Sashe 58
Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ki damu..har Abada matsayinki mai Sauya ba Diyata..Allah yayi miki albarka..! Su hanne suna son mgana da Amina basu samu zama ba itama tana so ta yi mgana dasu tana so ta fada musu komai Saboda taji sauki aramta tana cikin wani hali Bata barci Aminu na cikin ranta tana so tasan Halin Dayake ciki gashu bata san ta wacce hanya zata sani ba Duk abubuwan da suka Faru basu saka ya fita ranta ba yana nan a makale ta damu dashi ta Damu tasan wani Hali yake ciki. Tunda ga Ranar bata kara ganin Aba ba ballatana Yaya ammh har ya Zeenatu tazo sun gaisa su ya Zulaihat ma duk Mamanmu ta fada musu sun kira sun gaisheta kuma ba wanda yasan me yafaru sai dai ace abandaki ta Zame har su Anty Amarya sun shigo sun Dubata duk da tana ta Bin Diddigi Dalilin ganin Amina agidan. Sai da Amina ta kwana Hudu awajen Hajiya sannan suka samu kebewa da Amina suka tambayeta ta fada musu komai Hanne da Hamida suka Saki baki suna kallonta Amina ta cigaba da Fadin"Wlh bansan yaushe ne ba..Ban kuma sam Lokacin da soyayyar Amin ta shiga raina ba..Ammh wlh ina son shi ko da wannan abun ya faru ban ji ya Ragu araina ba ina nan kawai ammh ina cikin tashin hankali da Damuwa na san yans chan cikin Tashin hankali..! Hamida tace"Kina nufin wannan dai gayen da muka taba gani..? Amina ta daga kai Hanne tace"Amina kuskuranki ne..Meyasa baki barsa yaje wajen mallam ba..? Amina ta Dafe kanta tana Fadin"Bansani ba Hanne..Bansan haka zai iya faruwa ba..Gani nake kamar komai bazai yi daidai ba in yazo..Kuma wlh yanzu Ina son Amiu bazan iya Rabuwa dashu ba kuban shawara..! Hamida da hanne suka kasa mgana Hamida ce tace"Bamu ta cewa Amina..Mgana tana wajen Aba da Baba Mallan sai dai in zaki bi Shawarara kada ki nuna abunda ke Ranki..Ki bari har muga komai ya Daidaita..! Hanne tace"Nima abunda zan ce kenan..Gwara ki tsaya kiji abunda zasu ce..ammh koni kaina zan so ki Boye abunda ke ranki..Ina ji ajikina Ki rabu da wannan Mutumin Amina Shine Alherinki..! Amina kallonsu kawai batace komai ba Rabuwa da Aminu ba abu bane mai Sauki,Abu ne da bazai taba yuyuwa ba Domin don basu san me take ji bane..! Shuru tayi musu kamar ta bar mganar sai dai ta kasa sukuni Baba mallam bai ce mata komai ba kuma yana zuwa Dubata,ammh bai ce mata komai ba,ga Damuwar halin da Amin yake ciki tasani kila ita tafishi kwanciyar hankali tasan yadda yake sonta Allah kadai yasan wani Hali yake ciki