← Book details Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 95

Sashe 32

Rikon Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan wasu lokuta sai ga aunty sa'adiya da rakiyar Mai Aiki da kayan abinci na su ma'un ,Bayan sunci sun k'oshi Ma'u ta Fara watso ma aunty sa'adiya tarin tambayoyi ta hanata amsa ko 1 sakamakon jero su da takeyi kamar alokaci 1 takeson a amsa Mata , Aunty sa'adiya murmushi tayi tace "to wanne kikafi so na amsa acikin su? "Ma'u tace waye mijin da akace an auramai Ni? Me gadin gidan Nan ko direba? Ko iro Mai wanki? Idon ta cikin na aunty sa'adiya tanason sanin waye acikin su?
Sai sa'adiya tace "Husna duk ki wuce tunanin su da sanin su ke ai matar manya ce ,da namiji Mai 'yanci da kima Kika Dace ,Suma bawai Dan ba mutane bane aa ko 1 kowa dai da abokin Rayuwar shi Suma zasu iya Auren macce Mai daraja Kuma a zauna lpy babu yadda ALLAH baya yi,Ma'u dai saurare take taji amsoshin tambayoyinta can ,sai sa'adiya tace "nasan kinfi zak'uwa da son sani waye aka Baki matsayin mijin ki ? "Da sauri Ma'u ta gyad'a Kai alamun eh bakin ma be samun damar bud'uwa ba ,sai ko sa'adiya tace "Ma'u ki yi Amfani da damar da ALLAH ya Baki wajen d'orewar farin ciki da kwanciyar hankalin ki Dana duk wani masoyinki ko Mai tausaya Miki musamman baba , FU'AD shi ALLAH ya zab'a Miki matsayin miji Haka shima ya tab'a mafarki be tab'a ba ? Kece amatsayin matar shi matsayin uwar gidan shi Kuma Dan Auren ki aka Fara d'aurawa , nasan zakiji maganganu na kamar Ina watsa Miki ruwan batir ,ki bani nutsuwar ki kifahinci manufar mu Akan wanan had'in ,wacce ta asasa had'in Nan itace mumcy ,in tambayeki Zaki iya sadaukarwa ga mumcy kuwa Akan komai? Jiki Babu kwari Ma'u ta sake gyad'a Kai ,Bayan mamaki ,tsoro ,tashin hankali ,fargaba da duk suka dirar Mata tunda akace FU'AD ne mijin ta ,Tama Rasa Abin yi ko fad'a , sa'adiya taci gaba da cewa toh ashawarce Babu wani abun sadaukarwa ko sakaya ko farantawa da zakima mumcy da ya wuce karb'an kyautar da ta zab'o ki ta Miki ,Dan zab'o ki tayi ta had'aki da gudan jinin ta da take so ,kin taba tunanin Zaki auri FU'AD ? Da sauri Ma'u tace aa wlh ko amafarki yanzun ma ban Gama tabbatar wa ba wlh Tana Shirin yin kuka ....
Sa'adiya ce ta share Mata hawaye tace to Zaki tabbatar ranar da Kika ganshi agaban ki ,afirkice k'irjin ta ya bada daram tasa hannu ta rufe fuskar ta kamar Yana gabanta ,Tana ayyana irin tozarcin da ze Mata ,sai jin muryar sa'adiya tayi Tana cewa ,wani da Zai sa ki k'ara dagewa wajen faranta ran mumcy shine juriya da duk wani Abu da zai dinga bijiriwa daga FU'AD zuwa gareki na ,ki daure ki share matuk'ar babu cutuwa ko tozarci ,Dan shima irin biyayar d kikayi ita yayi aka had'a Auren ku,Kinga ko shi namiji ya hak'ura ma balle ke mace? Sai ko Ma'u tace au dama Auren Dole aka Mana gaba d'ayan mu ? Sai Jin muryar sa'adiya tayi ,nasan Zaki ce Auren Dole aka muku kenan? Sai ko Ma'u tace shikenan Abin da nakeson sani har ta hango kodai aunty mayyace? Sai sa'adiya taci gaba da cewa ,duk gaba d'ayan ku da FU'AD d'in da sanayan da ke duk umarni kuka bi kuka bi zab'in da iyayen ku suka muku ,Nan taba Ma'u labarin da Bata sani ba Kan Auren sanaya duk da tasan wani wani Kuma Bata sani ba sai taji tausayin kansu duk su 3 ya Kama su....
Sa'adiya taci gaba da d'ora Ma'u ahanya Tana nuna Mata sai tayi juriya da hak'uri insha ALLAH zataga ribar Auren ,Kuma Bata da matsala tunda har mumcy ce ta zab'e ta matsayin surikar ta ,Bayan ta gama Mata hud'ubar Aure da rayuwa ta koma wajen mumcy .
Aisha ta d'orama Ma'u da nata hud'ubar da hafeeza suka dinga sata ahanya Mai b'illewa ,sosai Ma'u take fahimta sai tsoro da shakkar aikatawa da takeyi ,zuciyar ta fal da mamaki da tunanin ya zasu zauna matsayin ma'aurata da FU'AD?

Sanaya ma tsirarun dangin dady sun tasa ta gaba sunata Mata tasu hud'ubar ,Yana Shiga Yana fita ,sosai akayi Mata iya nasihar da zasu iya da ban Baki ,mamy duk Tana Jin su .
Mufeeda tun da ta gano Ma'u kishiyar aunty sanah sosai taji dad'i ,Amman ita sanayan Bata sani ba ,Dan har ziyara ta Kai Mata suka had'u da Aisha ,sunata hira Abin su.
Itako sanaya Banda takaici Babu Abin da takeji gashi samarinta na Egypt sai Kiran ta suke wai ya zata musu Haka sunga k'awarta summy tasa a statun wai Ashe rabon aure ne yakai sanah 9ja .
Tun Sana na k'aryatawa Tana Basu amsa har abun ya Fara kular da ita Dan Haka ma ta kashe wayan ta ta jefa jaka kawai taji da zafi 1 .....
Mamy dai lalab'ata takeyi Tana tambayan ta abubuwan da take buk'ata amata ko ta hak'ura tayi zaman Auren da kyau duk da mamyn ma k'arfin ta dady yafi ta hak'ura da auren ,duk irin lalamin ma mamy ta Mata tak'i fad'an son ranta sai kalamai masu kaushi da take fesarwa ga mamy da dadyn nata Akan Auren ,sai dabara ne ya fad'o ma mamy tace "yauwa baby wane mota kwanaki kikace dadyn ki ya canza miji ma fad'amin model d'inta insa asai Miki ,sai ko sanah ta juyo ayatsune tace hmmmm a 9jan za'a zamu motan mamy ,Tana Mata kallon tuhuma da rashin kunya , "sai mamy ta Mata dakuwa tace "Dan uwaki dan ubanki me Kika d'auki tushen iyayen naki ko kin manta ne na tuna Miki? Sai ko sanaya ta yarfar da hannu take aa mamy ban nema ba ,ban nemi sani ko ji ba Wanda na sani abayama is ok ,nidai ba 'yar 9ja bace jibiyana na foreign country ,Kinga tushen mu daku da banbanci ,sai ko mamy tace Dan ubaki aidai Wanda suka haife ki kike fad'ama Haka wawiyan yarinya kawai duk motan da kikeso Akwai anan bana son karya mutunci k'asa ,ki fad'amin sunan ta Nasa dadyn ku ya siya Miki sanan in kina da ra'ayin fita Aiki sai kiyi magana anema Miki Mai kyau Wanda Rana beze dinga dukanki ba Inji dadyn ki ba injini ba ,muna sauraren ki ,mamy ta tashi ta fice Bata jira amsar sanayan ba .
Sanaya tunani ta Shiga yi Akan siyan motan da yin aikin ko barin shi ,daga baya tayi tunanin bazata Sha wuyan banza ba Akan wasu 'yan kud'ad'en da befi Tasha Mai amotan ta ba a wata amatsayin Albashin ta ba ,Dan Haka babu aikin da zatayi kawai asai Mata motan ko Shan iskan ta dinga fita da motan da su zuwa saloon ....

FU'AD sunata magana da B2k Akan ya zeyi da Mata biyu yanzu gashi kowa ta d'auki part d'inta sai ya raba musu kwana ,sai ko FU'AD ya Galla Mai harara yace ,Kaine kwanan ai me zanyi da kwanan balle na raba shi ? Abarshi a had'e Mana shi kwanan Yana Jan wani gajeren tsaki ,sai ko su B2k suka bushe da dariya ,sukace wlh Dan air ne Kai abokin mu ,Dole fa kaba dakai bori ya hau ahaka zaka samo Mana jikokin Wanda mumcy zata kalla taji dad'i? Sai ko ya kale su yace "Aiko bazata zamu ba Dan bani nace su jona min kowa ba acikin su ,ko suba kansu babin har Mata 2 sai kace noma zasu min .
Sai ko Ahmada abokin shi yacce eh Mana noma zasuma da taimakon ka ....be karasa ba FU'AD ya dakatar dashi yace d'an air Banda time d'in batawa Akan wanan Auren ki rabu Dani ,badon sun so ba sai Dan ganin FU'AD ya fututuke ,suka canja Hira .
Yamma tayi gari ya Fara duhu Babu FU'AD Babu labarin shi sai Yaya Jameel ya Kira shi a waya da kamar baze d'auka ba sai dai ya d'auka ,Dan bayason Ayi Mai magana Akan matan da aka aura Mai ,sai ko Jameel yace Yana son ganin shi da gagawa a gida Dan yaga alama kunya yakeson Basu , FU'AD tunda yace Yana zuwa be k'ara cewa komai ba ,sai da ya k'ara awa 1 da rabi shima sai da yaga Kiran mumcy sanan ya ,daga be Bari tace komai ba yayi saurin cewa gab yake da shigowa gidan ya kashe wayar Yana mita Akan Auren.
Su B2k nata bashi shawara da hak'uri da karb'an Auren da hannun Alkhairi .
Chapter 32 · 0% Book details