← Book details Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 193

Sashe 20

Ta Fita Zakka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sanda ya gama wayar ajiyar Zuciya ya Sauke lokaci Daya yana Sauke wayar Daga kunnensa,kusurwan Falon Mallan yake kallo inda Cabet din Jerin Littafansa suke,Tunani yake yi yazai yi ya Sanar da Hajiya ya kara aure..?ga Halin da Sakina take Ciki Tunda ya Fadamata an Daura musu aure da Sarood take kuka taki cin abinci ta Daina mai mgana Har yau da suka so gida Allah ya gani bai taba son Sarood ba ammh Tama da kimar da bai isa ya Wulakantata ba.
Daga Bayansa yaji Baba Sa"idu na Fadin"UMAR Baba mallan na mgana..?yace ko baka gama wayar bane..?
Jin Haka yasa Lokaci Daya ya Dago kansa Tare da Juyowa Ya fara Tako Doguwar Kafarsa Zarara saman Tattausan Cafet din Dake Falon Malam din
Tsarki ya Tabbata ga Shugaban Hallitun Duniya..Domin Tsabar kyau da Zati da kwarjini wajen bawan Allah nan,Shi ba Fari bane kuma ba Baki ba Fatarsa wani irin Fatace mai kalan Haske kamar na yan Moroci Tattausa Saboda jin Dadi da Hutu tana Sheke Dogon Namiji ne wanda ake Kura Ingarma yana da Fadin Kirji Daga Kafadamsa zuwa cikinsa ya Bude,FUSKARSA doguwa ce Sambal masu Dauke da matsaikatan Idanuwansa da Gashin gira dana Ido..Hancinsa Dogo ne ammh ba Sosai ba wanda ya karamai kyau da Zatinsa Sannan Bakinsa Zagaye da Saje baki wanda ke karamai kwarjini Daga kasan gemunsa kuma yabar gemu kadan wanda bau wuce kamu Daya ba.
Wanda ya Dace da Zagayyen Bakinsa mai dan Fadi kadam da Tudu,yana Sanye Cikin Pakistan Riga da Wando na yan Saudiya Rigar Tawuce gwiwansa Sannan wandon bai rufe kwarin Kafansa ba Kansa Sanye Cikin Hula irin ta Larabawa karamar nan wacce iyakarta rabin kansa mai Kulim Gashin Sakan Hulan Daga sama Wanda ya ba Sumar kansa Daga kasa zuwa sama sama Bayanna Duk da ya Asketa ammh gatanan tayi kwance gwanin Burgewa sannan Goshinsa ga Bakin Tabin sallah nan wanda ke karamai kwarjini da Haiba.
UMAR YUNUS ABDURRAHAMAN BAZANGA kenan Namiji kwara Daya Tal da Bayan Sa"idu Mallan ke matukar kauna acikin Ransa a Cikin Jerin ya"ya ashirin din da Allah ya basa mai tarin baiwa da Allah kadai Daya Hallicesa ya sani mai kimanin Shekaru Talatin da Takwas zuwa da Tara aduniya.
Har ya kariso ya zauna Kusa da Baba Sa"idu Baba Malam da Baba Sa"idu basu daina kallonsa ba.
Suna kara yaba kyan zatimsa ko su kansu kwarjini yake musu Tabbas Qur"ani ba karya bane kana ganin Mahaddacinta kake ganewa Saboda Natsuwar dabam take.
Kansa na kasa Cikin Muryansa mai Zaki yace"Afuwan Baba..na kira Hajiya ne..!
Baba Malam ya gyada kai kafin yace"Kace Shashenta ka Sauki bakuwar taka ko..!
Kansa na kasa ya gyada kai Baba malam ya cigaba da Fadin"Hajiya ko bata san mutum ba ita din mai karamci ne..Zata karramata matuka..!
Baba Sa"idu yace"Sosai shiyasa nace a kaita chan kaawi..!
Baba Malam yace"Da kaji an ambaci Hajiya Jikin ka na rawa ka yabeta..Ina mamakin yadda ZAINABU ta kwacemin SA"IDU NA..!
ya karishe Fada Cikin Zolaya.
Baba Sa"idu na Dariya Danmalam kuma Mirmishi kawai yayi.
Kafin Baba Sa"idu yace"Haba dai..Ai Tsakanin Uwa da da akace sai Allah baba..Kuma haka Tsakanin Uba da Dansa sai Allah har Abada Sa"idu na Baba Malam ne ba shi ba duk wadanda ke karkashin naka ne Baba..!
Baba Mallam Zuciyarsa kamar Farar takarda ya gyada kai kafin yace"Allah ya albarci Rayuwarka Kai da iyalanka Sa"idu..!
Suka amsa shi da Umar atare,Kafin Baba Malam yace"Ni na hana Sa"idu ya Fadama Hajiya komai..na bari sai ka zo..Ko sauran abokam zaman nata ban Sanar da kowa ba..Ina Fatan ka Fadamata ita Dayar iyalin naka ko..?
Kansa na kasa yace"Eh na sanar da ita tun muna chan..!
Mallam yace"Dakyau haka ake so..Allah ya zaunar daku lafiya..Sai ka zama jajirtattace adali zama da macen Fiye da Daya sai Adali Umar..Bana jinka nasan bazaka taba aikata wani abu mara kyau ba..Sannan itama Diyar Kattab din indai Halin Mahaifinta ta Biyo Har Abada bazakayi nadama ba..!
Baba Sa"idu yace"Allah ya sa...!
Kansa na kasa shidai bai ce komai ba basu Damu ba Sanin Halinsa Shuru Shuru bai da Hayaniya.
Baba Malam ne ya kalli Baba Sa"idu yana Fadin"Sa"idu ka tafi wajen aika..Nima anjuma kadan zan Gidan Sarki Tun jiya Sakon sa ya isoni yana son ganina..Umar kuma ya shiga Cikin Gida ya gaida iyayensa zuwa anjuma sai mu zauna gabadaya domin a gabatar da Bakuwar data Cikinmu Gabadaya..!
Baba Sa'idu ya jinjina kai yana ma Malam Allah ya kiyaye Hanya.
Tare sukayi mai Sallama suka Fice shida Baba Sa"idu sun Dade aharaban gidan suna jingine jikin Motar Baba Sa"idun suna mgana kafada na gugan kafada Malam na daga cikin Falomsa yana Hangesu da Wandow Falon Lokaci Daya ya saki kayattacen Mirmishi.
In ka gansu kamar wasu yaya da kaninsa uwa daya uba Daya ya Tabbata abunda bazai iya Fadamai bane yake Sanar da Sa"idu Akwai Shakuwa da Fahimta a Tsakaninsu Yana Daukansa kamar kaninsa Shima yana Daukansa kamar yaya kuma Uba agaresa
Sun dan jima suna mgana kan yana Fadamai bai Tsara Karim aure yanzu sai dai kana naka Allah na naka ne Baba Sa"idu na ta bashi Wasu Shawarwarin kafin suyi sallama ya Shiga Mota ya wuce Gidan gona yayinda Shi kuma ya Fara takawa yabar Filin Haraban gidan zuwa Shashen Hajiya ammh Kuma Ransa da Kallomsa na Shashen Anty Amarya yana Tunanin ko Sakina ta Daina kukan..?ya manta Rabonsa Daya ga taci wani abu sai ruwa kawai..!

*Janafty*
[11/3, 2:05 PM] Sweet sis: *TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Sadaukarwa ga Halima Yusuf gwarzo (Besty) Alherin Allah ya kai miki a dukkan inda kike*

*🅿️09*

Cikin Tafiyarsa ta natsuwa ya karisa Shashen Hajiya babba kamar yadda yake a ka"idarsa sai ya fara isa shashen Mallam sun gaisa sannan sai ya shiga cikin gidan Daya bayan Daya ya Bisu ya gaishesu.
Hajiya na cikin Dakinta har alokacin Daya shigo Aisha ce da Hanne har Lokacin afalon yana Shigowa Cikin Sallamarsa da Muryansa mai Zaki da Sanyi a koyaushe,Lokaci daya da kamshin Turaransa na Arab yayi musu Sallama..!
Gabadayansu suka mike Cikin Fara"a da Murnan ganinsa domin sun Dade basu gansa ba Tun Karshen wanchan Shekara sanda yazo Lokacin Duba Hajiya ce Datayi ta Fama da Kafa suna makaramta basu gansa ba kuma Kwana Biyu yayi ya koma.
Hannayensa duka Sanye Cikin Aljihun wandonsa ya Kariso Tsakiyar Falon gabadayansu har suna Hada baki wajen gaisheshi da yanayin Natsuwarsa ya kallesu yana amsa gaisuwarsu yana kara ganin girmansu acikin Idanuwansa.
Kai Tsaye yace"Hannatu Aisha meyasa baku je makaranta ba..?
Da Sauri Aisha tace"La yaya bana Fada maka ba..!
Sai Alokacin ya tuna da Sauri yace"ohm.Sorry na manta..Allah ya bada sa"a..!
Suka amsa da Ameen gabadayansu sai kuma yayi shuru yana kara nazarin Falon kamar me neman wani abu basu Damu ba Sanin Halinsa Sannan babu wani Shakuwa sosai a Tsakaninsu Tunda shi Babba ne sannan Lokacin da suka taso baya kasar yana Madina so zamansa Dasu bashi da yawa ammh duk da Haka yana da Kwarjini da baiwar da kowa ke girmamasa,ba Duka yake yi ba ba kuma Fada ba,Shi ina ma ya zauna ballatana yayi Hukuncin ..?in yazo kuma bai wani Dadewa yake komawa sai dai AllAh ya riga ya bashi wannan girman kuma ya Dauka kamar yadda In mallam yayi mgana bamai Musamai haka shima mgana Daya zai yi Cikin kwanciyar Hankali da Salama kowa zai shiga Taitayinsa bawai bashi da Sakewa bane, bai da yawan wasa da Dariya sannan bai da mgana ballatana Hayaniya yana da Matukar Sanyi Sosai a lamuransa.
Kamar ma ya manta daasu acikin Falon Saboda yadda yayi Shuru bai kara mgana ba sai chan ya kalli Aisha kafin yace"Ina bakuwar ku.?
Da Sauri tace"Na kaita Dakinmu na nuna mata Tiolet tana ciki na barta Tun dazu..!
Kai ya gyada kadan kafin yace"Ina Hajiya..?
Chapter 20 · 0% Book details