← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 193

Sashe 115

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ita kuwa mamanmu Rana Tsaka kawai hanne tazo tace Hajiya tace ta bada Sako zasu wajen Amina..
Ita har ga Allah mantawa ma take da wata Amina kudi kuma tabi ta kansu  Shiyasa ta Dauko wannan Turaran Tsinke wanda mamata ma ta bata shi ya Dade bata taba amfani dashi ba tamikama hanne domin bata taba Zaton Sa"idu yayi zencen ya bata kudi da Hajiya ba. ganin suna ta Murna yasa batace komai ba gwara Hamidan taje ta gano wani irin Halin da Amina ke Ciki don ta tabbata Sakina bazata mata wasa ba ita fa a gayyas gida yanzu ya Rage daga ita sai mijinta Jawaad yanzu in Aba ya Dawo yadaina zuwa saboda samunsa tayi tajamai kunni yaro kuma da Tsoro ko Aba ya Dawo ko ya kirasa daya zo sai yace yana da Homework sai ya tafi hakan yafi ma Mamammu Duniyarta take so taci ita kadai bata san Takura.

*Janafty*
[11/3, 2:06 PM] Sweet sis: *TFZB2008*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*

Amina tana rakube a falo tsoro duk ya cikata tunda Danmallam ya fita take duban idon su hanne ammh har Dare ya fara shiga ana gabda kiran sallar mangariba bata gansu ba Tsoronta Allah kada Dare yayi basu zo ba bazata iya kwana ita kadai ba Tana jin tsoro.
Tana zaune kan kujera a rakube saman kujera tana fiki fiki da ido,kamar mara gaskiya ko kwakwaran motsi bata yarda tayi ba, saboda tsoro,Saboda yanayin Datake ciki yasa ko karan Bude get bata ji ba sai ihun kiran sunanta da Hanne da Hamida suke mata kamar daga sama haka taji tana kyalla ido kawai taga Hanne da Hamida da kaya niki niki a Hannunsu,bata san sadda ta Diro daga kan kujera ba duk da yanayin Datake ciki bai sa ta tsaya ba Cikin Farin ciki da murnan da Rabonta da tayi har ta manta ta fada Jikin Hanne Tana Fadin"Oyoyo..oyoyo..!
Haka take fada sai hawaye sharr kafin ta Saki hanne ta Rumgume Hamida tana Fadin"Nayi kewarku..Nayi kewarku ba adadi Hanne da Hamida..!
Ta fada tana sharan kwallah suma sai da kwallar ta kawo musu suka kara Rumgumeta suna fadin muma mun yi matukar kewarki Amina.
Hannunsu taja tana fadin su kariso mana Bakinta yaki Rufuwa Saboda Murna basu Tsaya a falo ba sai Dakin Data kan gadon suka yada Zango Hanne da Hamida suna ta bin Gidan da Dakin da kallo.
Amina Murna yasa ta rasa me zata basu kallonsu tayi tana fadin"Kuna jin yunwa.?
Ga Abincin chan da ya danmallan ya siyomin kafin ya tafi zaku ci na Dauko muku..?
Binta kawai suke da kallo har ta Fice sai gata ta Dawo da shi a Hannunta Hade da maltina,tana shigowa Hamida tace"Mufa mun koshi Sai dai anjima..!
Amina ta Dago tana fadin"Hanne kema bazaki ci ba..?
Hanne tace"Mun ci abinci agida..Sannan ni ba abincin siya zan ci ba girkin Amarya Amina zan ci..!
Hararanta Amina tayi kafin tace"ai sai ki ci abinci bayan matar gidan ta Kulle Kitchen dinta ta tafi bansan inda taje ba..!
Hamida ta zaro ido kafin tace"Bangane ba..?
Hanne ta karbe da cewa"Naji Hajiya na Fada ammh inaga ya Danmallam ya mata mgana ga keys din gidan gabadaya na wajen Hajiya tace nazo miki dashi..!
Amina ta tabe baki batayi mgana ba, Hamida da Hanne sai binta suke da kallon kurillah Amina sai ta Tsargu ta balla musu harara kafin tace"Wai kallon fa na miye..?
Hamida ta kalli Hanne suka Tsintsire da Dariya Amina sai ta sha kuni Tana Fadin"Bana son munafunci hanne da Hamida..!
Hamida tace"Ba wani gulma munga kinga sauya ne Amina kin rame sannan kinyi wani sanyi kamar bake ba..Eye Amarya Amaryan Ya danmallam to ya amarcin ne da Dadi ko ba Dadi..?
Amina sai Hararanta take yi kafin tace"Sai dai ango..Sannan ba Amarci ba amaro..!
Gabadayansu suka saka Dariya Farimciki ya cika Amina bakinta yaki Rufuwa Hanne ce tabi Dakin da kallo kafin tace"Dakin waye wannan hala..?
Amina tace"Na Sarood ne..!
Hamida tace"To ba kayanta a Dakin ne..?
Amina tace"Dillah kun isheni ko bari ma na Tambayi mutanen gida baku yi ba..Hamida shegen son jin kwakwaf to da kayanta zaki ganni aciki ne..?
Hamida na Dariya tace"Allah ya baki Hakuri Daga tambaya..!
Amina ta mata banza ta zauna kusa da Hanne tana Fadin"Hanne ya su Hajiya da Baba mallam..ke kuma Hamida yasu Mamanmu da Aba ina Jawaad su ya Zeenatu sun san an kawo ni nan..?
Ta fada a marairaice kamar zatayi kuka Hanne ta tura mata Ledan Hannunta tana fadin"Kowa lafiya..Ga Sakon hajiya tace mu kawo miki Sannan tana gaisheki sosai..!
Hamida ma tace"Mamanmu ma na gaisheki Aba da Jawaad duk suna lafiya sannan kowa yaji kina gidan ya Danmallam sunce duk a gaisheki..!
Sai Amina ta jawo leda ta fara fito da kaya bakinta yaki Rufuwa Fadi take yi Duk ni kadai wannan..?
Tana Daga kaya da Hijaban tana fadin"Wannan nasan aikin baba mallam ne..!
Ta daga su yaji da kayan da Hajiya ta Hadamata tace"Wannan kuma na Hajiya ne..!
Hanne tace"Kamar kin sani ta kasa sukuni komai sai tace na Amina ne..!
Amina sai hawayen Farinciki Fadi take nagode nagode sosai Kafin ta kalli Hamida tana fadin"Hamida ina abun Dadin da mamanmu ta bada ki kawo min bana son wasa fitomin dashu kafin raina ya bci..!
Tafada tana mikamata Hannu Har da shan kuni.
Hamida sai taji wani iri ta kasa mgana Domin ita dai mamanmu bata bata komai ta kawoma Aminar ba Hanne ce ta ceceta ta Dauko mata Turaran  wutan da mamanmu ta bata ta Saka ma Amina a Hannu tana fadin"Ga shi in ji mamanmu..!
Amina ta karba tana jin Dadi tace"Kai nagode sosai nayi kewarta sosai Allah Sarki mamanmu..!
Haka take ta fada suna Binta da kallo Sai da tagama gani duka sannan zata kwashi kayan ta maida a ledan Hamida ta hanata ta karba tana fadin"Bari na jera miki Cikin Kwabarki..!
Amima tace"Wayyo Anty Hamida i miss u..!
Ta fada tana Rumgumeta Hamida ta kwace jikinta tana fadin"Ni sakeni..Dole kiyi missing dina anan bamai miki nasani..!
Amina tace"Wlh kuwa kamar kinsani..Ya Danmallam ne in yayi mun masifarsa nake dan ninkewa shi baya son ganin Datti..
Hanne tace"Tab baki san kyamkyamin ya danmallam bane baya shiri da kazami sam Amina sai a Rage son jiki..!
Amina ta Harari Hanne kafin tace"In an ki fa..!?
Hanne ta mike tana Dariya tace"Sai a Daku..Don Wlh keda megidan ne ba ruwana.!
Jin haka yasa Amina tayi shuru su kuma suna mata Dariya Hamida ta Bude Wardrope din taganshi Tsab Cikin mamaki ta juyo tana kallon Amina kafin tace"Amina kece yau da gyaran kayanki..Lalle aure dabam ne..!
Amina ta tabe baki kafin tace"Bani na gyara ba shi ya gyara ni fa tunda nazo gidan nan ban saki jikina ba sai yau dana ganku..!
Chapter 115 · 0% Book details