Sashe 25
Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tayi da Gudu da Abun suya a hannunta yana Digan mai tana Fadin"Kai kai..Ni yaranan zaku raina ko..?wlh na kama yarinya sai na Lahira yafi ta jin Dadi barin ma Amina zaki gane dani kike..!.abun ya bata mata rai kamar ita yaran suka ma haka su ko juyowa ma basuyi ba Hanyar Fita Amina ta kama Tana Fadin"Ku ka tsaya wlh ta Sauke Haushina Akan ku..! Ta kawo bakin kofar kenan tana juya baya bata ma kallon gabanta Daidai Lokacin aka Bude kofar Shashen na Hajiya Lokaci Daya da shigowa Amina bata sami ba ta karfinta ta juyo Hannunta Damke da naman data Diba sai Gaf taji tayi karo da Mutum ammh kamar Da Iccr taci karo Saboda ko gizau na Tsayen bai yi ba sai ma itace ta koma da baya Kamar zata Kifa da Azama da wani Zafin Nama ya ciro Hannunsa guda Daya daga Cikin Aljihun bakin wandon Dake Jikinsa ya Rike hannunta Cikin Tsausatsayi wanda Naman ke Ciki gabadaya maikon da ruwan da Tafashen ya gama Mamaye hannunsa.. Ammh duk da haka bai saketa ba sai da ya Dagota da hannu Dayan nan ta Tsaya da Kafafunta Idanuwanta na Runtse domin ta gama Sadakarwa ta Fadi Numfashi take saukewa shima da azama ya saki hannunta yana Bin Hannunsa da kallo ransa nan take ya baci kyamyami garesa Har tsikar Jikinsa na tashi. Cikin Tatattausan Muryansa ammah Cikin Fada yake fadin"Ke wata irin mara Hankali ce..?kina tafiya ba natsuwa kamar wata namiji..? Muryan daga sama ta jita sannan kafin ta gama Daidaita Natsuwarta ta Bude Dara daran idanuwanta Daga baya taji Hanne na Fadin"Sannu da zuwa Ya Danmalam..! DANMALAM..! DAM gabanta ya fadi kenan da Ya Danmallam ta ci karo bata sani ba.. Da sauri ta Bude idonta ta Sauke akansa alokacin bama ita yake kallo ba Hannunsa na Sama kamar wanda kashi ya taba yana kallon Hanne yace"Hannatu meke damun ku..?wani irin wasan banza ne wannan..? Yafada har Giransa na sama yana Hadewa waje Daya ya Abida Daga Kofar Kicthen ranta fes tasan sai ya Danmallam ya chasa mata su sosai. Amina batasan ta saki baki tana kallonsa ba Domin kamar mayen karfr na janta haka taji ta kasa Daina kallonsa Duk da ba juyo ma garets ba Kyau da zati kawai da wani Haiba take gani da Hange da kuma wani Dattako da wajen Baba Mallan kadai tasan dashi. Hamida jin Hanne tace ya Danmallan yasa ta gaisheshi ya amsa bai Damu Daya kalleta ba Yasan dai Cikin yaran gidan ne saboda ai ba Duka suka taso agabansa ba. Hannunsa ya kallah kafin ya Yamutsa Fuska yace"Miye wanna..?wacece ta shafamin wannan kazantar a Hannuna..? Yafada yana kara kyamatar hannunsa nasa Amina Girman idonta ta Bude tana kara kallonsa Daga sama har ksa Yana Sanye da Jallabiya mai Ruwan Madara,Da bakin wando sai kansa Sanye da Hula irin ta yan Saudiya karama iyakarta rabin kan nasa Fuskarsa tayu wani Haske mai Annuri sosai da Zati Lokaci Daya. Abida na jin abunda yace ta kariso Tana Fadin"ya Danmallan gwara da Allah ya kawoka..Nama suka zo suka Satarmin Hajiya ta sakani suya..! Cikin mamaki yace"Nama..? Da sauri tace"Eh ga shugabarsu na..Amina wlh yaya har tana Zubarda Naman a kitchen bata da natsuwa kamar yadda ka Fada kazamar ce..! Tafada tana nuna Amina wacce ke Tsaye tana kallomsa ga Hannunta Dunkule da Naman data Sato din Shi ko da suka ci karo ya Rikota bai Tsayama kallonta ba Duk azatonsa Sa"adatu ne ko cikin yaran gidan sai yana kallonta yaci gabansa yayi wani Dif saboda yadda Fuskarta ta Tsaya aransa yana so ya Tuna mai irinta Saboda Tsabar kwarjinsa akaron Farko Amina taji ta kasa Jurre kallon Cikin Idanuwansa Sai da ta sadda kanta gabanta na Fadi haka kurum taji Wani tsaro karon Farko da kunyar da Amina bata taba jin irinta ba. Ganin yadda ya Dawo da kallonsa kan Abida ne Cikin Alamun Tambaya. "Amina...? Da sauri tace"Amima..Diyar Baba Sa"idu ne..Yar wajen yaya ce fa..! Ga Hamida ma itama duka na gidan Baba Sa"idu ne..! Sai alokacin ya kara kallonta yasan wannan Fuskar matar dayake ganin kimarta bayan Hajiya babba ne wato yaya. Shi bai ma san tana da Wata karamar yarinya ba ya Dauka Jawaad ne Autanta Saboda in yazo yana ganinsa Tare da Baba Sa"idu shi bayansu Jadwa sai su Jaleela yaran nan duk ba Saninsu yayi ba. Hayaniya ce bai so sannan hannunsa kyamkyami ya ishesa yasa yace"Nama kuke sata agidan Baba Mallan..? Yafada Cikin Sanyinsa a karon Farko Hamida da Hanne basu Dauki Jidalin Amina suka Hada baki Wajen fadin"Bamu bane..Wlh Amina ce ta Shiga ta Dauko..! Suka fada suna Nunata Amina taji kamar kasa ta Bude ta shige saboda kunya tana jin idanuwansa akanta Ga hannunta Dauke da Nama Ruwan maiko na Diga da Sauri ya kauda kai ya wuce da Hanzarinsa cikin Natsuwa "Ita mace da natsuwa aka santa..Hakane ke bambamta ta da Namiji..Sannan kazanta ko a addini bashi da kyau Hadisi ne guda Ko Sallah bata cika ssi da Tsabta..! Bai ko kara kallomsu ba ya shiga Kitchen din ya tara hannunsa a sink ya wanke har da saka Omo yana jin karnin Naman a Hannunsa karamin Tsaki yaja kafin yace"Kazamar yarinya kawai..! Suna nan Tsaye kamar an Dasasu ya Fito Abida ssi Dariya take musu suna ganin ya fito Hanne taja hannu Hamida suka fice da Sauri ammh Amina ta kasa gaba ta kasa baya. Kunya da wani abu data kasa sanin Dalili taji wani abu sunan yau an kunyatata Duk da gaban Hanne da Hamida ne an kirata msi Satar nama kuma kazama kuma mara natsuwa har ana Dangantata da Namiji wadandan kalmomin sun taimaka wajen sata ta cigaba da Tsayuwa a wajen Saboda ji tayi kafafuwanta sun kasa Daukanta. Tana tsaye a wajen taji yana Tambayan Abida Hajiya tace tana ciki Tana kuma jin Sanda ya fara taku zuwa Dakin Hajiya yana Shigewa Abida ta saka Dariya tana Fadin"Bera mai satan Nama..!. Sai ga Idanuwam Amina sun ciko da kwallah suna Shirin zubowa. Su hamida sun fara gaba suna juyowa suka ga ba Amina Hanne tace"Amina bata taho ba..? Da sauri suka juya suka koma suna Shugowa falon daidai Yana fitowa Daga Dakin Hajiya shi da Aisha yana mata mgana ganin haka yasa suka kasa ma Amima mgana shi kan yama manta dasu sam Aisha Dakin da Sarood take ta shiga ba jimawa sai gata ta dawo tare da ita tana ganinsa ta Nufesa kamar zata Rumgumesa sai ya rikr hannuwanta Hanne nata Zungurin Amina duk son gulmarta wannan karom bata Dago ba Domin har alokacin bata gama Dawowa daidai ba. Mgana suke da harshen Laranci Cikin kwarewar da in ba ka iya Sosai bane bzaka gane komai ba ba Dadewa ya Dauko waya daga gaban Aljihun jallabiyansa ya bata Sannan ya Saki hannunta Tana Sakij mai kayattacen Mirmishi yana Shirin juyowa Hanne ta Fizgo hannun Amina suka jata suka fita da sauri har suna Bugo kofar Falon da sai ya da maida Hankalinsa wajen. Ganin bai ga kowa ba yasa ya barsa shima Ficewar yayi suna ganinsa labewa sukayi a wajen Bayan Shashen Hajiya,sai da ya wuce suka Fito Hanne ta kalli yadda Amina tayi zata Rantse da Allah bata taba ganinta Cikin wannan Halin ba Da Sauri tace"Amina lafiya..?ko wai Fadar sunanki da mukayi..? Da Sauri Hamida tace"Wlh shi ba irin ya jafar bane..Kinga idonsa kana mai karya sai ya ganeka..! Amina bata ma Tsaya bi ta kansu ba Nsman Dake hannunta ta saki ya Zube a kasa,kawai ta kada kai ta wuce Suka Bita da kallon mamaki suna kwala mata Kira bata amasasu ba. Suka fita har suna Hadawa da gudu ganin ana ta Haraman Alwala Domin lokacin Sallah ya kusa. Amina bata tsaya musu ba Har da suka iso gidan Ya Zeena na bakin Famfo tana wanki mamanmi na Shinfida Darduma kofar Dakinta Amina ta shigo ba sallama Ya Zeenatu ta dago tana Fadin"In kika gyara Halinki ai ke baki cika Amina ba..ki rika shigowa gida kamar Kafira..! Mara natsuwa kawai..! Amina ta jita ta kuma ji sanda Mamanmu kr fadin"Zeenatu bana son haka..?ban ce ki daina shiga Harkan Amina ba..,!? Ita dai sai da ta danganta da kan gadontw taci kukan data rikewa ya zo mata Kamar wacce aka Daketa ta Fara kuka tana jin Hanne da Hamida akanta suna tambayanta tayi kamar bata jisu ba. Kuma taji sanda su ya Zulaiha ta shigo ita da ya Zeena ganin Amina na kuka yasa suka tambayesu sanin halinta ba kasafai take da Saurin kuka ba. Hamida ta fara maida yar da akayi tazo wajen bayanin abunda Danmalan yace Amina ta Dago afusace tana Fadin"Eh yace min Kazama mara natsuwa ko..?haka kika so kice munafuka..! Tafada tana Sakarmata Jajayen idanuwanta da sai da ya basu Tsoro. Sai a ka rasa mai mata mgana har ta Fice Fuu Daga Dakin Zeenatu ta kwashe Dadariya tana Fadin"Ba Duka ba Zagi ashe mgana na Ladabtar da Amina bansani ba..? Hamida dai da Hanne sun kasa mgana ajikinsu yayi sanyi. Yasa suka fita suka fara shirin yin alwala Jam'i suka bi Amina na Dakin Mamanmu ta Dunkule kan kujera ko Sallar batayi ba tana jinsu a Tsakar gida suna Fadin yau Yaya Danmalan ya bada Sallar Itama ai taji Sanyayyar Muryansa yana Karatu Karatun da Har ita tayi karya tace bai natsar da zuciyarta ba tana jin Yaya na Fadin"Allah Sarki mun yi kewar karatun Danmallam..! Daman in yana nan shike bada Salla har ya koma..! Amina aranta tana ayyana yadda yau yaci Zarafinta sai taji gabadaya Duhu ya mamaye saninta dashi an sha ce mata mara natsuwa da kazanta ammh yau sai abunda ya Zafeta fiye da koyaushe. Tana jin sanda Hanne ta ke ma su Mamanmu sallama tatafi gida sai Alokacin Amina tatashi tayi sallar Tana Tura baki. Ganin yan jidalin na kusa yasa bama wanda ya sake bi ta kanta. Sai dai tun Safe Hanne ta Dawo Lokacin Amina ta dan Huce Tana zaune bisa gadonta ita da Hamida alokacin Hamida Ya Zulaihat bata Dakin ya Zeena na makaranta. Hanne tace"kunsan wani abu..? Hamida ce ta girgiza kai Amima kuwa Yamutsa Fuska tayi kawai duk da Hannen na kusa da ita ne. Hanne tace"Ashe balarabiyar nan mai kyau dinan da ya Danmallan yazo da ita matarsa