← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 193

Sashe 80

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda aka Tsaida Lokaci ya Abida da ya zeenatu suke ta rama atsaye sai wuya da ido kowa yasan sun fi Damuwa akan sauran da aka aurar duk sun yi sanyi barin ma ya Abida dake da Zakewa ammh yanzu ta koma Ruwan sanyi,Ko su Amina sai sun gaji da Tsokanarta sun kyaleta bata ma bi ta kansu kamar baya ballatana ya Zeenatu daman bata cika sakar musu ba Sai dai tafi ma ya Zulaihat sakewa da Mutane da Sakin Fuska..!
Ana biki Saura kwana goma Hajiya tace aje ayi jere kaduna Na Abida sai ana gobe Daurin aure Haj.Uwani zata tafi ita da ya Aisha su hadu da su Zahra su yi jeran kafin Amarya ta kariso..!
Masu tafiya jeran ya zeenatu Anty Amarya ce sai Haj.Nasara sai matan Ya Nasir da ya Jafar shamsiya da Fadila suka tafi kano suka kwana Daya daman already kayan dakin sun isa kaduna Washegari suka wuce suka ma Zeenatu jere a gidanta mai kyau da tsari,Anan gidan suka kwana Har da Jidda sai da Safe suka shigo Motar Haya zuwa Gumel ya Jidda ta hau ta kano..!
Tuni shiryen shiryen ya cigaba da Tafiya ta kowani bangare Amina ta fi kowa Murna ganin Ya zeenatu zata tafi ta bar musu daki daga ita sai Hamida in taga hanne na Damuwa Dakin Hajiya bakowa sai ita kadai Dariya Amina ke mata tana fadin"Ke fa banza ce..Bama kiji Dadi ba Daga ke sai Hajiya ki sha Shagalinki.!
Sai hanne tace"Kadaici zai dameni Amina..!
Sai Amina tace"Sai ki dawo gidanmu da zama ko Hamida..?
Sai Hamida ta gyada kai hanne baki take turawa tace"Uhmm kema waya sani ko daga nasu Bikin sai naki Amina..!
Aranar da Hanne ta fadi haka sai da suka kwana Amina bata mata mgana ba Tana Fushi da ita Sai da Hajiya ta shiga mganar tayi Sasanci Ta kalli Hanne tace"Ki bata Hakuri hanne..Ko ni ce mamah haka zam miki Fa..Ai sai naga kamar kin gaji dani ne kin kosa na tafi..!
Jin haka yasa Amina ta Sassauta Fushinta tace"Hajiya hakane fa..Kamar ta gaji dani..Ni ba inda Zani ina nan tare daku ko Hajiya..?
Ta fada idonta na tara maikon Ruwa Hajiya na Danne Dariyan tace"Da yardan Allah ma kuwa..!
Da sauri Amina tace"Yauwa Hajiya..Mun shirya..!
Tafada tana kallon Hanne har da bata Hannu suka kulla Hajiya na Dariya ita da Hamida harda ya Abida Dake falon acikin ranta tana auna yadda zama zai gudana Tsakanin sanyi da Miskilanci da Dattako da kuma Masifa da Jidali da Rashin kunya awaje daya Lalle akwai kallo kuwa..!
Su Amina wannan karon kansu yayi girma saboda su,su Abida suka sanya akan abunda za"asu raba wajen Walima su ka fara Bude Hanci suna Daga kai suma sun girma ba yara bane Tunda ana sakasu a sha"ani ba yan aiki aka maida su ba kamar baya..!
Tare dasu akayi Donot da Samosa da Dublan din da za"a raba agidan su ya Jafar suka hadu da su Anty Shamsiya,Sai kuma abincin da za"ayi aranar,waina kuma Gida za"ayita Mamanmu zasu yi da bakin gusai in sun iso Hajiya kuma ita tayi abun Rabo na Amare mug din shan Tea da Maficai da kofuna sai Jaka mai kyau Haj.Uwani tayi Key holder na Rabo Haj.Nasara kuma tayi robobi masu Murfi Dauke da yaji aciki Anty Amarya tayi Turaran wuta,Ta shiga Bikin sosai bata koma baya ba komai da ita ake yi har Amina na gulma Saboda Sakina take wannan Shigewar har sa"adatu wannan karon bata ware kanta ba Haka Anty Amarya tace mata Kada ta ware cikin yan"uwanta duk tsiya suna Tare bata mgana da Amina itama bata mata sai dai su yi mgana da Hamida ko Hannatu..!
Bangaran Kayan da amare zaku saka Baba mallan ya bama Hajiya Komai a hannunta an dinka musu kala uku uku Less Daya amtafofi Biyu masu kyau da Tsada sai Dogayen Riguna bakake guda biyu sai aka Dinka musu Hijabai Farare har kasa na walima sannan kuma ta Dinka ma su Amina Atamfa da Hijabi fari sai kuma su Matan Baba Maallam din suma Atamfa ce iri Daya harda Mamanmu na Fitan Biki kamar yadda aka saba Allah Sarki ba yaya da komai tare ake yi musu..!
Biki ya rage saura kwana uku Ranar agidan ya jafar suka wuni har Dare suna yin meatpie din da za"a saka a Takeway,a kasa suka tako zuwa gida Tunda duk ba mazan gidan ya Shamsu yana Dutse ya jafar kuma basu dawo ba Akilu ne da Zubairu kuma Baba mallam ya hana su Daukan Mota!
A kofar gidan Baba Mallam suka hangi ya jafar da ya Nasir da Aba awaje suna mgana sai wani mutum basu ganesa ba,Gabadayansu gidan Aba suka shige,Har da Sa"adatu su ya Zeenatu ne agaba su Amina na baya sai da suka shige gidan sannan Amina ta jawo Hannun Hanne suka koma baya zatayi mgana kenan ta Rufemata baki sai da suka Shige korido kana ta Saki bakinta cikin mamaki Hanne tace"Menene wai..?
Amina ta Tabe baki kafin tace"Ke baki ga sa"adatun nan bane..?
Sai wani shigemana take yi yanzu..?

Hanne tace"To ina ruwanmu..Daman mu bamu gujeta ba itace ta janye jiki Damu Tunda yanzu kuma ta Dawo shikenan..!
Hararanta Amina ke yi har ta gama mgana kafin tace"Sai gamu marasa zuciya sai mu biye mata..?Kune naga kuna mata Dariya ni ko kallo bata isheni ba wato taga yanzu mu ba yara bane muma mun girma Dole ta shigemana..Ni gaskiya ku sallameta in kuna son na rika Binku keda Hamida..!
Ta fada har tana yarfa Hannu,Hanne tace"Ko bakomai ai yar"uwarmu ce Amina..Naka ai sai naka..!
Amina tayi karamin Tsaki kafin tace"Yar"uwarki dai ni ban hada komai da ita ba .!
Hanne ta rike baki tace"Ehye..?in dai kuwa Kikace baki hada komai da Sa"adatu ba nima baki Hada dani ba Domin Uban mu daya da ita..!
Amina tace"Ke dabam ita dabam..In kuma kin Dauka hakanne to haka din ne..Ni fa Hanne basai kin min gorin Sa"adatu yar"uwarki bace ni kuma bare ce.!
Hanne ta saki baki kafin tace"Yaushe nace miki bare Amina..?

Cikin kufuluwa tace"Bansani ba..!
Tazo zata wuce fuu Hanne tace"Da kike mganar yar"uwata ce..To in dai baki karbi gaskyan Sa"adatu yar"uwarki bace ita din kanwa take gareki..!
Sai alokacin Amina ta waigo Cikin wani kallo tace"Kanwata ta gidan uban wa..?
Kai Tsaye hanne tace"Kanwar MIJINKI ce..Kanwar ya Danmallam ne ai shi bai isa yace ba kanwarsa bace..!
Amina taji kamar ta Tsinke hanne da Mari sai kawai taja Tsaki mai girma kafin tace"Sai dai kanwar Ubana bata Miji ba..!
Daga haka ta wuce afusace ta bar Hanne na rakata da Dariya Tayi Tsaki yafi sau goma in ta Tuna da Abunda Hanne tace shiyasa suna shiga Dakin mamanmu taga Sa"adatu kwance kan kujera ta Fara sakin tsaki tana Fadin"Ni fa bana son shisshigi..Abaya an nuna kai da banza duk Daya sai yanzu kuma azo ama wani Haba Haba dakai..Munafunci ne bana so..Kowa yayi ta kansa..!

Take fada tana Hararan gefe ya Abida na Dakin kuma tasan da Sa"adatu take itama Sa"an tasan da ita take yi ammh bata nuna ba Tunda abun nan ya Faru na wattanin baya Anty Amarya tace mata ko musu ta sake yi da Amina sai ta sani ammh yarda ta Tsani Amina ko Hanya bata Kaunar ta hadasu sannan karin bakincikinta da taji labarin auran dake tsakaninta da ya Danmallam Haba ai ba"a duba ba ba Sa"anta bane sannan Anty Sakina tafi karfin ta Hada Miji da Amina don ma Anty Amarya ta kwabeta da kame bakinta da kanta cikin mganar ne da yau sai Amina ta raina kanta maimakon haka sai ta nuna kamar ma bataji ba ya Abida ce ta tanka Tunda tasan Halin Amina cikin Fada tace"Amina ki mana shuru..Wlh bazaki Fara mana jidalinki da Daddaran ba..In kuma kika ki wlh bar ganin na yi sanyi yanzu sai mu Taru mu nada miki na jaki..!
Amina ta Hura hanci kafin tace"Mu ta kanmu kowa yayi ta kansa..Dariya ba fa so ba mai hali bai bari ba.!

Cikin waka take fada tana nuna Sa"adatu da baki ya Abida sai ta kasa mgana gashi mamanmu bata Dakin tana Tsakar gida wajen su hanne.
Amina cigaba da wakarta tayi tana fadin"Takun yayi..Wasu sun saki Reshe sun kama ganye...Warrrr..!
Sai ta watsa ma Sa"adatu hannu data juyo tana kallonta sai ta Daga mata ido ta Juya kafin ta fice ganin ya Abida ta Biyota ta gudu ta fice tana Dariyan Shakiyanci Ya Abida ta kada kai kafin tace"Kai Amina sai fatan Allah ya shirya. ya Danmallam zai sha fama..Sa"a kiyi hakuri kin ji ko..!
Sa"adatu tayi wani munafukin Mirmishi kafin tace"Bakomai ya Abida..Amina yar"uwata ce kuma haka take..Kinga tunda musan Halinta sai muci mganin da zama da ita kamar yadda su hanne sukayi..!
Ya Abida tace"Yauwa Sa"adatu na..!
Dariya kawAi tayi tana son ya Abida bata da Damuwa sam kaf cikin ya"yan Hajiya Babba da Hanne ne basa shiri itaama Saboda Amina ne..!
Abida aranta tana Tunanin ina Amina ta iya wakar nan su da ba waka suke ji a agidan ba,Abunda bata sani ba a wayar kawarta Zainab Amina tasa wakar Warr.
Agidan zasu kwana shiyasa suka Firfito waje ana Hira baki sai gobe zasu fara sauka ya Aisha ma gobe zata iso ita da ya Jamila da ya zulfa"u duk agoben zasu iso ya Jadwa ne bazata zo ba jamila da Jawahir ne kadai zasu zo har ya jalila bazata samu zuwa ba abun yayi kusa kusa da Rasuwar Yaya da suka zo Baba mallam ne ma yace duk suyi zamansu sai nasu Hannatu saboda kada Zirga zirgan tayi yawa .!

******
Chapter 80 · 0% Book details