← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 193

Sashe 84

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sum sum suka mike hanya maimakon su koma gidan Baba mallam sai suka koma gidan Aba ko motsin kirki sun kasa Baba mallam baya wajen ya koma Falonsa shi da Aba
Sakina ranta yayi Dadi ganin ba mgana mai Dadi Umar ke fadama su Amina ba sai ta saki Fuskarta.
Su Haj.Nasara suka ssaka amaran Amota tare da rakiyan yan gusai da yayyinsu da kannensu suna kuka kamar ransu zai fita suka mika hanya sai Fatan Allah ya Kiyaye su.
Kafin La"asar kofar gidan ya zama wayam ba Jama"a Danmallam gidansa ya koma ya Huta Aliyu kuma ya koma Dutse dazu.
Hankula basu kwanta ba sai da Amare suka natsu adakinsu Jidda na Tare da Ya zeenatu a Kaduna sai gobe zata koma kano hakama Abida sai Dare suka sauka su Anty Amarya sun gama gyara komai gidan Zahra suka koma zasu kwana sai gobe zasu dawo..!
Su Amina kuwa ba wamda ya kara ganinsu har aka kwana suna Dakin yaya chan suka yada Zangonsu ammh fa duk sun yi sanyi ba ya zeenatu ba Abida gida yayi shuru sai su kadai kuma aranar ma su zafira suka koma harda ya Jamila,sauran baki ma suna ta wucewa tunda an gama Biki sai kuma Taro ya tashi.
Su Anty Amarya da wuri suka iso wajen La"asar,suka yada zango Shashen Hajiya suna fadamata karan Dangin mallam tunda uban yaron dan bazanga ne kuma matsayin kawu uban yaron yake ga mallam..!
Hajiya Babba ta kudira abu aranta sai dai batace ma kowa komai ba ta bari sai angama Hayaniyar biki sannan zata Furta abunda ta yanke.
Sai ranar Lahadi gidan ya watse harta yaran sun koma gidajen auransu,Ranar Hajiya keda shashen Baba mallam bayan sallar isha"i Mallam da Aba sun dawo shashen mallam din kamar yadda suka saba suna Hira.
Sai ga Hajiya ta shigo Cikin mayafinta yanzu shashen nata ita kadai ce Hanne ta mata yaji tana tare da su Amima agidan Sa"idu.
Lokacin da tayi sallama ta shigo gabadaya suka dago suna amsa mata Mallam ya tareta da Mirmishi yana Fadin"Zainabu abu mai Tagwayen suna..Uwargida sarautar mata..!
Yar dariya tayi batace komai ba Aba ne yace"Kuma Amarya ba..!
Baba mallam yace"A"a uwargidan dai Ni da zainabu ai mun tsufa kodon baka san tsufan ta..!
Aba na Dariya yace"Allah ya kara girma mallam..!
Hajiya na zama gefen mallam tace"Ameen kyalesa Sa"idu..Marliya ce Amarya barni in rike Tsufana..!
Aba yace"Haka za"ayi Hajiya..An watse taro lfiya yau ina sauri ana jirana na fita ban leka mun gaisa da ban gajiya.ba..Angode Hajiya Allah ya kara girma..!
Hajiya tace"Ameen bakomai..Tunda naga ban ganka ba nace uzuri ya rikeka..Ina yaran nan..?Hanne ma tamin yaji wai shashena ba Dadi ba kowa..!
Baba mallam yace"Daman ni na sani..Ranar da Abida tatashi..Sa"idu da Balaraba zasu ja Hannatu..!
Hajiya tace"ba ruwansu mamarkace da Hamida suka jata..!
Mallam na Dariya yace"To shikenan ku kyalesu ke hajiya kiyi zamanki ke kadai tunda kin zama giwar mata ki aurar da naki ki hada har da wanda ba naki ba..Allah ya kara girma da Lafiya Hajiya..!

Tana Mirmishi ta amsa Ameen kafin Aba yamike yana fadin"bari na shiga gida..!
Hajiya ta kallesa tana Fadin"koma ka zauna Sa"idu mgana nake so muyi..!
Ba musu ya koma ya zauna Baba mallan yace"Tunda na ganki daman nasan akwai mgana..!
Hajiya tace"Ina Danmallam..?
Bai shigo wajenka ba..?
Baba mallam yace""Yau kwata kwata ban gansa ba bai shigo anguwan tamu ba..yadai kirani da Safe ya gaisheni..!
Aba yace"Yaje gidan gona yau..Tare mukayi La"asar dashi ma..!
Hajiya ta fito da wayarta tana Fadin"Bari na kirasa.!
Daga Aba har Mallam ba wanda yayi mgana har ta Kira Danmallam bayan sun gaisa tace yazo gida shashen mallam gata nan tana jiransa.
Daganan ta datse kiran Mallam ya koma ya kishingida jikin kujera daman da yaga Yadda Hajiya ta shigo yasan yau Rigima take ji kuma ga Duk alamu kawaicinta ne ya kare kan Umar yau zai sha Fada..!

Tunda ya Dawo daga gidan gona bai kara Fita ba yana gida,Cikin Dakinsa Sakina kuma tana falo tare dasu Sa"adatu da suka zo mata yini,Sallar mangariba ce ta fitar dashi sai da ya Tsaya yayi sallar isha"i a Hanya sannan ya shigo gidan sai kuma yaga su Sa"adatu basu tafi ba ya farama Sakina Fadan meyasa sukayi Dare Cikin Basar da mganrsa tace"Nan zasu kwana fa..!
Kallon bacin rai yayi mata kafin ya kalli Sa"adatun datayi Fiki Fiki da ido yace"Ke mallan yasan kun zo nan zaku kwana..?
Kai ta gyada alamun A"a Harara ya sakar mata kafin ya wuce cikin Dakinsa Uzairu yaso ya kira yazo ya kaisu gida sai gobe yaso ya leka chan din sai ga Kiran Hajiya gabansa sai da ya fadi ba kasafai Hajiya ke kiransa ba yasan akwai wani babban Dalili kuma tace afalon Mallam.
Ko zama bai yi ba ya fito ransa bace Daman shi da Sakinan haka suka zo kowa na Harkan gabansa ya riga ya Dauke mata Tunda ya Lura bai isa da ita ba,Yayi alkwarin wlh bazai koma da ita ba nan zata zauna bashi da kudi bazai matsa ma kansa ba kuma ta nuna tafi son zaman nan din tabbas zata gane bata da wayau..!
Yadda taga ya fito yana cika yana batsewa sai da ta sha jinin jikinta da Sauri tace"Bari na kira Anty ko cikin mazan nan wani yazo ya kaisu..In kuma Idi na nan shikenan..!
Ko kallonta bai yi ba ya fice yana cema Sa"adatu"Dauko Hijabanki mu tafi..!
Daman ita da Sabeeha ne suna Shirye tunda yayi mgana basu ga ta zama ba suka mike tama kasa bin bayansu Saboda mamaki tabe baki tayi aranta tace sai kuma kayita yi ni dai na Riga da na nazo..!
Tsawon mintuna Talatin sannan ya shigo Falon a waje ya ijiye motarsa ya Sauke su Sa"adatu suka nufi Cikin gida yadda ya iske Aba da Mallam ga Hajiya yasa yaji kafafunsa sunyi sanyi Jikinsa ya basa wani Laifi ya aikata Domin Hajiya ko mallam ko Aba suke da Alhakin Zartar da kowani Hukunci..!
Gefe ya zauna bayan yayi sallama kansa na kasa ya gaishesu suka amsa mai Cikin Sakewa har mallam na mai Tsiyan"Umaru na kusa daina ganeka..Ka koma sak Balarabe..!

Ballatana daman shigar Jallabiyace ajikinsa mai Kalan ruwan madara kansa ba Hula gashin kansa ya bayyana..!
Kansa na kasa bai ce komai ba Aba ne yace"Ai yama koma Balaraben Mallam harta Harshensa ya koma nasu..!
Mallam na Dariya yace"Na bar ma Kattab.ni nan ya"yana sun isheni..!
Hajiya na jinsu batace komai ba Sai da ya Dago yana fadin"Hajiya gani nazo..Allah yasa Lafiya..!
Hajiya tace"Eh na ganka..!
Mallam mganar tarewar Amina ne dakace nan da wata shekarar ina so ka ijeta gefe..Ba shawara bace mallam Umarni ne amatsayina ta mahaifiyar Danmallam...Zai tafi da matarsa chan inda yake aiki..!
Daga Mallam har Aba da Danmallam baki suka saki suna kallon Hajiya wacce Daga yanayin mganarta zakasan ba wasa aciki.
Danmallam gabansa ke fadi Hajiya zata Takaitasa ina zai kai wannan yarinyar a yanzu kuma..?
Mallam ne ya katseta da Fadin"Meyasa abaya kika yarda da hakan yanzu kuma kika ce ba haka ba..?
Kai Tsaye Hajiya tace"Kada ku matsa sai kun ji Dalilina don Allah..Bazan Fadama kowa ba..abaya na yarda da hakan ne saboda ina ganin shine Daidai ammh Shekaranjiya na Fahimci munyi kuskure Mallan..anyi mai Wahalar an Daura aure To me zamu jira..!Biki ai ba Dole bane..Saboda haka in zai koma ya tafi da matarsa shine mganata..!
Aba ya bude baki yace"Hajiya hakan kamar ba adalci bane..Shi ai bai yi shirin haka ba..Ta yaya Lokaci daya kuma atakuramai..?
Hajiya ta karkace kai tace"Sa"idu ina da Dalilina..Ni ba shiri nake so yayi ba..Ko ya shirya ko bai shirya ba Insha Allahu da Mamah zai tafi in har na isa Dashi..!
Tafada tana kokarin mikewa da Sauri Mallam yace"Koma ki zauna Zainabu..Muyi mgana..!
Ba musu ta zauna Umar ya kallah yaga kansa na kasa sai zufa yake yi sai ya bashi Tsausayi bai da Hayaniya sam mai Biyayya ne da bin Umarni.
Yasan bazai taba musa mata ba har abada.
Cikin Salama ya kalli Hajiya na wani Lokaci kafin ya koma ya kalli Danmallan lokaci Daya yana Fadin"Umaru kaji abunda mahaifiyarka tace..Kuma bakace komai ba..!?

Sai da ya Hadiye wani miyau mai zafi kafin yace"Mallam bani da tacewa..Duk abunda Hajiya tace shi za"ayi..!
Baba mallan yace"Kana da inda zaka ijiyeta in ka tafi da ita ne..?Ko kuwa zamanta achan bata da takardan zama ba Takura bane..?
Sai da ya Dade bai yi mgana shi kuma Mallam Dubara yayimai su samu su lallaba Hajiya yasan da matsala rana Tsaka ya tafi da Amina gari ba kusa ba kuma ba kasarsa ba sannan abu Lokaci Daya ba shiri..!
Yasa yacemai haka domin ya samu ya kwaci kansa yana so Hajiya tabi komai a sannu sai dai baya so taga kamar yaki Sauraranta da kuma bata goyon baya..
Cikin Dattakonsa yace"Muna Sauraranka..bakace komai ba..!
Hajiya tace"Mallam basai mun jirasa ba..Koda bashi da inda zai ijiyeta sai ya tafi da ita ai ba'a Daji yake kwana ba..!
Da sauri mallam yace"A"a ba"a haka..Ki bari yayi mgana kada ki manta kasar dayake aiki ba Kasar sa bace nan din dai nan ne Kasarsa..!
Dole tayi shuru shi kuwa ya kasa mgana Aba ma haka Domin hajiya Fuska ta Hade ba Fara"a ballatana su ga wani Rahma tana so ne ta Nuna ma Sakina da Amarya Danmallam ya zauna acikinta na wata tara..!

Cikin karfin Hali ya fara mgana yana Fadin"In da son samu ne mallam.Hajiya ta bari in na koma sai na Fara cikun cukun sama mata takardan zama a kasar..sannan da wajen zamanta gidan da nike ciki karami ne Ni da Sakina da Sarood ma maallam maneji mukeyi yayi mana kadan gidana na nan yafisa girma Wlh Tallahi na rantse da Allah in na Tafi da ita zamu Takura mallam..Sai dai bazan iya bijirema Umarnin Hajiya ba..Sai ta fara shiri Jafar zai zo ya kaita ayi mata passport saboda Visa Nan da kwana Hudu nake so na koma..!
Daga Aba har mallam Tsausayinsa ya Rufesu Umar mutum ne mai Ladabi da Gudun bacin ran iyayensa,Hajiya kuwa bata Damu ba illah kada kai datayi tace"Ko ya ya ne dai tunda da inda zata zauna kamar sauran ka tafi da ita..Ka tafi da ita nace UMAR..!
Chapter 84 · 0% Book details