← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 95

Sashe 94

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

FU'AD dai babu yadda ya iya da jarabar sanaya gashi yanason cimma manufarshi Dan Kar yaki Bata hadinkai ta fahimci wani Abu Dole ya dinga biye Mata Yana Jan al'amarin burin shi kafin komai ya wakana bakin da dady ya turo su k'araso jami'an tsaro suyi ram dasu sai wasan ya Kare tsakanin shi da sanayan.
Sanaya ta Gama mutuwa Akan FU'AD yau ga FU'AD Tana saraffashi yadda takeso Dan Haka tafi kowa sa'a ayau yanata sakin jikin Dole da ita Ana cikin Haka yaji motsi a falo lokacin da sanaya take gab da cimma burinta akan FU'AD har sai d su kidnappers din suka shigo suka doshi d'akin shi Dan Haka aka Basu damar suyi Basu San ya canja wajen kwana ba ,duk shigowar su gidan a idon Jameel d sa'adiya ta window sa'adiya ta tsure Jameel ne ke kwantar mata da hankali da sauri sak'on karta kwana ta gauraye wayoyin su d jami'an tsaron da FU'AD din da kowama Wanda yasan da Abin Husna ma ta farka duk sai taji ta kasa bacci alamun wani Abu na Shirin faruwa.
Bayan kidnappers din sun shige d'akin FU'AD sukaga kud'i a zube a gadon suka fada Kai suna kwasa kafin su nemi Wanda sukazo domin shi dake mayunwatan kudinne d sauri jami'an tsaro suka shigo suka arresting din su Kowa Baki sake cike da mamaki aka Fara fito da kudaden dasuka jida aka kwace bindugogin su Ana cajesu anaka saka musu handcuff kowannen su aka fito dasu falo Jin Ana gunjin ihu da ban hakuri FU'AD ya kwaci kanshi da kyar daga wajen sanaya ya fito falo Yana hamdalar yasha a wajenta batare da burinta ya cika ba,itama bayanshi ta biyo Tana Mai magiya sai sukayi cirko_cirko suna mamakin yadda akayi hakan ta faru.
FU'AD tafi ya farayi Yana tafama jami'an tsaron Yana yabana aikin su ,Yaya Jameel ya Kira da sauri sai gashi harda aunty sa'adiya Bayan an Gama magana aka tasa keyar su a motar jami'an tsaron su 6 sukayi ofishin su dasu cikin Daren hajiya baba tajiyo alamun da matsala Amman ta window ta fahimci wani Abu kamar barayi aka Kama Jameel ta Kira a waya d sauri yazo y saneta Dan yaji alamun hankalinta y tashi ,Husna ma dama tun tashinta Bata koma ba Jin motsi a falo sai ta sakko duk taji Abin dake faruwa,suka dinga salati har su harri sai da suka fito suma.
Sanaya kuka taketayi Yaya Jameel sunata bayanin Wanda yasa Ayi hakan mamakine bayyane a fuskokin kowa na gidan sanaya tashi tayi d gudu ta koma sashinta jikin Daren ta kulle kanta a d'aki tanata kuka.
FU'AD ko d su Husna d su mumcy kusan anan falo suka karasa kwanan su Kowa ya kasa komawa anata tatauna yadda za'ayi d safe.

Da gari y waye sanaya ta Kira dady ta sanar Mai da komai hankalin Dadi y tashi y rude y dinga surfa Mata zagi da masifa Yana cewa ya yafeta Yana Gama waya da ita ya kashe wayoyin shi yasa Mami ma ta kashe nata jami'an tsaron nata neman numbers dinshi shiru dake kidnappers din sunci gabza da kansu suka fada suka bada number shi ganin ba'a sameshi ba aka karbi na Mami itama shiru Dan Haka suka San Akwai Shirin da aka kula Wanda suna zargin sanayace ta sanar musu Dan Haka FU'AD ya nemi Husna da tabashi number mufida k'anwar sanayan ta bashi aka Kira ta d'auka akace tasa a speaker yadda dady d Mami zasuji aka Mai razanarwa Mai tsauri Akan sanaya da karamin company shi dake 9ja suna hanun jami'an tsaro inya kawo kanshi a yau ya nemi sulhu inko be kawo ba ya tabbatar suna cikin garari wata uwar ashar dady ya sakarma mufida Akan tabar waya a kunne har ankirashi za'aci zarafin shi har da duk'a ya bita , jami'an tsaron sukace a rabu dashi ai sako ya Isa su bashi yau zuwa gobe.

Bayan su FU'AD sun koma gida ne suka mayarma d mumcy duk Abin d y faru tsakanin su day dady.

Dady kuwa tunda yaji asirin shi ya tonu ya Shiga garari d tashin hankali har mamy ,da kyar mamy t lalabashi Akan su taho 9ja akashe case din su taho d sanaya ,d masifa ya Shiga surfa Mata Yana cewa duk ita tabata Mai shiri Kuma ai ta sani shi kawai zejene saboda company shi ,mamy amincewa tayi tace suje din inde zeje.
Mufeeda ko cewa tayi bazata bisu ba Dan bazataga Abin kunyan d yayi ba Amman sai ta fake da katatun ta ita d kanin sanaya Dan shima y Gane gaskiya Dan Haka fumeeda ta koma gidan wani abokin dady su Kuma suka dunguma zuwa 9ja k'asar gado.

Da zuwansu a hotel suka sauka basufi awa 1 da sauka ba suka amsa gayyatar ofishin jami'an tsaro aka Kira su FU'AD da har hajiya babba ma sai da taje har sanaya da Ido ya raina fata taga samu taga Rashi na FU'AD.

Ganin abun na Shirin zama babban case sai mumcy tace abarsu suyi sulhu Amman komai arubuce ze kasance kowa ya yadda Amman abokin FU'AD jami'in tsaton da kyar ya amince Dan yace Abin ba na Wasa bane.
Dady ko sai hura hanci yake aka fito da kidnappers din aka musu tambayoyi duk babu Abin da suka karyata sai dady d ya musu taurin kai.
K'arshe dai aka kare da dady yasa hannu Akan duk Abin da ya sake faruwa da ahalin mumcy shine Kuma se ankamo shi a duk inda yake ,da kyar yace ya amince .
Aka tambayi su FU'AD sun yafe mishi asake shi? Dan mumcy ce to bada umarnin Haka FU'AD yace "eh sanan ya sawakema sanaya Auren shi dadyn ta ya tafi da Yar shi ta jari hujja da ya bashi aurenta"
Salati mamy tasa sai sanayan ma ta fad'a jikin mamyn ta shiko dady uwar harara kawai yake jifan FU'AD dashi k'arshe aka Gama komai a rubuce aka sallame su day niyar sanaya d jami'in tsaro zasuje ta kwado komai nata a gidan mumcy.
Mumcy ma taja iyalanta suka tafi kafin su tafi sai d mumcy ta zubarma da dady kalamai masu Sosa zuciya kamar ya kasheta Dan bakin ciki hotel suka wuce suna zaman jiran sanaya Dan yace gobe zasu koma Dan bayaso Yan uwansu na Nan Susan me ake ciki gwanda ya gudu kafin labari ya Isa garesu.

Sosai sanaya ta dinga kuka d zata bar gidan Tana ba FU'AD hak'uri d mumcy.
Mumcy dai tace ta yafe Mata FU'AD Kam cewa yayi ALLAH ya yatemu Baki daya na rabu da kidnappers.
Ranar gidan mumcy wuni akayi Ana murna da mamakin faruwar al'amarin ma gaba daya.

Bayan sati guda FU'AD yakai Husna gidan hajiyar mu Dan acan za'a daura Auren maman Husna da baba harda FU'AD d Yaya Jameel da B2k aka d'aura auren.
Baba kuwa bakin shi har kunne d abokanen shi wajen dai ya cika kamar manya akema Auren ba.
Itama maman Husna taji kwaliya anata tsokanan ta husna sai narkewa takeyi Tana musu shagwaba aunty huwaila nata lalab'ata hajiyar muma nata bata kulawa sun Gama fahimtar ciki ne da ita basa barinta tayi komai kuma duk Abin da takeso Bata sukeyi.
Sai d aka daura Auren su FU'AD sunci sun Sha sanan suka tafi gida d niyar sai dare zezo ya d'auki Husna, Yaya Jameel ne ya kawo su mumcy ,su hafeeza ma duk sunzo d mamanta d abokanan arziki har kawayen mumcy ma sunzo sosai bikin gyatumai yayi armashi har kowa ya washe ya koma gidan shi aka mayar da mumcy gida aunty sa'adiya kuwa Husna ta hanata tafiya wai su Bari akai Mata mamanta gidan babanta kafin sai sukoma Dole ta hak'ura.
Dare Bayan i'sha aka d'ebi motoci da Amarya d komai nata da hajiyar mu d taimakon FU'AD d aunty huwaila suka gyarama baba d maman Husna gidan su yayi kyau aka kaisu FU'AD ne yakai su Husna daga can yayi gida dasu baba ko takan mama habee bebi ba sai sauti yaba k'anwar ta me jinyar ta da zuwa yanzu ta Fara gajiya yace ze tafi gidan Amarya Dan matarshi amaryar shi ta dawo wacce sanadin dawowarta ne habee ta fad'a wanan Halin na k'aikayi koma Kan mashek'iya.
Kafin ya fice sai ga humaira afujajan Ido duk hawaye Tana Kuka ta shigo sai ko k'anwar mama habee ta Fara tambayar ta lafiya?
Baba da mamaki ya cikashi sai ji yayi tana cewa ,wai na dawo gida har sai ya nemeni wallahi bashi da mutunci Dan akuyane Ashe .......Bata k'arasa ba baba yace "ko Kuma kece Yar akuyar ba " da ganin Kira ai Daman zataci mutum.
Kanawar mama habee sai cream tayi ai tunda Auren rawa yake Zo ki kula d mamar ki Dan ko da take da lafiya ba dadinta mukaji ba tausayi da Imani yasa nake zaune a wajenta ,sai ko humaira tasa kuka ta kamata Tana Bata hak'uri Tana cewa"ta Mata Rai wallahi ta San komai ,baba ficewa yayi ya barsu a wajen Yana zumudin gidan amaryar shi sabuwa.

Bayan sati 4 humaira duk ta fita hayyacinta d jinya baba so 2 kawai yaje ya duba su shima kayan abinci yakai musu da zuwa d'aukan haidar Dan samamai makaranta Mai kyau ,haidar nata murna baba ya tafi dashi Dan yanzu tsarin kayan abinci yake bayarwa buhun hunna ya tashi daga awo duk wanan taimakon FU'AD ne Dan husnan ma Bata sani ba.

Husna tazama Yar dangi ji take tafi kowa Jin Dadi da farinciki ayanzu taje taga babanta da mamanta taje gidan kakaninta duk inda taso zuwa dai yin duniya zata ta dubo humaira d mama habee ,Amman FU'AD ya hanata Dole ta hak'ura.
Chapter 94 · 0% Book details