← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 193

Sashe 6

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Dariyan me kukeyi haka ne..?
Da Sauri suka jiyo suna kallonta Hajiya Babba tana sanye da Doguwar rigar Shadda ajikinta Mace ce Doguwa ga kiba,Akallah ta bama Shekaru hamsin baya sai dai Hutu sun Lullube shekarunta Da ka ganta Kaga su Hanne da Ya Aisha Saboda suna Kama da ita sosai.

Amina ce ta mike zaune tana Fadin"Hajiya ina yini..?
Hajiya na Daga kofar Dakin tace"Lafiya lau Mamah..Sai yau nake ganinki..?
Amina na Dariya batace komai ba Bata iya maidama Hajiya mgana Saboda Kirkinta,Mamah take ce mata Saboda sunan Mahaifiyar Baba Malam Amina kec dashi basa Kiran Sunanta ita tace Mamah shi yace Mamana..!
Hanne ce tayi zaraf tace"Yau ma Laifi Tayi Hajiya..!
Hajiya ta kada kai tana Fadin"Ohh maamah duk baki ji nasihata ba ko..?Don Allah ki natau ki dinga jin mgana Bana son wannan Korafin Kowa yace ke Babanki Sa"idu kullum Mganarki yake yi hakama iyayenki mata Don Allah Mamah ki rika jin mgana ki zama kamar kowacce y"a acikin Gidanan..!
Zaku Dauka yadda Amina tayi shuru Tana jin Fadan ne nan kuwa bata ma Fahimta Domin indai wannan Nasihan ne ta Haddacesu Daga bakin Hajiya da Baba Malam
Ammh Cikin Dan kada ido tace"Shikenan Hajiya..!
Kallon Hanne tayi kafin tace"Ku tashi kuyi sallar isha"i gashi chan ana Kira..Ku fito muje falon Malam mu ci Abinci..!
Da Sauri Amina tace"Hajiya zamu ci namu anan..!
Saboda in akwai abunda ta Tsana wannan al"adar ta gidan mallam Akwai Wadanda bata son Haduwa Dasu acikin gidan nan.
Hajiya ta juyawa tana Ficewa Lokaci Daya tana Fadin"Ba ruwana ku da Babanku..!
Sai da Hajiya ta fice ne Hanne tace"Meyasa indai kikazo gidanan bakya son zuwa Falon Baba cin Abinci..?
Amina tace"Ba wani dalili..Kawai bana son ganin matar nan ne..!
Hanne tace"Wai Anty Amarya..?
Amina ta tabe baki kafin tace"Itafa Bata da Mutumci Ni tun Ranar da Fada ya hadani da Sa'adatu ta Shigar mata Har tana Fadin meyasa ta Hada kashi da irin Tsiya kamata..?na tsaneta Daga ita har ya"yanta kinsan ko a makaranta bana mgana Dasu..kuma ina jiran Watarana yarinya ta shigar min Harka na Sauke mata Hayakin kaina..!
Hanne ta mike tana Fadin"Amina baki da mantuwa..!
Amina tace"Bana manta wanda yayimin Alheri..Da wanda yayimin Sharri..Kina wani abu kamar kuma jin Dadin zama da ita kuke..Saboda Baba malan ne take Rage wasu abubuwan ammh da badomin haka ba Allah kadai yasan iskancin da zatayi..!
Hanne tace"Ni ina ruwana da ita..Iyaka in mun hadu na gaisheta ko Shashenta bana zuwa sai ta kama..Sa"adatu ma ta Dade batamin mgana kinsani Saboda ke..!
Amina tace"Share banza..Itace akasa mu muyin gaba badai ta Mutum ba sai Allah..!
Hanne na Dariya tace"Kinsan fa Diyar yayarta Ya Dan mallam ke aure ko..?
Amina ta yamutsa Fuska tace"Haka naji shiko Duk yanmatan Duniya sai ita .?
Hanne tace"Kowa haka yake fadi..in kinga ya"yan masu Sarauta da masu kudi da malamai yadda suka rika kawo ya"yansu wajen Baba ammh Duk yaki sai kawai Rana Tsaka yace Anty Sakina yake so..Kinsan tare tatashi wajenta dasu ya Jidda !
Amina tace"Eh mana na Tuna lokacin duk da bamu da wayau tafi kowa iskanci kamar gidan Ubanta..Nifa inaga Tun da akayi auran ban kara ganinta ba Duk zuwan da sukeyi har su tafi bama Haduwa har shi Ya D'anmalam din bazan iya Tuna kamaninsa ba gaskiya..!
Hanne tace"Kinsan bai cika yawan zuwa ba..?in yazo ma shi kadai kwana Biyu yake ya koma in kuma Zai zo da ita sai karshen shekara kuma suna Gidansu Dake nan Kano Road sai dai in sunzo gaida su Hajiya kuma Har gidanku yana shiga gaida Yaya Hajiya tace Dan Dakinta ne sosai..!
Amina ta mike itama tana Fadin"Ke ni ban taba ganinsa ba..Kina da Hotonsa .?
Hanne tayi Dariya tana Fadin"Sha Kurumimki naji Hajiya na Fadin nan da wata Daya suna na nan zuwa Saboda Mganar auran su ya Aisha..!
Amina ta kwalalo ido kafin tace"Kice muna da shan Biki..!
Hanne tace"Wlh kuma har dasu ya Sadiya ma za"a Hada fa...kilama Har dasu Ya Zeenatu..!
Amina tayi wata Dariya kafin tace"Allah yasa hardasu..su tafi su barmana Gidan dagani sai Hamida muci uban juna..!
Dariya suka saka Gabadaya Harta Tafawa suna cigaba da Hiransu Salla sukayi Tunda suna da alwala Sai da suka idar kana suka fita Falo ba kowa suna Falon Baba Malam Kichen din Hajiya Hanne ta shigo ta Dibo musu Doya da miyar Stew nan falo suka Fito suna ci suna Hira da Dariya Daga ganinsu kasan kaunar da suke ma juna Daga Allah ne.
Sai wajen 9:30am na Dare su Ya Aisha da Ya Abida suka shigo Ya Aisha Daki ta wuce ita bata cika mgana ba Ya Abida ce ta kallesu tana Fadin"Meyasa baku je Dinner ba..!
Amina ce tace"Mun yi namu mu kadai..!
Kai ta kada kafin tace"Sannu Shafaffu da mai..To Baba na kiranku..!
Amina Rada take ma Hanne tana Fadin"Mijin Ya Abida zai sha Gulma..!
Hanne na Matse Dariyanta Ya Abida ta Zaro ido tana Fadin"Amina me kike cemata akunne gulmata ko..?
Da Sauri Amina tace"Labarin wata yarinya mai Bala"in saka ido nake bata..yar ajinmu a islamiya..ko Hanne..?
Hanne ta Daga kai da Sauri Abida Wucewa tayi tana Fadin"Sai na Daki bakin yarinya yanzu nan..!
Amina ta Rakata da Daga Lefe tana Shigewa suka kyakyalce da Dariya
Saida suka gama Hanne ta kwashe komai takai Kitchen Amina tace"Dauko Hijabina na tafi gida Hanne..!
Hanne tace"Kiran baban fa..?
Tace"In mun fito sai na shige gida..!
Hanne tace"Nazata nan zaki kwana..!
Kafada Amina ta Daga kafin tace"Anki din..Ina fa Kirge nice na kwana Na karshe..Malama kece fa da kwana..!
Hanne tace"Dillah zan kwana nima gobe..!
Amina tace"Yauwa sai na baki ma Labarin wannan litaffin..!
Da Sauri Hanne ta Danne bakinta tana Nuna mata Dakin dasu Ya Abida suke Amina Tayi Dariya Kafin tace"Sai me..?Allah yasa ma suji..!
Hanne dai wucewa tayi ta barta Tasan wacece Amina bata da tsoro komai zai Faru sai da ya faru ita zata saka a uku.
Hijabinta ta Dauko mata itama ta Dauko nata tana Fadin"Muje na Rakaki..!
Fita sukayi Daga Dakin suna Tafe suna Hira Amina na Zagin malamar hausansu har tana kwaikwayon mganarta Dukkansu Jss3 suke sai dai Amina Ita da Sa"adatu suna A ne yayinda Hamida da Hanne ke ajin B.
Suna tafe har Shashen Baba Maallan Amina tasan inda suka zo yasa ta Bude baki Daga Kofar Falon ta kwarara Sallama.
Hajiya Dake Cikin Falon gefen Baba Mallam Dake zaune kan kujera yana Duba wani Littafi tace"Ga Mamar taka nan ta iso..Kaji Doguwar sallama kamar ta Kirki..!
Tafada Cikin Zolaya yana Duken yace"Ta kirkin ce mana Zainabu...Mamana Harda yarinta ajikinta da ta kara girma ta mallaki Hankalinta sai dai Labari..!
Kai kawai ta Kada tana Hangen abunda ba Haka ba kan Aminar ita ta amsa Sallamar ta Amina Hanne na Shirin Shiga ta riketa tana Fadin"mu shigo baba cikin harshen larabci
Shi kanshi sai da ya Murmusa ya Dago Fuskarsa Daya cika da Farin gemu Cikin Dattakonsa yace"Na"am...!
Baisan meyasa ba Ko Muryan yarinya yaji sai yaji wani Dadi yana mata kauna wanda ko cikin ya"yansa sai an Tona Amina haka Allah yayi ta mai Farinjini ne Malam yana sonta Saboda Allah da kwazonta Duk da take bata maida hankali Kokari gareta yana ganin makamceceniyar kwakwalwarta Data D'an malam awajensa da itace kadai yake Dogon Mgana da Larabci bata kakare ba Tana Jin Labarci Fiye da yadda kowa ke Tunani kuma Bayan Baba Malam ko Baba Sa"idu baisan wannan baiwar nata ba..
Sannan ko makaranta sun sani tana da Jawo Jidali ammh itace Over roll acikin ajinsu har mamaki ake yi masu Hassada da ita na Fadin Cuta akeyi Amina jidalinta baya barinta gane Karatu shiyasa Sa"adatu ke Kishi da ita matuka basa Shiri ko a islamiya da hadda Itace Zakka kamar yadda ta Fita Zakka acikin gida Daga waje ba,sannan Amina Zakka ce sai kowa Tunani yake sa"a take ci Saboda ba"a Taba ganin tabama karatu Muhimmanci ba nan kuwa basu sani ba Tana da baiwa sau Daya zata ga Abu Ta kuma karantshi ta gane shi kuma ya Zauna Bisa kanta Har Abada.

_Naji Dadin yadda kuka karbi Labarin nan kamar yadda kuka saba karban Duka Labaraina Naji dadi nagode matuka Allah ya bar zumunci nayi alkawarin bazan baku kunya ba_

*Janafty*
[11/6, 3:34 PM] Sweet sis: *TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Sadaukarwa ga Halima yusuf gwarzo(Besty) Alherin Allah ya kai miki adukkan inda kike*

_Intelligent writer's asso_

*🅿️03*
Chapter 6 · 0% Book details