɗumin jiki. Ga matar Aure kuma yana ƙara mata juriya wajen gamsar da mai gidanta cikin sauƙi. Tareda ɗorewar nishaɗin su gabaɗaya.*

*Hajiya maza ki nememu don ki mallaki SABAYANKI, don kema ki zama mace mai aji kuma ƙasaitacciya, karki yarda ki zauna yarkace-yarkace kamar kin fito gidan Yari😂, Gyara shine Mace Hajiya, idan bakya gyara jikinki sunanki mata maza, ko kuma in kiraki da suna wadda ta rako mata duniya Kawai🙅‍♀️*

*_Domin niman ƙarin bayani ku tintiɓeni kai tsaye ta wannan lambar:_* +234 706 548 1260 *_Muna tura kayan mu ko wani gari da zarar kinyi order

💃. Kuma duk akan farashi mai Rahusa🥰

muna maraba da masu siyan daya ko sari..mungode sai kunzo🙏

07065481260

*Janafty*
[11/3, 2:06 PM] Sweet sis: *TFZB2004*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*

BAYAN KWANA BIYU.
Chapter 104 · 0% Book details