Sashe 62
Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ganin Halin da yake ciki yasa Baba Mallam yace su tafi asibiti haka kuwa akayi Ya Jafar ya Tuka Motar Mallam dashi da Yaya suka tafi asibiti da Aba su Hajiya kuma suna tare da Amima da tasha gashi Ta samu Targade a Hannunta na Hagu da gocewar kashi a Kafarta Mamanmu da Hajiya suka Shafe mata da man zafi tama Hawaye sunayi Mamanmu ma kasa zama tayi ta koma Cikin Bedroom dinta tana kuka Anty Amarya nan nan bata tafi ba da anyi abu sai ta Tafa Hannu tana Fadin"Oh..Allah dai ya shiryamana..An haihu dai a Ragaya..!
Sai da Hajiya ta gaji ta tanka mata da Cewa"Ki kama bakinki Domin kema Uwace..Akwai Sa"adatu da Sabeeha agabanki bakisam ina Kaddara zata kaisu ba!
Jin haka yasa ta Fara Fadin Hajiya na mata Mugun fata Cikin gatsali tace"Allah ya Tsareni kowa yasan ya"yana basu fita zakka ba..Daman ai wanda yasiya Rariya yasan zata Zubda Ruwa..!
Ba wanda ya kara bi ta kanta kuma taki Tafiya kamar mayyah har sai chan Dare Baba Mallam ya Dawo Jinin Aba ne yayi sama An bashi gado ya Jafar na wajensa zai kwana sai alokacin suka koma gida bayan Baba Mallam ya kwantar ma da Yaya da suka Dawo tare ita da Mamanmu sun Daina kukAa Amina kuma ta samu barcin Wahala Baba Mallam yace zuwa da Safe mai gyaran Targade zai zo ya gyara mata.
Sanda suka koma gida Dagashi har Hajiya sun kasa Runtsawa Fadi kawai Take"Na kasa gane meke Faruwa Mallam..?
Nasan Jafaru bazai yi karya ba..Nasam jikina na bani Amina ba haka take ba..!
Baba Mallam yace"Wani al"amari ne da Allah kadai yasan me ya Lullube aciki..!
Nan ya shiga Fadamata yadda sukayi da Baba Sa"idu ta sauke Tagumi tana Fadin"Kai..wata sabuwa to memene Mafita..?
Baba Mallam yace"zan kwana Istikara Zuwa Safe Boyayyan al'amarim zai bayyana Hajiya kema ki tayani..!
Da kai ta amsa mai,Tabbas sun kwana Gayama Allah Hajiya ce ma wajen Uku na Dare ta kwamta Baba Mallam sai karfe 4 ya iya barci saman Darduma bai tashi ba sai da yaji wayarsa Dake cikin Aljihunsa na Ringung yayi Zumbur ya Mike yana Lalubota yaga DANMALLAM..!
Ne ke kiransa ajiyar rai ya Sauke ya Daga wayar da Sallama Dagachan bangaran Umar ya amsa cikin Sanyinsa yana Fadin"Baba..Nasan yanzu asuba ne a Nageria shiyasa na Bugo Domin na samu ladan tashinka Duk da nasan kila ma kana masallaci..!
Baba Mallam ya Mike a kasalance yana Duba agogon bangon Bedroom dinsa 4:55pm na asuba..!
Cikin karfin gwiwa yace"Na makara yau Umaru..Naji Dadin kiranka Allah yayi maka albarka..!
Ya amsa da Amen Cikin Farinciki kafin suyi sallama suna gama wayar Baba Mallan yayi kasake na wani Lokaci kafin Lokaci Daya Mirmishi ya mamaye Fuskarsa Hajiya ya kallah Dake barci ya karisa ya Bubbuga Gefen gadon yana Fadin"Hajiya..Hajiya..!
Mika tayi Cikin Tattatusan lafazi yace"Ki tashi mun makara sallar asuba..!
Mikewa zaune tayi tana Mutsike ido Lokaci Daya tana Fadib"Mallam kasamu mafita kuwa..?
Wlh da yarinyar nan na kwana araina ita da Sa"idu..!
Cikin Mirmishin data kasa gane masa yace"Kada,ki damu..Cikin ikomsa ya kawo mana Mafita tashi kiyi sallah ki shiga gidan Sa"idu ni kuma Daga masallaci asibiti zan tafi na Dubasa..!
Kai ta gyadamasa tana kallonsa ya saka akyabbansa da Rawaninsa ya Fice acikin ranta tana Tunanin wata mafita Mallam ya samu wannan Fara'ar dake fuskarsa ta bayyana Koma wata Mafita ce ta zauna mallak din sosai acikin Ransa..!
*Janafty*
[11/3, 2:05 PM] Sweet sis: *TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*🅿️21*
Suna idar da Sallar Asuba Baba Mallam bai Tsaya ba Ya Nasir ya Tukasa zuwa asibitin Tunda shima nan ya sallaci sallar asuba Ya jafar tun Daran jiya ya kirashi ya fadamai kafin su tafi sai da Baba Mallam ya Umarci Shamsu daya kira Mallan ya"u mai Dori yazo ya Duba Amina..!
Haka kuwa akayi gari na waye bakwai na safe Ya shamsu yazo da mai Dorin,Koda yaje Hajiya Babba tana gidan Amina jiki yayi Tsami sai faman kuka take ashe kadan tayi Domin wajen gyaran Targade da Goshewar data samu sai da ta raina kanta sai da su Hajiya da Mamanmu suka Riketa Hamida da Hanne suna ta kuka Ranar ko shirin zuwa Hadda ba wanda yayi acikin gidan sai dai chan su Sa"adatu ne Idi Direba zai kaisu..!
Yaya kuwa Hada hadar abun karin da zata kai asibiti take yi ko afuska bata bayyana wata damuwa game da Amina ba Ita ta Aba take yi,ammh sai dai karkashin Ranta Damuwa ne Dankare wanda Tsabar kawaicinta yasa bata bari a Fahimceta ba, sai dai fa Uwa uwa ce kuma bazata Haifi abu da Cikinta tace kuma bata kaunarsa ba sai dai kawaici da wasu abubuwan da kansa Uwa ta kauda kai kan abunda ta haifa sanin Halinta ma ba wanda yabi ta kanta Domin kowa yasan Yaya bata taba Shiga Sha"anin Amina sai abun yaci Tura yakai mata makuran da zata tanka..!
Ya bada mgani an shafa mata Cikin kwana Daya ammh Amina ta Fita Hayyacinta ta rame sai ido,Tasha wuya cikin kwanakin Wuyan da bazata taba mantawa da ita ba Hamida da Hanne sun fi kowa sanin Amina tafi kusa dasu shiyasa lamarinta yafi Damunsu gabadayansu suma Suku suku suke kamar basu da Lafiya sun tasa Amina da Tagumi tana kallonsu sai dai yau karon Farkon Bakin Amina ya Mutu bata mgana sai ido sai kuka acikin Ranta wani abu ne mai Girma Tana ji ajikinta komai yazo karshe ta rasa Aminu shima ya rasata sannan abu mafi girma tana jin kamar wata Kaddarace zata faru da ita yasa abubuwa suka kwabe mata Lokaci Daya sai dai koma menene Tayi alkawarin bazatace komai ba Tunda mai Faruwa ta Riga ta Faru babu Tsumi babu Dubara..!
Dakyar Hajiya ta Lallasheta tasha Tea da Panadol Saboda Zazzabin Jikinta sai ta samu barci sai alokacin suka samu Daman karyawa Mamanmu da Yaya suna shirin Tafiya asibiti duk da sunyi waya da Ya Jafar yace ya Dawo gida Ammh Baba Mallan nachan suka barsa tunda safe Ruwan zafi ma Nasir ya koma gida ya Taho dashi Da kayan Tea..!
Ya Abida ta shigo ta Duba Amina kafin su wuce Hadda ya zeena ma bataje ba su Sa"adatu ne suka tafi dasu ya Akilu sai Umaimatu,Misalin karfe Tara na Safe Hajiya Babba da Yaya da Mamanmu da Anty Shamsiya matar ya Jafar suka tafi asibitin da aka kwantar da Aba domin su Dubasa shi kowa kagani rai da zuciya ba Dadi.
Wani private Hoptal ne Daki na Musamman Aba ke ciki Vip.
Suna shiga Baba Mallam kadai suka Iske awajensa Aba din yana ta barci su Mamanmu suka gaisheshi Cikin girmamawa ya amsa yana Fadin"Mungodema Allah..Ya jikin uwar tawa?Nace shamsu yazo da Mallam ya"u sun zo kuwa..?
Wannan karon Hajiya ce tace"Eh har ya gyaramata ya bada mgani an shafa mata tasha mgani koda muka fito ta samu barci..
Ya shi Sa"idun..Ya farka kuwa..?
Baba Mallam yace"Eh ya farka da Safe jikinsa da sauki sosai bai dade da komawa barci ba koda Nasir ya bar nan muna ta Hira dashi..!
Gabadaya suka amsa da Alhamdulillah mai sunan Mallam ne Dake bayan Shamsiya ya fara kuka Mallam yace Hajiya ta karbo shi ,ta kwatoshi daga baya Ta mikama Hajiya ita kuma ta mikoma Mallam ya saka Hannu Biyu ya karbesa yayi wayau Yayi girma kansa ya dafa yana Tofamai addu"a sai da ya gama sannan yace"Ciwon kunnin nasa fa.?
Kan Anty Shamsiya na kasa tace''Yayi sauki..yadaina kukan tun jiya daddare..!
Baba Mallam ya gyada kai yana Fadin"In muka koma gida zan bama Jafar wani mgani ku rika Digamai Daga Saudiya nazo dashi..!
Kai ta gyada kafin tace"Jiyan ma Da daddaren wajen Mamanmu yacemin zai zo ya karbo masa wani mgani shine baidawo ba sai waya naji yana Fadamin yana Tare da Aba a asibiti..!
Baba Mallam yace"Wlh kuwa..Ammh ai da sauki yana ta cewa ma a sallameshi ya koma gida..!
Mamanmu tace"Daman ai baisan zaman asibiti..!
Hajiya tace"Sai hakuri ya bari ko zuwa gobe ne in ya kara jin Sauki..!
Suna cikin mganar ne Aba ya Farka Daga barcin daya kwasheshi suka fara Rige rigen mai sannu Mamanmu tana kokarin Taremai Filo Sai Yaya ta rigata sai ta sakarmata Ya jingina da Filo sannan ya tashi yana amsa gaisuwansu Lokaci Daya yana Binsu da kallo cikin Tsausayinsa Yaya tace"Ga Ferfesun kayan ciki nayo maka..In zubo maka zakaci..?
Mirmishi ya saki kafin yace"Zubomin Hadiza..Nagode Allah yayi miki albarka..!
Akunyace ta amsa ta Duka tana Zubamai Cikin Filet din da tazo dashi,Kadan yace ta zubamai ta mikamai ya karba Baba Mallan na Fadin"Ashe girkinta kake jira shiyasa bayan Ruwan Tea kaki cin komai..Duka abincin da matan yaran nan sukayi bai taba komai ba Hajiya..!
Dariya tayi tana Fadin"Sa'idu ne fa..Tun farkon auransu Girkin Hadiza yasa ya faramin yajin cin abinci kaga Tunda yayimin yaji nasan Hadiza ta Curi Tuta..har yayi aure adakina Sa"idu ke cin abinci Mallam har haushi yake ji na kwace masa yaro..