← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 193

Sashe 8

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Achan gidan Baba Malam kuwa Shamsu ya Kira yace yazo yana son ganinsa ba Dadewa sai ga Matashin Saurayin ya shigo,Dogo ne mai Kaurin Jiki Kadan yana da Haske ba sosai ba Yana Shigowa ya Duka ya gaida Malam da Hajiya Suka amsa mai Cikin Sakewa Hanne ta gaisheshi ya amsa yana Hararanta Tunda ya gansu yasan Su suka saka aka tadosa Amina kuwa kanta na gefe aranta tace"Yasin bazan gaishe shi ba..!
Tafada Har tana Murguda baki Baba Mallam ya kalli Shamsu yana Fadin"Me kake yi sanda na Kira ka Alarammah..!?
Daman haka yake kiransa Saboda Mahaddacin Qur"ani ne sosai.
Kansa na kasa tace"Ina k'arama zubairu da Akilu karatu ne Baba..!
Dan Mirmishi yayi kafin yace"Dakyau Alarammah..To kafin ka koma ka cigaba da Biya musu karatun Ina so ka Raka Mamana gida sai ka Tabbatar da ta shiga gida sannan ka dawo..!
Kai ya gyada aransa yana fadin sai ya Daki bakin yarinyar nan ko gaisheshi batayi ba sannan ga Jiranta datasaka yau sukayi a makaranta tatafi gantalinta ga kuma Tasosa da ta sa akayi Duk sai ya famshe ajikinta.
Baba Malam ganin yayi shuru bai ce komai ba yasa yace"Kana jina ko..?
Kai ya jinjina yana Fadin"Naji Baba..!
Amina ya kallah yana Fadin"Tashi kuje Mamana..Sai da safe kenan ko..?
Mikewa tayi tana Gyara Hijabin Jikinta Tana Fadin"Baba sai da safe..Hajiya sai gobe..!
Tare suka amsa mata da Fatan Allah ya kaimu Baba Malam ya kalli Hanne yana Fadin"Rakata mana Hannatu..!
Tanajin Haka ta Mike suka Fice Shamsu ya Rigasu gaba suna Fitowa suka gansa yana Tsaye yana Jiransu Fuskarsa ta Hade kamar bai taba Dariya ba.
Hanne ta makale bayan Amina tana Fadin"Ya shamsu..Wlh Fuskarsa ba Rahma..!
Amina tace"Dillah sai me..?mala"ikan Mutuwa ne..!
Kwas...!
Bata sani ba kawai sai ji tayi wani Rankwashi ya Ratsa kanta Bata gama Dawo Hayyacinta ba taji an ja kunnenta an murde Cikin muryansa yace"Wato ba mala"ikan mutuwa bane ko..?zaki gane baki da wayau..!
Yafada yana kara sakar mata rankwashi kanta da Dafe da hannu Daya tana Fadin"Occh..Ya shamsu kunni na..?
Da bakinsa yace"Shiii..Yana kallon Falon Baba Malam,Hanne ta fara baya Baya tana Murza ido Amina ya Sakarma Kunni yana Fadin"Oya wuce muce..Wannan na Farkon na Jiran da kika sa mukayi yau a School ne..Akwai na Kin gaisheni da kuma Tasoni da kika Saka Baba Malam yayi..Wuce muje..!
Yafada yana Tura kanta gaba Ta wuce tana Dafa kanta Cikin kunkuni take Fadin"Allah ya isa na mugu..!
Shamsu da karfin ji kamar maciji Kallonta yayi yana Fadin"Me naji kince Allah ya isa Amina..?
Da Sauri tace"A"ah fa..Cewa nayi Allah yayi maka albarka..!
Mirmishi yayi yasan Allah ya isa tamai ammh Tunda ta nuna Tsoronsa yasa ya kyaleta Hanne ya kallah da Sauri ta Juya zata koma ya Kira ta ta dawo Kafin tayi mgana ya Tasa keyarta zuwa gaba yana Fadin"Ina zaki..?kema wuce muje..Duk tare kuke daman sai Hali yazo Daya ake aBota..!
Har yana gwara kansu,Kafin yakai su kofar gidansu Amina sun Sha Rankwashi kamar kansu zai Cire Daman ai ya iya Rankwashi baya Dukan Bulala Murdan kunni Rankwashi da Iza keya a kofar Gidan ya Tsaya ya Tura get din yana Fadin"Oya to a shige..!
Amina ta shige tana Hararansa ta kasan ido,Hanne tayi Saurin cewa"Ni gida zan koma..!
Hararanta yayi yana Fadin"Ina..!nan zaki kwana tunda kika zo shiga.!
Ya Tunkudata ya Rufe get din ya Juya yatafi Amina ta kalli Hanne tana Sosa kanta tace"Wlh Gidanku Duk mugaye ne Hanne..!
Allah ya isa bamu yafe ba..!
Hanne na Sosa kanta tace"Kaina Zafi yake ya iya rankwashi fa Amina..!
Amina tace"Insha Allah sai ya samu mai mai mafinyinsa..!
Hanne Dariya abun ya bata Amina Tayi gaba Tana Fadin"Alqur"an ban yafe ba Har kabarinsa na Balbali da Wuta..!
Hanne sai kanne Dariyanta take har suka iso Tsakar gida ko"ina Shuru sai Hasken Inji Dayake an kunna Tun Dazu Hanne tace"Kowa yayi barci Amina..Da ma agida mukayo kwanciyarmu..!
Amina ta balla mata Harara kafin tace"Bafa nayi niyyar kwanan bane..!
Daga haka ta wuce Dakinsu Hanne tabiBayansu.
Aba Dake bakin Kofarsa ya Sauke ajiyar rai kafin ya Fito Kai Tsaye Kofar Gidan yaje ya Rufe da Kwado kafin ya Dawo yana Dudduba Tsakar gidan,Shi ya Rufe Kofar Kitchen din kafin ya Shige Dakinsa ya Rufe Yau Mamanmu keda shi yasa Tun dazu Yaya ta shige Ciki ita da Jawaad.
Hanne da Amina sukayi mukus da sukaji Motsi Amina na mata Rada akunne tace"Aba ne ya fito..!
Hanne ta gyada kai basu wani motsi ba sai da sukaji Shigarsa Dakinsa Sannan Ya Zeena tayi barci ita da Hamida Ya Zulaihat ne batayi ba tana Karatu Saboda suna gabda fara Jarabawar Fita.
Ta Dago ido ta kallesu Hanne tayi Saurin gaisheta ta amsa kafin ta maida kanta tana Cigaba da Karatunta Amina ta karisa wajen gadonta tana Fadim"Ji Hamida tayi barci..Hanne tasheta..Yasin da ita zamu Hirar nan..!
Ba Musu Hanne ta Daketa sai gata tatashi Hanne tace"Tashi mu yi hira..!
Hamida tayi Tsaki kafin tace"Uban Hiran gobe fa muna da Hadda kun sani..!
Amina na Kwabe kayan ta tace"Hanne kizo ki Saka wannan Rigar..Ke Hamida Sarkin karatu Badai kin iya Haddar ba..?Hanna ma ta iya ba shikenan ba..!
Hamida na Hamma tace"Ke fa Amina..?
Amina na Dariya tace"bala"i ai ni na manta inda nike ma..Kamar Cikin Suratun Khafi ne ko..?nifa inaga Tun Sati Hudu daya wuce Malan Amadu bai karbi Haddata ba ni Tunda Ranar nan ban kara Bi ta kansa ba..!
Hamida da hanne suka kalli Juna kafin Hamida tace"Kinsan Bulala goma ce..!
Amina na Hawa kan gadonta tace"Shine me..?yayi ya gama na Kakkabe jikina..!
Tafada tana Dariya Hanne Zatayi mgana Amina Taja Bargo Tana Fadin"Malama Hanne ki adana wannan wa"azin naki zuwa gaba wajen Amina bamai amfani bane..!
Suna jin haka suka kyaleta Hanne ta Cire kayanta a Tiolet ta Sako Rigar Barci akwai Gado wanda ba kowa kai Saman na Ya Zeena Daman nan take kwana in tazo ta Haye tana Fadin"Uncle T ya baku Assigment Amina..!
Amina tayi Tsaki kafin tace"Kila ya basu ni ina na sanin musu.!
Au kice Uncle Gajere yana Tafiya kamar Dan kaciya..!.
Sai Tasa Dariya Zulaihat ta Dago Dagachan kafin tace"Amina Dare ne fa..?sannan Tsakaninki ga Allah Uncle T din ne mai Tafiya kamar dan kaciya..?
Da Sauri Hamida tace"Ya zulaihat kalli yadda Duk Unity ake Fadin kyansa da ajinsa..Ammh Amina Tsinarsa take..!
Amina Dariyanta ta Rage tana Fadin"Ku Anty Sara mai Warin maza..!
Don Allah kuna jin warin in tazo kusa da ku..?
Hamida da Hanne suka kalli juna ya Zulaihat kuwa cewa tayi"Hamida Kashe mana Hasken Dakin nan nagama karatun..!
To ai tasan Tunda Amina ta shigo to ta Daina Fahimtar komai kenan.
Hamida ta mike ta Sauka tatafi Rage Hasken Dakin Hanne ce tace"Amina kiji Tsoron Allah duk Unity wa yakai Anty Sara gayu da kamshi..!
Zulaihat ta tabe baki tana Fadin"To a ina ma tasan kalan warin maza Hannatu..!
Amina tace"Tabdijam..To wlh warin kashi take duk wannan Uban Turaran datake sawa da kaje kusa da ita kake ji..Wai baku taba ji ba..?ku Tsaya Harda Warin bakin Sir Gumel ma baku Taba ji ba..?
Gabadaya Salati suka saka Ba Hamida Data Kulle Kofarsu ba Hatta Zulaihat Datace"Amina Sharrin naki Harda Principal..!
Bakinta ta Danne tana Dariya Hamida Da tadawo zata kwanta tace"Kibar mganar nan Amina kada kije ki Fadeta a makaranta ya koma kunnensu..!
Amina tace"Sai me..?karshenta kenan Suppention Amina Saidu ta samu freedom ni daman suji Wlh a koreni Gabadaya..!
Ba wanda ya kara tankata ita kadai ta Cigaba da mgana sanin Halinta Duk mganar data Fada har ranta take Nufin haka din.
Zulaihait ne ta gaji tace"Ki kama mana Bakin ki anan wajen Amina ko in na taso kika ga yadda zan yi wurgi waje Haba..Muna so muyi barci kina Hanamu..!
Tafada Cikin bacin rai Amina ta Tura baki cikin kunkuni tace"Mutum dai ya Kusa aure ya bar mu mu shakata..!
Tana jinta batace mata koma ba Indai ta Biye ma Amina sai Su Aba sun fito sun jisu Domin bakinta bazai yi Shuru ba.
Chapter 8 · 0% Book details