← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 193

Sashe 60

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tundaga nesa yake kallon Amina Hankalinsa ya tashi da suka kariso yaga saman kanta da Ciwo an cire Pastan tuni,Da hanxari ya karisa gabanta yana Fadin"Meenata me ya sameki ne..? Yadda yake kallonta haka take kallonsa Hawaye sun tarun mata ganin yadda ya rame hamida da Hanne sai suka koma gefe suna kallon Ikon Allah ganin yadda Amina ta Fashe da kuka Aminu ya Rude ya rasa ya zai yi Cikin wani yanayi yake fadin"kiyi wa Allah Amina kibar kuka ki Fadamin me yake faruwana..! Hanne ce taga Tsayuwar bata da Amfani kada wani yazo ya gansu yasa tace"Amina ku shiga wannan..Kinsan dai Halin da ake ciki ko..? Tafada tana nuna mata lungin bayan gidansu da kai Amina ta amsa mata Kafin ta wuce tayi gaba shi kuma yabu bayanta su kums sai suka koma Cikin Haraban gidansu Amina suka Labe Jikin Get gabansu na Fadi Fat Fat suna Tunanin anya basu ganganci ba..? Amina kuwa suna shiga dan lungu ta Fashe da kuka ta Duke Amini yabita shima ya Durkusa Kamar yayi kuka yana Fadin"in kika cigaba da wannan kuka Amina zan iya shiga wani Hali..Kiyiwa Allah ki Fadamin abunda ya Faru..! Yadda yake mganar ne yasa Tsausayinsa ya kamata yasa ta Dago Cikin kuka ta fara Fadamai abunda ya Faru Tundaga farko sai dai ta boyemai Sakin da Aba yayi ma mamanmu akanta Ba saboda komai ba akwai Kunya ta ce an saki Mamanmu Saboda ita ta karishe Da Fadin"Soyayyarmu zata zama Tarihi ne Amin..Rabuwar mu shine Alheri Wannan abun da ya faru kadan akan wanda zai kara faruwa..Ni kaina nasan ba Domin baba Mallam na sona ba da yanzu wani Labari akeyi..Wlh bawacce tataba aikata abunda na aikata Bansani ba..Ba Laifina bane Soyayyace ta jani inda ta kaini In sonka ammh kayi hakuri mu Kareta anan akuma yau Amina..Don Allah kayi hakuri..! Kuka take kamar ranta zai fita Aminu yaji kamar ta Chakamai mashi da Sauri ya Mike yana Fadin"Bazai taba yuyu ba Amina..Ina bazan iya Rabuwa Dake ba..Laifinki ne da kin bari na gabatar da kaina da Duk haka bai Faru ba..! Yau ba sai gobe ba zan bayyana kaina Amina insha Allahu ke Rabona ce..! Jin kalamansa yasa ta Mike da Sauri Har tana neman faduwa tace"Kada kayi haka..Lokaci ya kure abunda zaka aikata bazai kawo mafita ba Amin..! Yana Kokarin Hana Idanuwansa zubar kwallah ya ke kallonta ta Duhun wajem Cikin wani yanayi yace"Mecece Mafitan AMINA..? Kada kice mafitan itace na Hakura Dake..Wlh in haka ta faru Zan Lalace Amina akanki ki taimakeni kimin Rai don Allah..! Yake fada sai Hawaye Gwiwansa ya saka a kasa yana Rokonta Kada ta barsa Amina ta Rude batasan sadda ta saka Hannu ta Dago Kafadun Aminu ba Cikin kuka take fadin"Don Allah ka tashi..Na shiga uku..! Yana Dagowa bai yi wata wata ba kawai ya jawota ya Rumgume kam kam kamar wanu zai kwaceta alokacin Inda tasan sanadin wannan Rumgumar da basu taba yi ba sai Ranar Zanen kaddaranta zata fara na Tabbata da Amina bata amince ba in da Aminu yasan sanadin wannan Rumgumar Amina zata haramta garesa da har Abada bai yarda yazo ba..Sai dai ina bakin Alkalami ya Riga ya Bushe..! Amina ta kasa yin wani motsi ballatana ta kwace jikinta Tayi luf akirjin Aminu yana Fadin"Bazan iya Rayuwa baki ba Amina..Kinsan ina sonki..kinsan ina sonki in kika barni ina zam saka kaina..? Amina alokacin Tunanin bai bata ta kwace jikimta tsausayin Aminu da soyayyarsa ya Rufe mata idon da bataji bata gani. Alokacin wani al"amari ya Faru wanda ya Faruwarsa ya Fallasa abubuwa Dadama kuma ya Watso wasu sirraka a waje alokacin kuma Zanem kaddaram Amina da wanda Allah ya Turo mata cikin Rayuwarta ya fara..! Suna cikin waannan yanayin suka ga an Dallaresu da Hasken Fitila Lokaci Daya Cikin Muryansa da ko barci Amina Take bazata taba bace Mata ba yace"Su waye anan..? Dam..! Gabanta ya amsa hakama na Amin arude ta Dago kanta Daga Kirjin Aminu karaf Hasken Fitila ya Hasketa Tar Cikin Faduwar gaba da wani yanayi ya Jafar ya Zaro ido Cikin Tsawa yace"AMINA..!!! Yadda ya Kira sunan ne ya Girgiza Zuciyar Amina Hanjinta suka Cure wajr Daya kuma har Alokacin Tana Rike da Aminu shims yana Rike d ita Rudewa yasa sun kasa Sakin juna..! Hamida Daga cikin gida ta kalli Hanne tana Fadin"Hanne gabana na Fadi..Inaji ajikina mun rusa komai fa..! Ita kanta Hannen Jikinta rawa yake gabanta na Fadi Cikin Tsoro tace"Nima Hamida..Na farajin wani iri na fara Nadama fa Hamida..! Hamida ta Bude baki zatayi mgana kenan Muryan ya Jafar ta shiga kunnensu sanda yake fadin"Innalillahi Amina me zan gani..? Iskancin naki har yakai kikawo wani kato a kofar gidanku kuns shanshanci Amina..! Dam gabansu ya fadi atare suka kalli juna suka zaro ido kafin suyi Rige rigen Lekawa ta kofa sai da suka kusa Sakin Fitsari a wando ganin ya Jafar Tsaye bakin lungun da su Amina suke ya Hsskesu da Hasken Fitila Fuskar nan kamar an aikomai da Sakon mutuwa.! Hamida ta Damke hannun Hanne suna karkawa Lokaci suka Hada Baki wajen fadin"Mun shiga uku..Mun kara saka Amina acikin Bala"i..! Agaban idonsu ya jafar ya taka ya Shiga lungu sai gani kawai sukayi ya Tunkudo Amina saida Hijabin jikinta ya Hardeta ta Fadi yaraf Cikin Fitan Hayyaci ya saka kafa ya Shureta yana Fadin"Tashi Tashi munafuka yau Allah ya Toni asirinki..Daman wannan Idanuwanki naki bakomai Cikinsu sai iskanci Kece Amina yarinyar dake Rumgume da wani kato Amina..? Tashi muje gaban Aba na Sanar dashi Abunda naganu tashi nace don Ubanki kafin nayi miki illah yanzu nan..! Yafada yana kokarin kara Shurinta da Sauri Aminu ya rikosa Cikin wani yanayi yana Fadin"Kadaina Dukanta..Don Allah ka Tsaya ka Bincika wlh ba abunda kagani bane gaskiya..Ina son Amina kuma auranta zan yi..! Ya jafar ya Fincike hannunsa bai yi wata wata ba ya Daga hannu ya Sharara ma Aminu mari lokaci Daya ya Nunasa da yatsa yana Fadin"Har kana da bakin mgana Lallatace kamar ka..?Allah ya isa Tsakanimu dakai Tunda kayi Samadiyar batamana kanwarmu kuma kabar kofar gidan kafin na Fito da matasan gidanmu su Illata yanzu nan..! Shi bai Damu da kansa ba Amina yake kallo tama kasa kuka Zuciyarta ya Soye ta riga ta sami ajikinta tanaji Ba wani Tsumi ba Dubara ayadda ya Jafar ya gansu Allah ne kadai zai iya Fitar da ita shiyasa ta kasa motsi ko mgana! Yana so yayi mgana bakinsa yayi Nauyi yana ji yana gani Ya Jafar ya isa ga Amina ya taso ta Bai yi wata wata ba ya Daga hannu Dama da Hauni ya Dauketa da maruka da sai da ta Koma ta Kife kamar zata Fadi ya Fizgota yana Fadin"Muje agaban Aba da mamanmu mai kareki..Ki Fada musu Tun yaushe kika fara Wannan Lalacewar Amina..! Ya karishe Fada yana ingizata gaba,Aminu ya taka ya Bisa ya Dagamai hannu yana Fadin"Karka Nuna min iskanku na yan Tasha..Nima In akabi ta wani Fanni na Fika tashanci wlh zan kara Dauke ka da mari Kaji ma na rantse in baka bace Daga gani na ba..! Ayadda Ya Jafar zai aikata Abunda ya Fada din sai ya koma baya Cikin Raunin Murya yace"Amina komai zai yi Daidai..Zan tafi Yola...su Alhaji Baba zasu zo nema min Auranki..! Amina tana jinsu tana so,tacemai kada yayi haka,ammh kuma a wannan gabar bazata iya mgana ba Domin mganar bata da wani amfani..! Hamida da Hanne suna jin Bude gidan ya Jafar suka Rumtuma zuwa Cikin gida ba inda jikinsu ba rawa Saboda Abunda zai iya Faruwa yau..! Haka Ya Jafar yake iza keyar Amina kamar wacce tayi sata Yana tafe ya Dukanta Fadi yake"Amina kece Rumgume kike da wani kato..? Yaushe kika fara wannan lalacewae..? Yana Fadi yana Dukanta Saboda Wani Bakinciki ke kara kamasa in ya Tuna da yadda yaga Amina Rumgume jikin wani kato..! Hanne da Hamida Dakinsu Hamida suka Fada suna Haki ya Zeenatu na kwance ta Mike tana kallonsu,Cikin wani yanayi tace"Lafiyarku kuwa..? Kasa mgana sukayi jin Muryan ya Jafar Tsakar gida yana Kiran sunan Aba gabadayansu suka kara Tsurewa Hamida da Hanne suka kamkame hannun juna,Saboda Tsoro ya Zeenatu ne ta Mike tana Fadin"Muryan Ya jafar nake ji..? Meya faru kuma..? Tafada tana mikewa Tsakar gida ta Fita Daidai Sanda Aba ya fito shi da Yaya Sai kuma Mamanmu data fito Daga Dakinta Dankwali a hannu Tana Fadin"Lafiya hayaniya me nake ji..! Ya Jafar Amina ya Tura gaban Aba sai da ta Fadi cikin Fushi yake fadin"Aba Gatanab ta fada muku tun yaushe ta fara Lalacewa..Yanzu nazo zan karban mganin da za"a shafa mai sunan Mallan akansa kawai naci karo da yarinyar Rumgumr ajikin wani Dan iskan kato ajikin gidan Aba..! Gabadaya jikin Aba sai ya fara rawa Yaya,kuma Kirjinta ne ya fara Lugude Yayinda Mamanmu ta saka Salati tana Fadin"Innalillahi...! Haka kawai take fada Hanne da Hamida dake cikin Daki suka kalli juna suka Gwalo ido,ya Zeenatu kuma Xuciyarta sai da ta amsa Amina bazatayi haka ba Halinta bane..! Ba wanda ya Lura da Aba Jiri ya kwashesa sai da ya Saka kafa ya Ture Amina Dake gabansa takasa kuka sai na Zucci Domin kukanta bazai taba Cetonta ba..! Kadan ya Rage bai Fadi ba Yaya tayi Saurin Rikosa ta fashe da kuka Bango ya Dafa yana Fadin"Jafar fitarmin da ita Daga gidana..Ka fita da ita ban Haifi Dan da zai zamenin zakka ta ficemin Daga gida..! Yake Fada sai hawaye Sharr Mamanmu ta Fashe da kuka tana Fadin"Na shiga uku ni balaraba..In ka Koreta ina zataje Abbansu..? Wlh Amina bazatayi haka ba Halinta bane..! Ta karisa wajen Amina ta Dago tans Fadin"Amina ki tashi ki fadamusu karya ne..Abunda Jafar ke fada ba gaskiya bane..! Da manyan Idanuwanta Take kallon Mamanmu Lokaci ya kure bazata iya kare kanta ba batasan sadda tace"Gaskiya ne Mamanmu..Gaskiya ne ya ganni..Rum..Rumgumr..! Bata karisa ba Mamanmu ta Dauketa da Mari Cikin kuka take fadin"Karya ne..Ba gaskiya bane..! Take Fada tana kuka kamar Ranta zai Fita Zuwa Lokacin hatta Hanne da Hamida sun fara kuka Aba kuma Yaya na Rike dashu Dafe da Bango Yana Hawaye..! Ya Jafar ya kalli Aba yana Fadin"Aba kadaina kuka..Wannan yarinya Dukan mutuwa zan mata yanxu nan..Wai har dan iskan yaron yana Fadin sonta yake yi zai aureta..! Aba ya girgiza kai yana Fadim"Na Rantse da wanda
Chapter 60 · 0% Book details