Sashe 190
Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar yana kiran Dutse haka tayi mai yasan Laifinsa yasa ya fara mgana"Amina kiyi hakuri Ana Asif..Nasan ban kyauta ba da na tafi ban Fada miki ba..Ammh kema ai kinsan kin batamin ko..? Kamar tana jiransa ta juyo Lokaci Daya ta Mike zaune tana Fadin"Au nama bata maka ko..!? Saboda ban je nayi ma Hajiya Rashin kunya nace zan bika ba ko..? To ai da nayi hakan da nagane bani da wayau domin ka nuna min Tabbas ku maza baku da Tabbas haka zan bika kuje ku Hadu da matanka kuna wulakantani Tunda ka nuna musu ban da Daraja..duk lalacewar naka ai naka ne. watarana Hajiyar dai itace Uwata kuma wajenta zan koma bari kaji na Fada maka har yau ban yi Nadaman Kin binka ba..Indai kan Umarnin Hajiya ne da kai ma ta isa Dakai bama niba..! Ta fada tana bayyana bacin ranta Danmallam sai ya kasa mgana yana kallonta Amina taji hawaye sun kawo mata sai tama kasa Cigaba da mganr Danmallam ya Bude baki yana Fadin"Amina n...! Dakata..! Tafada tana Dagamai Hannu kafin ta kallesa Tana fadin"Ba sai kace min komai ba..Ka nuna min matsayina amfanina ya kare Tunda kamin ciki na Haihu ni Aikina kenan shiyasa Domin ka nuna min ni din ba wata bace yasa ka Dauki matarka kuka koma Tare bansani ba.? Saboda ka nuna min in ban bika ba kana da Biyu irina ko..? To ai bakomai yanzu ma sai ka koma wajensu ni ban kira ka ba sannan ban aika maka da katin gayyata ba..! Daga haka ta juya zata kwanta ya riketa da karfi tana so ta kwace jikinta yaki barinta sai ma gadon da ya hau ya Rumgumeta sosai Duk yadda taso ta kwace kanta yaki barinta sai kawai tayi Lamo sai kuka Danmallam ya kamkameta yana Fadin"kiyi Hakuri Amina na Tuba nabi Allah..Na biki..Nasan ban kyauta miki ba ni Haushina da na shirya tafiya Dake kika bi na..Wlh Amina na kasa zama in baki kusa dani ina Bukatarki kusa dani Amina..Noor ina sonki..Wlh ina kaunarki ki yafemin..! Amina ta kara sakarmai kuka Tana Fadin"Baka sona ka nuna ka fi son matanka akaina..! Yana kara riketa cikin jikinsa yace"A"a kada kice haka.. Kema kinsan ina sonki..Tunda na koma bana cikin natsuwata na gama Fushin na Sauko na nemeki baki bani Daman kare kaina ba..Sannan ki duba na kasa zama a madina saboda ke..Hankalina ya tashi ko Barci bana iyawa..! Wannan duk ba so bane. ? Wannan duk bai sa kisan kina da Daraja ba..? Amina na jinsa ta masa banza sai Faman mata rantsuwa yake yi yana Lallashinta Amina na karamai Bore Gajiya yayi ya Hade Bakinta da nashi Duk yadda taso ta hanasa ta kasa Domin itama ai ta gyaru tana Bukatar Mijinta a kusa da ita tun ana Lallashi har aka Sauya salo Danmallan yadda ya Samu Amina yasa sai da ya raina kansa kuka reras ya Dinga rairamata Albarka kuwa tashashi har sai da tagaji Sai da suka samu natsuwa sannan sukayi wanka tare bayan sun fito taje ta Hada masa Tea ta kawo mass Yakaka da yaran Tuni har sun yi barci. Sai janta da Hira yake yi taki Sakarmai Fuska sai dai eh ko A"a shima yasan ai yaga karshensa ina shi ina kara ma Amina Laifi..? Irin wannan Hukunci haka..? Duk Fushinta kafin wayewar gari ta Sauka sannan ya Lallabeta suka koma Ruwa wajen Danko yake mai Amina tasha gyaran da yasa Danmallam ya kara raina kansa da duk abunda yake Takama dashi. Amina sai yanga take mai sai da Safe ne ya Dauki su Aba bayan Yakaka ta musu wanka Allah yasa bata da Paper ranar ammh taso tana dashi tayi Tafiyarta ya karata shi kadai Tunda ya Dawo bai fita ba ko Sallah acikin gida yake yi wayarsa ma kasheta yayi saboda yasan Halin Amina da zafin kishi yanzu ya samu ta Dan Sauko ai sai su Sakina su Ballomai ruwa ya shiga uku..! Yakaka sai ta koma zaman Daki Ta bar ma"auratan su ci Lokacin su Taji Dadi Data ga sun sasanta kansu. Allah ya taimaki Danmallam kwana Hudun da yayi Amina bata da Jarabawa da su yayi amfani ya Gurji Amarcin sa sannan ya samu ya Nuna ma Amina matsayinta duk da ta gamsu bata wani Sakin mai sosai shifa Jidalin Amina shi zai bada Labari Domin shi yaga komai ganin Idonsa..! Ranar kwana Biyar tana da Jarabawan Safe sai da taje tayi ta Dawo bai Fita ba har tace mai ko gidan mallam bazai leka ba saboda ya wanke maata zuciya yasa yace Zuwan nata ne baki ta tabe bata nuna mai tawani ji Dadi ba aranta kuma ai tasan ko yanzu kasuwa tatashi Dan koli yaci Riba..! Sati Dayan da Danmallam yayi komai ya Daidaita Tsakaninsa da Amina Saboda kada ya kara ballo ma kansa ruwa yasa yace in ta gama jarabawar ta shirya tafiyan ta gaya masa sai yasa Jafar ya nema mata Visa sannan ya Sanar da ita ya Sama mata Takardan zama achan na Dindin bata wani Nuna murnanta ba sukayi sallama Ta Abuja ma wannan karon ya kara tashi Sai washegari ya isa jidda Daganan mota ta kaisa garin Madina Ya kirata ya samu ta Daga wayan Daman kafin ya Tafi sai da ya roketa alfarma shi yanzu Lallaba Amina yake tasha shi ya warke..! Yar ya tafi su mallam basu san yazo ba bai gayamusu ba sannan kuma itama Aminar bata gayamusu ba tayi gum da Bakinta itama Yakaka bata Fadama kowa ba..! Danmallam Daya koma sai ya Fara Cukun Cukun sama ma Amina gida sun yi shawara da Aliyu akwai kudi a Hannunsa zai siya mata gidanta ne ya Fasa,karban na cikin makaranta Yasan ko giwan wake yasha bazai Hada Amina zama dasu Sakina ba..! Tafi su kishi da Jidali zaman ma bazai yi Dadi ba,Sannan Aliyu ya bashi goyon bayan ya samata gidanta ita kadai Saboda tana da yara sannan kuma hakan ne ma ya Dace zai fi Samin kwanciyar Hankali da hakan suka Tsaida mgana da Taimakon Abu Kattab ya samu karamin gida nan cikin gari kusa da Masallacin madina..! Bedroom biyu sai Falo sai Kitchen da karamin haraba kafin dai abubuwa su Daidaita,sannan yasa aka gyara gidan ya Zuba abubuwan amfani na Daidai misali Duk da ya Takura bai da kudi sai da Aliyu ya turomai wasu suna waya da Amina ta fadamai sun kusa gama Jarabawa. Ya kira jafar suka yi mgana kan zai nema ma Amina Visa ammh sai ta amince sannan Jafar mamaki ya kamasa su ya Danmallan an shiga Hannun Amina sai Allah..! Ko su Hajiya bai Fadama Amina yake jira ba sun zata fushin da yayi bai Sauko bane suka zubamai do suga iya gudun ruwansu..! Amina sun gama jarabawarsu Cikin Sa"a sai Fatan Nasara asatim Matar Aliyu ta haihu Aliya jin haka yasa Danmallam yace ta shirya taje suna ta kwana Daya batamai musu ba ana Gobe suna Idi yakai su ita da Yakaka da yaran Aliya nata ina ta saka dasu sai Faman nuna ta take yi a matsayin Amarya abokin mijinta Amina dai Sama Sama domin ita bata da yarda ne kan wasu abubuwan sannan bazaka nuna mata ki da Farko ba Sannan ka Dawo ka nuna mata so ba, Daga baya baya ba..! Kuma Aliya sukan yi mgana da Sakina ammh ba kamar baya ba Sai dai Sama sama kawai kowacce tasan matsayin yar"uwanta sakina kuma sai dai a gaisa da Labarin Duniya Tariga ta gama Shiga Taitayinta..! Kwana Daya sukayi suka Dawo Gumel ammh sai da Amina taje ta kara Duba Anty Amarya abun sai addu"a Yanzu takai sai ana kulleta adaki Itama Daga Bakin window ta Lekata Sai da ta mata kwallah Mamanmu ma suna waya da su ya Zeenatu an sallameta tana gida sun ce dai da Sauki ammh ba Baki har yanzu ganin ma dai sai ahankali ita kanta Hajiyar uwar ma Duk ba wani Cigaba sauki sai na Allah itama har yau an kasa gane Cutar Dake Damunta..! Amina batayi gaban kanta ba sai da ta Samu Hajiya ta Fada mata yadda sukayi da danmallam da yazo sai dai Ta Boye Rigimansu Hajiya tayi ta Dariya aranta Ta kuma godema Amina sannan ta godema Allah ko banza yarta nada Daraja Hajiya tace zasu Tattauna da mallam tana mai mganar yace ta shirya tabi mijinta Hajiya tace to..Anty Hadiza tama mgana aka Hada mata kayan gyaran jiki Sannan da Dake Dakem kayan kamshi da sauransu na Tafiya. Sannan Hajiya ta kira Danmallam taji Tsarin Tafiyar na Amina da inda Zata zauna ya fadamata ya siya mata gida Hajiya taji Dadi tana ta sakamai albarka..Sannan ta mai mganar Yakaka yace sai in Amina ta Fara Tahowa sai yaga yarda za'ayi shima yasan zaman Yakaka da Amina taimako ne sosai Danmallam bai saka a fara neman mata Visa ba sai da Amina ta Kirasa da kanta tace ta amince zata taho sannan ya yarda Jafar yazo ya amshi pasport dinta sannan yace ta Hada kayanta saboda jirgin yawo zai yi gaba Dashi..! Jin haka yasa Hajiya ta siya mata Kamshin Girki kala kala da su garin kuni aka shanya mata wake surfaffen da Danyen shinkafa kaya da marasa Nauyi da su fulawa da Sauransu,Sai kayan sawanta dana yara duk da ba Duka ta Diba ba..! Ansamar mata Visa zata su tashi nan da kwana goma ta Abuja,sai Amina ta Cigaba da shirinta ta kira duka yan"uwa awaya tayi musu sallama su Hanne suna ta Fadin zasuyi kewa da kuma Fatan in suka Haihu Allah yasa tazo tace tasan da wuya. ! Ana jibi zasu tashi Suka kulle gidan suka je gidan Baba mallam tayi sallama da Aba da Anty Hadiza anan ma gidan ta kwama itama Yakaka ta musu sallama Domin abuja gidan Ya Aisha zata koma kayan su Tuni suna Madina har Danmallan ya karba. ! Washegari Idi yakaisu Abuja gidan ya Aisha suka kwana washegari karfe Uku na Rana su ya Aisha da mijinta da Yakaka suka Raka Amina Filin jirgi tana Sabe da ya"yanta daya a gabanta ta Sakashi Cikin Abun goyo Daya kuma yana Kafadanta suma yaran sun yi Bul Bul Dasu suna Daga mata Hannu Amina sai da tayi kuka Lokacin da Jirginsu ya Daga Tana Salati Allah yasa akwai wata Farar mata