← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 193

Sashe 44

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

suna Yar Jagora. Duk da kunnenta baya wajen taji Suman Radau acikin kanta. Saratu ta kalli Zainab tana Fadin"Ni ban da wasu wakoki Zainab..Sai dai ina da Sabbin wakokin AMINU buba Da yayi kwanan in kina so sai na Tura miki..! Kamar a mafarki taji ankira sunan ta Taba jin sunan ta kuma Haddace sunan acikin kanta. Da Zumudi a Murnan Zainab tace"Yauwa don Allah sakamin..Ina son wakokinsa..! Daga sama kawai suka ga Amina Sanda ta Dafa Saratu tana Fadin"Wani Aminu Buban..? Da mamaki suke Binta da kallo kafin Zainab tace"Mawaki ne mai Tashe Amina..! Ido ta zaro kafin tace"Da gaake..?kina da Hotonsa..? Zainab cikin mamaki tace"Hotonsa kuma..?a"a ni bani dashi wakokinsa kawai nakeji shima a wayar ya Kamal nasansu..! Saratu ce tace"Yayata nadashi in kina son ganinsa ki bari gobe zan turo miki..! Da sauri Amina tace"Yauwa don Allah ki turomin akwai wani dana sani ne in so nagani ko shi ne..! Da mganarta suka yarda da ita Washegari kuwa suna zuwa makaranta Saratu tace ma Amina ta Turo Hoton a wayarta Vivo Lokacin da Amina ta ga Hoton sai da Gabanta ya Fadi. Yana Sanye cikin Riga da wando Ja da Fari Wandon Ja ne Rigar ciki Fara sai Jaker dinsa ja Takalmin kafarsa Booth ne fari haka ma Facing cap din Kansa Ja ne mai Kalan Fari yayi Tsayuwar matasan wannan zamanin Fararan Hakoransa mai Wushirya duka suna waje a kasan Hoton an sanya A.A BUBA..! Sai alokacin Amina ta tuna yana ta Nanata mata bata sanshi ba..?Ashe cele ne shi to ita ina zata sanshi..? Ba waka suke ji ba ballatana kallo. Saratu ta karbi Wayarta tana kallon Amina Zainab isa ce tace"Shine..? Sai ta samu kanta da girgirza kanta Saratu tace"Kila suna ne yazo Daya..Shi wannan Aminu Aliyu Buba sunan mawaki ne mai tashr yadda naji ana Fada bai Dade ba sunansa yayi Fice..! Amina na jinsu batace komai ba Zainab ce ta karba tana ganin Hoton kafin tace"Kyakyawa dashi kamar Bafullatani..! Saratu tace"Ance Bafulatanin Yola ne..Karatu ya kawosa kano..ya fada Harkan waka..! Amina ita Daga Lokacin batama jinsu Tana chan Tana Mirmishi Lalle Amina mai Sa"a yau ga Wanda Duniya ta sani ya Taba cewa tana Burgesa anya in ta Fadama Mutane zasu yarda da ita..? Taso gaban irin su Sa"adatu ne ta tabbata sai Hauahi ya kashesu ita Kadai kawai in ta Tuna A.A Buba ranta sai yayi Fari kanta ya kara Girma Ho..Sai ita Amina Aminene Manya kasa..!
Chapter 44 · 0% Book details