Sashe 30
Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ke hannunsa gari guda ne..! Hanne ta karbe da cewa"To yaushe zamu je mu gani..?bamu taba zuwa ba..? Amina tace"Kuma fa hakane..?to ammh Aba chan yake zama fa..?ya zamu yi mu je chan Hadeja Road ne fa..? Hamida tace"Nidai ba ruwana..! Amina tace"Sai me..?ke dain kin cika Tsoro..Hanne bari nayi shawara na Rabtse koda bala'i sai mun je mun gani ko da zamu dawo a yankamu ne..! Hanne tace"A"a fa ni wasa nakeyi..! Amina tace"Ke fa sai an je..Inaga ma gobe saboda bama wanda ya Damu damu..! Hanne zatayi mgana kenan sukaji mgana da kofar Falon Baba maallam gabadayansu suka Leka suna ganin Ya Uzairu ne ya fito Daga Falon mallam din Bayansa ya Shamsu ne sun saka Takalmansu sun nufi barayin da Dakumansu suke Amina ta juyo tana Fadin"Jaruba..Daman ya Uzairu ya Dawo ne..! Hanne tace"Eh mana tare suka zo da Ya Zulfa..! Amina tace"Harda Ya Nazem..? Wannan karon Hamida ce tace"A"a shu naji Ya Zahra na fadin sai gobe yace zai taho yana da Karatu gobe..! Amina tace"Mugayen gidan.com zasu Taru Lokaci Daya bala"i..! Hanne tana Danne Dariyanta take Fadin"Har na tuna ya Nazeem sanda ya miki Dukan Tsiya Lokacin muna aji hudu kin Tuna. ? Amina tace"Kan bala"i ina zan mata..Ranar ai mariya na Tsungula ya kamani Shinr ya fitar dani gaban aji kusan awa daya nasa ya manta dani ne na Daga Murya nace Tattasan da ka shanya ya isa Bushewa sai kazo ka kwashe..! Gabadayansu suka saka Dariya Hamida tace"Kin ga kwashewa kuwa..Amina kin Daku fa hannu. Ya Nazeem..! Amina ta Ciji yatsa Kafin tace"Kuma Wlh har yanzu ban yafe ba Wuta bal bal har kabarinsa..! "kai su waye anan..? Mganarta ta Katse ne sanda aka Dallaresu da Filita Lokaci Daya da mgana suka Tsorata gabadayansu sukayi Tsumu Tsumi. Ya Uzairu ne zai fita shago ya Siyo kato yaji mgana daga bayan shine ya Haskasu da wayarsa. Karisawa yayi gabansu yana kallonsi Daya bayan Daya ya ganesu mamaki ya bashi me suke anan..? Cikin Tsawa yace"Su waye anan..? Hanne ce baki na rawa tace"Mune ya Uzairu..! Amina kuma namanta take kullewa a leda yace"Ke miye wannan..? Daidai Lokacin da su ya jafar suka fito daga Falon Baba Malam daman tun Fitowarsu masallacin Sallar isha"i suka Dumgumo suka shigo. Bayan Ya Nasir ne sai ya Danmalam Daya fito Daga karshe. Jin mganar ya uzairu yasa Ya jafar Daya sanya Takalminsa yake fadin*Kai Uzairu lafiya..?kai da su waye..? Juyowa yayi yana fadin"Wlh yaya zan wuce naje siyan kati naji mgana ta nan ina Haskawa naga yaranan bansan Uban da sukeyi anan lungun ba Cikin Duhu..! Dukkansu matsowa sukayi shi da Ya Nasir banda Ya Danmallan Dake gefe yana Danna Wayarsa. Gabadayansu suka Haskesu da Fitulan wayarsu Ya Nasir yace"Lalle nema yaranan to ku fito don kaniyanku..! Ba musu suka mike suka firfito Amina ce ta karshe tana Boye abunda ke hannunta ya Uzairu ya jawota yana Fadin"Bani abunda kike Boyewa..? Baki ta Tura kafin tace"Bafa kom..! Bata karisa ba ya make bakinta yana Fadin"Bani kafin nayi kasa kasa Dake mara kunya..! Hannunta Dafe da baki da mikamai ya karba Daidai sanda Ya Jafar ke fadin"Me kuke yi anan da Daddaran nan..! Gabadayansu sun kasa mgana Ya Nassir ya fara Duba bayansa yana Fadin"Inaga sai sun ajikinsu..Kai shamsu Duba Sanda don Allah..! Ya karishe Fada da karfin daya Janyo Hankalin Danmallan kansu ya Zura wayarsa gaban Aljihun farin yadi Riga da wando Dake jikinsa. Shamsu Daman tun farko ya fito jin haka yasa ya shiga Dakimsu ya Fito da wata Bulala mai kyau katuwa da ita yake duka A islamiya Ai Hanne da Hamida na ganin ya mikoma ya Nasir har sun Fara Nade Hannun riga suka Duka harda Zafira Data fara fadin"Wlh ba komai..! Sai kuka ya Uzairu ya Bude ledan sai ga Nama da Sauri yace"Ya jafar nama ne aledan nan..? Gabadayansy suka ce Nama..? Cikin mamaki Har da ya Danmallan Daya kariso wajen basu sani ba. Da Sauri zafira tace"Eh nama ne..Dama Dama..Amina ce ta sato a Kitchen shime muka zo nan ta san mana muna ci ammh Wlh bamu komai ba..Amina ce ko Hamida..? Hamida da Hannr sun kasa mgana Amina na Tsaye ko gizau. Ya Jafar yace"ai ta saba indai Satan Nama ce..Amina ta saba..! Ya Danmallan sai Lokacin ya Fahimci mganar ya kuma kare ma su Amina Dake wajen kallon idonsa ya Fada kanta yadda take wani Juya ido. Aransa yace"Again..?satan nama..? Meke damun yarinyar nan..? Ya Nasir ya kalli Amina yana Fadin"Anan gidan ne kike mana Satan nama..?kin ce abaki an hanaki ne..? Ya karishe fada cikin Tsawar dayasa Bba Mallam da Aba Dake cikin Falon zaune suna mgana sai da sukaji. Amina kuwa baki ta Murguda kafin tace"Ni ba barauniya bace..Ba sata nayi ba..! Ya Nasir yaga sanda ta mai haka yasa yacDaga Bulalar ya Shimfida mata yana Fadin"Karya zan miki..?kuma ni kike juyama baki zaki gane yarinya kwana Biyu jikinki na kaikayi..! Ya Jafar yace"Dake ta shegiya bakinta baya mutuwa..! Amina ko ko gizau ya kara Lafta mata wannan karan da karfi tace"Ai ba Sata nayi ba..ni ba barauniya bace..! Dukanta yake tana mgana su Hanne sun koma gefe har sun fara Hawaye.. Ya Danmallam mamakin Taurin ran yarinyar yake gani da Har yanzu ko Dukawa batayi ba kuma bakinta bai Daina mgana ba Su ya shamsu na gefe suna Dariya. Ya Danmallam yaga dukan yayi yawa yasa yace"Kai Nazir bar dukanta hakanan mana..! Ya Jafar yace"Ka bari ya Daketa baka ga bata da kunya ba ai tare sukayi Laifinta da yan"uwanta meya su ba"a Dake su ba..! Sai ya kasa mgana Idanuwanta yake kallo ko kwwllah basu Tara ba kuma bata tar dukan ka,Idonta kyam ba ko alamin nadama ballatana ta bada Hakuri. Yana auna Shekarunta ne har ya isa ta Zama kangararriya irin haka..? Yana cikin wannan Tunanin yaji mganar Baba Malam a sama yana Fadin"Kai kai Nasiru..Kaga naka nan..?ka samu jaka ne dake dukanta kamar ka samu namiji Dan"uwanka..? Sai Lokacin suka Lura dasu shi da Aba suna Tsaye ran Malam ya baci da azama ya kariso wajen Har Akyabban Dake jikinsa na neman Rinjayansa. Gaban Nasir ya tsaya ya Fizge Bulalar yana Fadin"Sau nawa zan gaya muki ba kyau Horo da duka..?Wlh banta Hora ku da duka ba sai Nasiha mai yasa kuma bazaku yi haka ba..? Ya nasir kansa na kasa yace"Baba ra..! Hannu ya Dagamai Lokaci daya yana Fadin"Bana son jin komai..Bana son Sarkaci kai Umar agabanka suka Tasa yarinya karama da duka baka Tsawatar musu ba..! Danmallam ma ya kasa mgana Dakyar yace"Kayi hakuri Baba..! Aba Dake gefe yace"Baba da kar barsu sun mata Hukunci Amina ce..Amina ai bata jin mganar kowa..! Aran Danmallam yace"Kenan ta gagara..! Baba Mallam ya Dagamai hannu yana Fadin"Kaima ka fita idona Sa"idu..! Jin haka yasa suka fara basa Hakuri ko kallonsu bai yi ba ya Juya ga Amina Data ga Baba mallan ta fashe da kuka Tana Fadin"Ce min fa yayi barauniya Baba..Ni kuma bana sata Daga na Diba naama shikenan..! Baba malam ya rikota yana Fadin"Bai kyaita ba..Mamata ai ba ta sata..Kuma naman da kika Diba ai na Gidanku ne ba wanda ya isa ya hanaki daina kuka Share hawayenki kinji..! Yana Fada yana goge mata Hawaye Ya Danmalam mamaki ya cikasa ya Tabbata ko cikin kannensa bai taba ganin Baba mallan yayi ma wata haka ba..Kenan ita wannan Dabam take.? Su ya jafar ko basu mamaki ba sunsaba ganin haka. Har su hannen haka ya taso su ya Damka musu Amina yana Fadin ku shiga Cikib gida..! Amina tace"Gidanmu muke kwana nan ya cika..! Baba mallam ya kalli su shamsu kafin yace"Ku rakasu sai kin tabbatar da sun shiga gida kana ku dawo..! Hakanan basu so ba suka tasa su Amina suka rakasu gida ya shamsu kam harda Tsaraban rankwashi. Baba malam bai Tsaya Sauraran ban Hakurin su ya jafar ba ya koma Falomsa Ransa bace. Aba ya Sauke Numfashi yana Fadin"Ku tafi gidajenku..Yau baba malam ransa ya baci..An taba Amina..! Ba wanda yayi musu suka juya wajen Motocinsu ya Danmallam dai na tsaye aransa ayyana wasu abubuwa kafin ya Tabe baki kawai.