← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 95

Sashe 37

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da safe da suka had'u da sanaya shi yace Mata kin kwana lpy ? Dan yasan ba gaishe shin zatayi ba sab'anin kwanan da yayi a wajen Husna be tab'a rigata gaishe shi ba ,cikin Isa da mulki tace kalau na tashi ,Kai fa? Yayi murmushi yaji sabon salon gaisuwa" shi ma yace yadda Kika ganni ,atunanin ta ko zata gyara sai kawai yaga ko ajikin ta ,yace ALLAH Mai mutane ya wuce dining don breakfast sai da yayi Kat sanan yace "ita taci ne? "Tace lokacin karyawan ta da sauran awa 2 don Haka Kar ya damu da ita " yace shi kenan ai ba feeding d'in ki za'ayi ba " ta Harare shi tace ko za'ayi ma ai ba kowane ke iyawa Dani ba sai Wanda yakai " ko kallon ta beyi ba ya koma d'akin shi be nuna mata beji dad'in maganar ba ma ,yayi wanka ya shirya ya ce tazo suje su gaishe da su mumcy . Uwar taurin Kai tace yaje zata Zo ya tafi ya barta yaso tursasata sai ya fasa gudun Kar tun yanzu ace ya Fara takura Mata ,Amman tabas Halin sanaya Akwai gyara akansu . Bayan ya Isa ya gaishe da mumcy sun zauna suna Hira , mumcy tace yaje yaga lafiyar Asma'u sai ya sakko ya cigaba da hirar ,zece wani Abu yaga mumcy Tasha mur ko damar k'orafi be samu ba Dole ya Gama nok'e nok'en shi ya tashi ya haura sallama yayi batare da ya jira an amsa ba yasa Kai Abin shi ,Yana Shiga Husna ta tashi da sauri alamun zata gudu saboda Babu gyale ko hijab a jikin ta har tayi hanyar Shiga d'aki ya dawo da ita da cewa "Ina Zaki Kuma ba kwana nazo yi ba yanzu Zan koma nazo ganin lafiyar kine kamar yadda aka umarce Ni . Sai ko ta dawo ,tazo ta d'an rusuna tace "Ina kwana? Yayi murmushi Yana sake bambance Hali irin na Asma'u da na sanaya ,yace Lafiya ,kin tashi lafiya? "Tace lafiya Lau ya matarka? Wani murmushin ya k'ara sakewa yace Lafiya Yana sake tunanin Akan Abin da sanayan Bata tab'a yi ba kenan ,sai yaji kamar ya zauna su d'anyi Hira Yana son fahimtar yarinyar da dalilan da yasa mumcy ta aura Mai ita matsayin aure share hawaye ,sanan yanada tarin tambayoyi Kan yarinyar Wanda masu amsawar ma sun kasu Kashi Kashi ,Yana nazartan halayen ta sosai ,ganin kamar ta takura tak'i sakin jiki ta sunkuyar da Kai sai yayi tunanin Bari ya tafi ya barta ko ta Sami nutsuwa da sakewa ya Mata sai anjima har Yana tambayar ta ko Akwai wani Abu? "Tace Babu yace to sai anjima in ya lek'o "tace ALLAH ya kaimu agaishe da ita" ya juyo yace wafa? "Husna tace matar ka ta shige d'aki abinta " Murmushi yayi yace Zan sanar Mata d sak'on ki in ta karb'a to ,ya sauka wajen mumcy . Bayan ya dawo sosai mumcy ta sake Mai fuska sukayi Hira har aunty sa'adiya da Yaya jameel sukazo gaishe da mumcy ,Aisha nata tambayan Husna ,Jin tambayan yayi yawa FU'AD yace wait Ina kikasan Husna Haka ne keda ba Yar k'asar Nan ba? Sai ko Aisha da aunty sa'adiya suka kalli juna ,sai Aisha ta Fara inda inda Tana cewa a Nan gidan Mana ,sai aunty sa'adiya tayi murmushi irin ALLAH ya taimake ta d'inan ,duk FU'AD na lura da su ,yayi murmushi yace hmmmm Akwai ayar tambaya aunty na . Kafin mumcy tace wani Abu sai Jameel yace kasan fa Mata basu da wiyan sabo a mota ma suka had'u sai kaga kamar tare aka haife su . FU'AD yace da wanan Dan wanan Amman badan ya yadda ba . Ita dai Aisha cewa tayi Bari naje muyi Hira da husna ko na sakko da ita ,ta haura saman aunty sa'adiya na Mata dariya . Sosai Aisha da Husna akasha Hira har taba Bata labarin yadda sukayi da FU'AD d'azu ,Husna ta dinga dariya Tana cewa itama fa Tana so tasan danme za'a b'oye Mai Dan bazata d'auki wulak'ancin da ya Mata ba a baya , Aisha dai tace kedai kibi komai sannu a hankali Dole ma ai ze sani komai zai dedeta ,Amman fa kinyi sa'a miji k'awata wlh FU'AD na daban ne kin Gama d'auke jarumin jarumai a cikin 9ja ,Husna dai keb'e Baki Tana cewa hmmmm wai sa'a Auren da Babu shawara ko tambaya kawai had'amu akayi gaba d'ayan mu Babu so balle k'auna ? Duk Ni aka ma son Rai ma Dan ansan baze Soni ba kuma bamu da komai wlh da annemi shawarata da nace Kar....... Da sauri Aisha ta toshe Mata Baki tace "karki k'ara furta irin wanan kalaman kina nufin godiyar da zakima mumcy kenan da wanan kalaman Zaki saka Mata? "Husna ta girgiza Kai " Aisha tace takayar da Zaki Mata kenan ? Don ita ta had'a Auren ki da d'anta Abin soyuwa agareta baran Tana k'in ki ba Kuma Tana so ku had'a jini da zuriyar su Bata Miki daidai ba da ta zab'o ki cikin Mata dibu? "Husna tace aa ba Haka nake nufi ba ,Baki fahimce Ni ba Aisha " "Aisha tace bazan fahimta ba kuwa indai Akan hakane ,ashawarce karki Kuma ko kusa ko Alamar sake furta Haka akan Auren Nan ki kasance Mai fad'an Alkhairi ko kiyi shiru zakiga Abin mamaki cikin aurenki da FU'AD insha ALLAH ,wace zata zamu kamar FU'AD tafara k'orafi ko Auren Dole aka Mata dashi ? Tab jarumin jarumai ne fa? "Husna hmmmm kema dai ALLAH ya Baki jarumin jaruman Nan " da sauri Aisha tace na Ghana ba" suka sa dariya "Husna tace itama matar tashi ai ko damuwa dashi batayi ba kamar yadda be damu Dani da itan bama kina hango Mana zama na soyayya ko na k'aunar juna ko Nan gaba ahakan? Aisha tace Kwarai ma kuwa da yadda ALLAH ki rubuta ki ajiye mahak'urci mawadaci ,maganar matar shi Kuma ki ajiyeta gefe iya Ruwa fidda Kai ,nifa banason firta maki wasu abubuwane Dan Ni fa Akan kishi ko kishiya inada k'azamin kishi har Addu'a nake ALLAH ya yaye min ,keko Naga Abin naki da sauki ,kuma hakan nada kyau Dan mazan yanzu sai dai abarsu wlh ,Amman nidai nafiso ki nemi soyayyar mijin ki da k'arfin ki da 'yancin ki da kanki basai wata uwar miji ko wani yazo ya karb'an Miki ba ,wallahi ki tashi tsaye zakice na Gaya Miki , ALLAH ya kashe ya Baki ba kud'in da yake dashi bane Abin dubawa ko so ba dukiya daban so da k'auna daban in takai ce Miki ma Babu Abin da yafi kulawa da zaman lafiya dad'i acikin sha'anin Aure ba duk da banyi ba Ina tare da wad'anda sukayi Kuma suke Jin dad'in hakan ,Dan Haka hajiya ta ki dage ki karb'i soyayyar ki kawai ,husna dai dariya tasa Tana cewa ALLAH yasa mu Dace to" Aisha tace Amin . Bayan sun Gama Hira suka sauka k'asa suka samu sai mumy da Yaya Jameel da FU'AD ,aunty sa'adiya ta koma sashin sanaya wai zata tayata Hira Kar ace basa kula da amanar da aka barmusu , mumcy dai murmushi tayi tace hakan nada kyau ,su Aisha na Jin Aunty sa'adiya na wajen sanaya Suma suka tafi , mumcy tayi murmushi tace ALLAH ya tabbatar min da dawamamen zaman lafiya cikin ahalina Wanda ze zamar min matsana ALLAH ya nisan tamu dashi " su FU'AD suka amsa da Amin. Husna , Aisha da sallama suka Shiga part d'in sanaya anuty sa'adiya na zaune Tana Taya sanaya Hira Tana amsawa kamar Dole tanayi tana danna wayar ta Alamar charting takeyi . Tun da ta d'ago suka gaisa da su Husna Bata k'ara kallon su ba ,sai da Aisha ta gaji da zaman shirun sanaya ta barsu yasu yasu suna hirar su sai tace "aunty Sana ke mukazo tayawa Hira fa Amman kin barmu munatayi mu k'adai ? Sai sanaya tace " ayya sorry wallah mutanen Nan ne suke d'auke min hankali sorry Ina zuwa ,ganin Abin bana k'are bane sai Aisha ta tashi ta k'arbi wayar sanayan Tana cewa mugansu suwaye ne suka Hana 'yan uwa hirar zumunci bakije wajen mumcy anyi dake ba mun biyo ki nanma kin barmu munatayi mu kad'ai ,suna cikin haka sai ga FU'AD ya shigo bak'in shi d'auke da sallama da sakin fuska yasan su aunty sa'adiya na d'akin ,Yana shigowa Husna tace Aisha muje ko ? Sai ko FU'AD yayi Mata wani irin kallo Mai sigar rarashi Dan yaga su aunty sa'adiya "yace Ina zaku ? Tayi shiru ta sunkuyar da Kai " sai yace kuyi zaman ku Nima Ayi hirar Dani ya nemi waje can gefe shi kad'ai ya zauna Yana kallon makeken TV dake manne a falon Aisha rik'e da wayar sanaya sai cewa tayi laaa ,aunty ai Baki da enough charge ma? 43% fa? Barin sa miki ,ko amsa Bata tsaya jira ba ta tafi ta saka Mata wayar a caji ta dawo ta Fara janta da Hira sunayi suna kalon TV ,sanaya a Dole ta Fara amsawa Aisha hirar duk ta Haka tanayi tana Shan qamshi . Shi ko FU'AD sai Satan kalon Husna da sanaya yake , Aisha na kalon shi ,suko Basu San ma yanayi ba ,ita dai Aisha ta Rasa me yakeson hangowa atare dasu tanata kalon shi ,shima besan Tana lura dashi ba . Sanaya adole take hirar har aunty sa'adiya take cema sanaya Bata Jin wani iri da zaman kad'aicin da take? "Sai sanaya tace aa ai ta Saba indai itace Bata son damuwa wani lokacin ,suko mutane indai zaka zauna acikin su wani lokacin Akwai damuwa a tare dasu " sai ko maganar ta tsayama Husna a Rai tace au yanzu mu damuwa ne kenan da mukazo tayaki Hira? Ita kanta Husna batasan ta furta hakan ba . Tambayar Tama kowa daidai har FU'AD yace yauwa Ashe kinada zurfin tunani karamar cikin su ,sai ko sanaya ta dafa kafad'un Husna tace "ayya sorry ba nufi na kenan ba ,banyi Dan ku ba ,bakiji ba nace wasu kema kinsan Akwai irin wad'anan mutanen ai kiyi tunani Akan magana ta ,sai ko Aisha tace hakane ,Amman Nima nayi tunanin ko mune damuwar ,Yaya Jameel ne ya musu
Chapter 37 · 0% Book details