← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 193

Sashe 176

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

kara Nisan kwana..! Kawai sai yaji kamar yasaka kuka Baba mallam ya kariso ya rumgumesa yana Buga bayansa Kafin ya Dagosa yana faman share masa hawaye yakuma ja Hannunsa suka fice Daga Falom aka Bisu da kallon Tsausayi da kauna. Su ya jafar ma suka mimmike da su Aliyu jiki duk a sanyaye Ya Danmallan ne ya isa wajen su Hanne yana Fadin"Noor ki bar wannan kukan kinga fa bake kadai bane..Sake su..Ku saki juna hakanan..! Jin muryansa yasa suka saki juna suna kuka Sai suka basa Tsausayi sai ya fara rike hannun Amina sannan ya rike na Hanne da Hamida ya jasu har gaban Hajiya yana fadin"Hajiya ki yi abunda kika saba..! Don Allah kice subar kuka in suka bari Noor zata bari itama..! Hajiya tayi mirmishi ta Karbi Hannun Amina kafin ta karbi nasu hanne Hajiya Nasara tataso ta karbesu tana Fadin"kada ka damu Danmallam bazasu kara kuka ba Insha Allahu..! Ya kalleta kansa na kasa kafin ya juya yabi bayan su Nasir da suka fice tun dazu. Aka bisa da kallo sha"awa irin su Anty Amarya kuma sai kunci da Nadama mara amfani. Hajiya ta tasa su Amina Cikin Dakinta ta Kira Yakaka dasu Aisha tace su lallashe ita kuma ta koma Falo tace a kwashe kayan Amina akai Dakinsu Hanne.. Yan gusai kuma suka koma gidan Aba suma da su ya zulahait domin Hamida ce kadai tare da su Amina Su ya jadwa ma suna Shashen Hajiya suna faman kuka su kuma sai suka koma gida suka Hada kai suna ta kuka ya Zulfa da ya Zeenatu da ya Zulaihat sai yaya Zahra bamai lallashinsu su kansu yan gusai sai Tofin Allah tsine suke yi ma Mamanmu. Kamar wasu marasa galisu haka akayi banza dasu Haj.Uwani ta fara rarrafawa ta Fice cikin kunya da kuka sai Anty Amarya da ta fita tana kuka sai Mamanmu kallo arziki ba wanda ya kara yi musu har suka shige shashensu Daga Anty Amarya har Haj.Uwani Datse shashensu sukayi suna ta kuka ita Anty Amarya ba yan"uwanta duk suna asibiti wajen Sakina da tayi bari ita kuma Hajiya uwani Daga ita sai Umaima dake kwance batasan meke faruwa ba su Nazifa bata san ina sukayi ba,Bata Tunanin ma zasu nemeta nan kusa. Mamanmu kuma fakaitan idon mutane tayi ta shige Dakinta chan kurya tana kuka saboda yawanci bakin suna Dakin yaya ne yaran kuma suna Dakin su Amina kowacce tana Ciki tana Dirzan kukan nadama da nasani da kuma rashin madafa Daga mallam har Aba basu ce musu komai ba ballatana su san ina matsayinsu.! Su Amina kuwa Dakyar suka Daina kuka suka koma ajiyar zuciya.Yakaka tayi ta kokarin Lallashinsu. Sannan su kansu ya Jadwa sai da Hajiya tayi ta musu nasiha suka Saurara sannan Hidiya matar Nazir da Aliya matar Aliyu na tare dasu ita duk ta tsorata tasan tana da Zafin kishi ammh bata san Bin malamai ba..su matan su ya Jafar ma suna nan tare dasu Sarood Hajiya Nasara ta kaita Shashenta Hayaniya ya saka mata Ciwon kai,su fatima na Tare da ita suma duk jikinsu yayi sanyi sun kara Godema Allah Daya tsare imanin Mahaifiyarsu domin ba wayau bane kuma ba Dubaransu bane. Su ya Danmallam kuma suna Shashen mallam,shi da Jafar da Nasir sai Nazir,Aliya su shamsu dai suna Dakim su Nazeem sun kulle kansu Nazifa dai Ta koma Shashen Hajiya Nasara bayan sun gama kukan nasu. Su kansu zaman jugun jugum duk Dauriyan mallam Lamarin ya tabasa shi da Aba sai dai yayi kokarin nuna komai ba komai ba sabida Aba da su ya Danmallam. Mganar Daurin auran gobe suka Tattauna Daganan ya Sallamesu dukkansu ba wanda yayi kokarin komawa gidansa duka nan suka kwana Har Aba da su ya Danmallam shi da Aliyu da Nazir a falon mallam kamar kwanan zaune ma sukayi su ya Nasir ne da Jafar suka kwana Dakin samarin gidan su Akilu da suma Jikinsu duk yayi sanyi har garin Allah ya waye ba wanda ya saka wani abu acikinsa ko su kansu matan sai da Hajuya tayi ta Fada ne suka sha Tea har su Amina. Mazan kuma da Safe kowanne ya koma gidansa Ya Danmallam shi da Aliyu da Nazir gidansa suka tafi suka natsa kafin Lokacin Daurin aure kowa kagani ba walwala. Ammh Danmalam bai tafi ba sai da ya leka Amina ya tabbatar da ta daina kuka sannan tana Lafiya. Chan gidan Aba ma haka aka tashi Goggo Husai ne tazo ta zauna dasu Zeenatu tana nuna musu suyi hakuri Laifin Balaraba bazai shafesu ba su yi Hakuri Bikin kanwarsu ake yi to da hakane suka samu suka karya da Safe har suka Dan saki jiki Mamanmu kuma bana wanda ya san tana gidan ballatana abi ta kanta ta kwana kuka ta kasa fitowa ta zama mujiya yau gashi Bikin data cima burina ne ake yinsa ta zama kamar mujiya Cikin mutane. Haka ma bangaran Anty Amarya ita Kadai kamar mayya ta gaji da kiran wayoyin su Jidda sun ki Daga kiranta Har ta A"i taki Daukan wayanta ballatana taji wani Hali sakina ke ciki ta rasa ina zata saka kanta taji Dadi har Sabeeha bata nan sun tafi da ita. Hajiya Uwani kuma kafin Safe har ta Rame saboda tashin Hankali sannan tayi ta kiran Batula bata samu ba tana so ta Sanar da ita komai fa ya Tsaya. Alokacin Datake kiranta ita ta kama Hanyar Minna domin taje ta aiwatar da gudurin Uwani bata sani ba,Ajalinta ne yake kiranta. Domin sun fita Tsafe ba Dadewa suka samu Mummunan Hatsari da yayi Sanadiyar rasa rayuwakan mutum Hudu Dake motar har da Batula aciki..!
Chapter 176 · 0% Book details