← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 95

Sashe 28

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

labarin fan dinta na social media. B2K sosai yake rarashin FU'AD da nunamai mahimmancin bin iyaye Yana bashi hak'uri ta tausan shi da rarashi ,da nuna Mai ya d'auki hakan matsayin k'addara Mai kyau sai ALLAH yaga niyar shi ya jefa Mai Albarka cikin Abin , sosai FU'AD ya fahimci abokin nashi ,Amman daurewa kawai yakeyi shi kad'a yasan ya yakeji Aran shi , B2k sai da ya shafe wasu awwanni tare da FU'AD seda yaga Yaya Jameel yazo sanan ya barshi ya tafi don Shirin angon cin abokin shi me Mata 2 lokaci 1 Dan FU'AD yace Babu Abin da zeyi Wanda ango yakeyi na farin ciki da auren da zeyi don Haka B2k ya d'auki nauyin yin wasu abubu bawai na bidi'a ba kawai irin Ayi party ko 1 ne sai kayan da zesa na angwancin da duk wasu abubuwan daze buk'aka tare da taimakon Yaya Jameel Dan sunyi magana kafin ya tafi . Gudun rigima Yaya jamee yace abar ma'un acan gidan aunty sa'adiya ,Amman mumcy tace dole ta dawo gidan su don bama mahaifinta hakkin shi na uba agareta Kar suyi Aiki da Kai Mana ,don Haka jibi su Ma'u da sa'adiya duk su taho in Kuma Kai zaka je ka taho dasu to ,kaga gatana ne d'aurin Auren in sun dawo washe gari za'a daura Auren ranar jama'a .. Sosai B2k da Yaya Jameel suke shiri sun shirya lefen amaren biyu duk da komai cikin gagawa akeyi ,komai iri daya ake sa musu sai banbancin kala in ansama wanna green sai asama wanan red Haka ake zuba musu uwar Kaya cikin setunan akwatunan nasu ,ita sanaya cikin gidan aka kawo nata akaba mamy ,itako ma'un mumcy ta Adana nata har sai baba yace akai in Ma'u ta iso garin . Ma'u ta Kira hafeeza ta sanar Mata d Auren d za'a Mata har take Mata jajen barinta gidan mumcy da Aiki sosai itama ma'un takejin abun Amman Babu yadda zatayi ,sosai hafeezar ta rarashi ma'un ita . Sanaya Ana nuna Mata lefenta da yaci uwar kud'i sai wani yatsuna takeyi Tana gwasale kayan wai ankarya darajarta ,kayan lefen ta had'in 9ja ba England ko Germany,ko India ba ko Yar Dubai d'inan da tazama Gama gari ita wlh ancuceta batason lefen aba almajirai masu buk'ata ,mamy da Taji haushi tace to ko amayar ma da uwar mijin naki? Da rashin kunya tace eh ace Mata nagirmi had'in 9ja wlh ,sai ko mufeeda tayi dariya ciki ciki tace ai aunty Sana d'auka zakiyi ki kaimusu abinsu ganinan biyo ki da wani Nima ,sai ko ta mik'e Tana turo Baki ta d'auki wani kit Tana Jan wani trolly wai zata mayar sai ko mamy tace ke Dan ubanki goyon gwauro ce ke? Baki da tunani Ashe kunya ta Miki k'aranci? K'anwar takice zatace kiyi Abu kiyi ? Sai ko mufeeda Tace mamy ki barta tunda batasan gatse ba,da gudu ta biyo mufeeda Tana setaci ubanta ita zatama gatse ? Mufeeda ta sunale ta Bayan mamy ta gudu ta bar musu d'akin a 360 ,sanaya kamar ta mutu don bak'in ciki ,kifewa tayi Kan gado Tana kukan shagawaba Tana cewa wlh in kuka auramin shi kun siyamai wahala don banayin shi wlh ...mamy tace Aiko saidai kiyi Kuma bakin alk'alami ya bushe ,sanaya cikin kukan tace to wlh ku tanaji kotun yin shara'a Mai suna *day to day court* tare da manyan alk'alai .......mamy tace wanan Kuma mun Jima da tanadar su yarinya ta fice ta barmata d'akin ta tafi wajen dady . Ta same shi Yana son fita Yana tsoron Rana wai bayason Rana ta tab'a shi Kuma wajen abokin shi zeje suyi maga Kan bikin Dan shine waliyin sanaya gwanda ya bashi girma yaje kafa da kafa don ya sanar mishi ga Rana na Shirin Mai cikas ,haushi da takaici ya kama mamy tace Ni bansan ranar da zaka canza ba Akan sababen akidan Nan naka kamar ba cikin ranar ka taso ba ka girma inda Tana kisa ma da bamu had'u ba ,sai kuyita wasan b'uya Kai da ranar .......da fad'a ya dakatar da ita nace ki dinga sanin lafazin da Zaki gayamin ko kin San banason Ana dawo min da Abin da ya gabata ko? Har zakice cikin ta na taso Amman ba tare aka haife mu ba ,kice ki tambayi masu ilimi akanta kisan irin illar da take Mana a jikin mu da fatocin mu kafin ki Shiga Abin da Babu ruwanki ,Tace bansan ilolin ta ba nadai fi sanin amfanin ta musamman irin na hantsi da kariyar da take bama jikin d'an Adam ,Bata k'arasa ba yace wanan Kika sani? Je kiyi k'ok'arin sanin ilolin sai Kika wanne yafi rinjaya ,kawai malama Zaki b'ata min Rai inaji da son fita Rana tak'i rusunawa Dan wanan ranar ko easy na kunna sai ta shinshinani ko Babu yawa wlh sai ta buys Zan fita duk nacin ki tuna ba aikena kikayi ba Kuma ba d'andako ko Mai wulbaro nake ba ,in abun buk'ata ne kinsan na Tara bani da matsalan komai ko Egypt Kuma kinsan da ba 9ja bane ko can innaga ta kaleni kinsan buya nakeyi bare 9ja da da kamar tasu ta daban ce ,mamy tace karde ashiga hurumin Mai komai dai wato ALLAH shi yayita dai asan matsaya Kar harshe yayi subul da baka baruwan wani da ALLAH bame Shiga tsakani ,sai ko ya Fara jaraba wai wa'azi zata Mai ? Ganin ya hassala sosai ta sulale ko Abin da zata fad'amai Bata fad'a ba ta barmai d'akin . Washe gari Yaya Jameel yaje ya kwana a Abuja don taho da su sa'adiya . Abu ya kusa saura kwana 2 d'aurin Aure ........
Chapter 28 · 0% Book details